💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 30.
*Taqabbal minna wa min kum*
"A'uzubillahi" shine kalmar da maimunatu ta furta cike da tsoro ta kalli kofa sannan ta fara kiciniyar mikewa amma tam ya matseta a jikinsa har tana jiyo saukan numfashimsa a wuyanta nan da nan jikinta ya fara b'ari sai kokari take ta kwace jikinta.
Cikin rawar murya tace "yallabai dan Allah ka sakeni ni ba yar iska bace." Cusa hancinsa yayi tsakankanin wuyanta tare da furta "how i missed this." A can kasan makoshinta duk da gyalen da yayi musu katanga bai hanata jin wani familliar feelings na taso mata kara yunkurin tashi tayi taji ya kara matseta zuwa lokacin ranta ya kai kololuwa wajen baci adduanta daya kar wani ya shigo ya samesu a haka.
Cikin tsawa tace "dallah malam na gaya maka ni ba yar iska bane ka rabu dani ko,in ka saba iskancinka toh ni ba sababbiya bane ka sakeni tun kafin in tara maka jama'a."
Cak ya tsaya da abinda yake yi ya sassauta rikon da yayi mata ba shiri ta mike tana gyara kayanta a hankali yace "miemie ni kike d'agawa murya haka?" Wata uwar harara ta banka mishi tana kara gyara rolling din gyalenta dan kar ta fita a zargesu shi kam sai kallonta yake yi.
Tana gamawa ba tare da ta ce mishi komi ba ta fara tattara yan komatsanta zata fito ya riko dantsanta cike da mamaki cikin fusata yace "miemie wai ba dake nakw magana bane kin mayar dani dan iska?" Kwace jikinta tace "da kai me ye ba dan iskan bane? Kuma bari kaji ni ba sunana miemie ba da ubana ya rada min suna ba miemie yace sunana ba sunana maimuna in zaka iya kira fine in baka iyawa tafi nono fari,on a second thought ban ma son kara jin sunana a bakinka dan ban sanka ba kuma bani buqatan sanin dan iska irin wanda da ganin mutum zai cakume sannan kuma murya kuma da na daga maka kai ka siya tunda ka tabani ba da izinina ba in kai baka girmama mahallicinmu kan abinda ya haramta ba banga abinda zai sani in girmamaka a matsayin uban gidana ba mtsseww." Ta sa kai ta fita kar ku so kuga yanda zuciyanta ke rawa zuciyanta cike yake da tsoro dan tafi kowa sanin munin fushin marwan wallahi yana iya tara mata jama'a yanzun nan da hargaginsa na banza.
Tana fita taci karo da Tahir yana pacing kofar dakin taron tana fitowa ya taho inda take da hanzari har zai riko hannunta ya fasa fuskarsa dauke da murmushi yace "hope all is well?" Da mamaki ta kalleshi sannan ta kalli dakin taron ajiyar zuciya ta sauke sanin da tayi dakin sound proof ne na waje ba zai ji na ciki ba murmushi ta dan saki na yake tace "yeah am good,me ka gani?"
Marwan kasa kwakwaran motsi yayi dan ya cika da mamaki ko dai da gaske wannan ba maimunatunsa ba ce? Maimunatu da ya sani bata da hayaniya she is as frigile as a morning flower amma yau she stood up to him ya san ko zata yi wa kowa tijara but not him toh me ya faru me ya canza maimunatunsa yayi zaton tana ganinshi she will rush to him in tears tana tambayan inda ya shiga me ya faru basu kara jin duriyar juna ba amma me sai ya ga sabanin haka.
Dan murmushi yayi ya sani fushi take da shi,fushi take bata kara jin labarinsa ba shima ai yana fushi amma zai ajiye fushinsa ya lalasota ya shawo kanta ya san ya zai yi.
Da wannan tunanin ya mike dan ya fita yana fita idanunsa ya masa mugun gani.
"Ba komi! Tahir yace tare da cusa hannunsa cikin wandon suits dinsa dan karkata kai tayi tana kallonsa yayi kyau abinshi shima cikin suits she wonder me yasa suits ke yiwa dogayen maza kyau,marwan ya san wannan kallon ya san tana appreciating Tahir ne nan da nan ranshi ya b'aci sai hadiyen yawu yake.
A tare suka yi magana ita da tahir
"Kin ci abinci?"
"Kayi sallah ma kuwa?"
Dariya suka saki a tare maimunatu na dafe bakinta tare da saukw kanta.
Gyaran muryan marwan shi ya dauke dariyar maimunatu d'ip."Taheer me kuke yi a nan har yanzu?" Cikin murmushi yana kallon maimunatu yace "zamu je cin abinci ne da miss maimoon." Dan tabe baki marwan yayi ya ciro hannunsa daya cikin aljuhu yana duba time a jikin rolex wrist watch d'insa yace "wuce muje muyi sallah first." Dan shagwabe fuska tahir yayi yace "yah marwan ci na gaba da sallah fa."
Marwan bai kalleshi ba yace "miemie wuce ki cewa mubeena ina son minutes din meeting din nan a email dina in an hour."
A kufale tace "maimunatu sir. " daga kafadu yayi yace "whatever" tabe baki tayi kaman tayi tsaki sai taga rashin dacewar hakan tunda ga taheer a wajen zai mata kallon rashin da'a har ta shiga elevator dan ta tura mishi haushi tace "T sai naji kiranka." Kafin Tahir ya bata ansa kofar ya rufe sunkuyar da kai marwan yayi yana kallon takalminsa dagowan da zai yi sai da Taheer ya tsorata saboda yanda lokaci daya farin ya koma ja kowa ya san irin temper din marwan shi yasa kowa ke kiyaye masa yana da saukin sha'ani amma fushinsa ba kyau."Yah Marwan muje sallahn ko?" Ya fada dan yana tunanin sabosa yayi masa musu a gaban employee din shi ne dan girgiza kai yayi yace "jeka kawai,ya juya ya nufi private elevator dinshi har ya kai ya juyo yace wa Tahir "bana son shashanci in zaka wooing mace not in my building." Gyada kai Tahir yayi sannan ya juya ya bar taheer a tsaye, shi ba wawa bane marwan is indirectly telling him kar ya bi bayan maimunatu sai in sun bar cikin company dinshi.
Dan daga kafada yayi ya nufi elevator.Maimunatu na shiga office dinta kiran Khalid na shigowa dan tsaki ta ja tare da fad'in "not again." A nutse ta dauka tare da sallama cikin taushin murya yace "munah are you ignoring my calls again?" Jikinta ne yayi sanyi tace "khalid ba haka bane na riga na gaya maka in har kaje ka aiwatar da abinda nace maka wallahi zan aureka." Numfashi ya sauke yace "zan shigo in mayar da ke gida in an tashi aiki." Lumshe idanu tayi tace "da mota na zo."
Bai ji dadi ba sam amma sai yace "toh in sameki a office ko gida dan ina so muyi magana." Daga kafada tayi tace "duk wanda yayi maka."
"Alright zan kiraki,ki kulan min da kanki. " tana ji ya blowing mata kiss shiru tayi ba tace komi ba ta limshe idanu tana jin sound din kiss din har tsakan kanta.
"Me kike nufi DA zaki aure shi in ya aiwatar da abinda kika ce........?"