page 42

2.1K 229 59
                                    

💖KINA RAINA💖










By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14








Page 42.








Waro idonu tayi ta saki baki tana kallonshi na sure ko ta ji abinda ya fad'a gyada kai yayi yana murmushi ya saka dan yatsansa a kasan habanta tare da rufe mata baki da kyar ta tattaro tunaninta tace"yayana ban fahimceka ba,ban fahimci ta inda maimunatu ta zama miemie dinka maimunatu ta zo moh enterprises just 8 to 9 months ago kai kam ma gaba daya da dawowanka bai kai 2 months to how?,when duk hakan ya faru? Right now i am really confuse ."

Murmushi yayi tare da gyara zamansa yana fuskantarta ya riko hannunta kafin yace "ni ban san maimunatu a moh enterprises ba na santa shekaru kusan shida zuwa bakwai da suka wuce rabona da in ganta kuma ya kusan shekara biyar." Ai kam zuwa lokacin da idanu na barin socket dinau saboda gwaluwa da na mubeena ya bar nata cikin inda inda tace "yayana how?... I mean when.... Ya salam" ta dafe kanta dariya yayi yace "calm down zaki ji yanda muka hadu a cyprus ne time din da naje phd dina........" Nan dai marwan ya kwashe haduwarsu da miemie da soyayyarsu da shakuwarsu ya gayawa mubeena har da zuwa rabuwansu.

Cikin tsananin farin ciki mubeena take kallonsa ta wani gefen kuma tausayinsu taji sun rabu Allah ya kara hadasu bayan shekaru biyar shi yasa maimunatu take wasu abubuwa in ta ganshi amma kuma? Cikin confusion tace "toh yayana me yasa kuke nunawa kaman baku san juna ba?" Fuskarsa cike da damuwa yace "in ta nine i will show the world my woman amma hakan zai yuwu ne in tana sona ko tana son a san ita din tawa ce,miemie ita ta fara nunawa bata sanni ba da na confronting dinta sai ta nuna she dont want anything to do with me? Abu daya na sani tana tsananin fushi dani fushin da na kasa gane mafarinsa she thinks i wanted to take advantage of her which i never did,yes we did some stuffs but i never sleot with her." Ya fada yana lowering kwayan idonsa

Mubeena tace "tana tunanin kayi amfani da soyayyarta da yarintarta ne kuka yi wasu abubuwan saboda ta gane kayi haka da wasu kafin ita?" Ya gyada mata kai a hankali tace "i am sorry yayana i think i contributed wajen bataka a wajen munah amma banyi hakan da wani manufa i told her da kai din player ne amma yanzu son mace daya ya canza ka wanda yanzu na gane ita din ce macen da nake magana." Murza hannunsa tayi tace "wallahi yayana maimunatu na sonka kar ka karaya har yau banga namijin da yau ta nuna mishi soyayya mutum daya shine mai daraja da na sani a wajenta dict danfulani shima ta tabbatar min babu soyayyarsa a tare da ita soyayyanta na ga wani ammma bata gaya min waye ba yau dai ina ganin na samu amsata." Murmushi yayi mata yace "i hope so domin miemie itace farin cikina." 

Kame baki mubeena tayi tare da fadin"wow! Ga yayana in love." Zungure mata kai yayi yace "na fara wasa dake ai, yanzu kin san matsayin mimi sai ki tayani yakin samunta already daddy ya nema min izini a gidansu and mahaifinta yace in nemi miemie kuma sam taki saurarata."

Cikin tausayawa tace"yaya are you sure iyakacin laifinka kenan? Me ma ya raba ku and why didnt u guys get in touch?"
A hankali ya warware mata komi kuma ta fahimta tace "toh ga laifinka na farko dole sai ka warware wannan laifin sannan komi ya zo maka da sauki yanzu kallon mayaudari kawai take maka gani take dan kawai Allah ya kawota gareka ne amma baka yi yunkurin nemanta ba."

Shiru yayi yana tunanin tabbas mubeena tayi gaskiya me yasa bai taba kawo wannan a matsayin matsalarsu ta farko ba? Tsam ya mike yace "thanks auta,kiyi bacci me dadi." Dariya tayi tace "Allah ya tashe mu." Yana amsa mata ya sai kai ya fice.

Wani irin tsallan dadi mubeena tayi yayanta maimunatu yake so har yanzu ta kasa yarda,ita bata san irin zurfin cikin muna ba kai! Murna take yi har da rawa gaba daya ta manta da duk wani matsalarta.
Da sauri ta janyo wayarta ta kira sai dai ta taki rashin sa'a wayar a kashe.
Kwanciya tayi tare da kudurtawa zuciyarta gobe da sassafe ta gidansu zata bi ta dauketa suje office tare.

Marwan time ya duba ya ga har goma ta wuce wannan dalilin kadai ya hana mishi zuwa gidansu maimunatu a wannan daren ya kira wayarta bila adadin amma a kashe da zai iya sammakon zuwa gidansu da gobe a nan zata tsince shi amma zai jira zuwanta a office dinta ai b'oye b'oye ya kare tunda ya fara bayyanawa yan uwansa yanzu mufl ce kawai bata sani ba.

Maimunatu kam a ranan suka wuce Zaria zuciyarta fal farin ciki bata taba tunanin zata tsinci kanta a cikin farin cikin da ta riski kanta ba dan zata ga dangin mahaifiyarta this is not her first toh ita ko ta je ma bata iya sakewa dasu amma ganin aunty khadija duk sai taji kaman taga mahaifiyarta duk da kasancewar aunty khadija ko kusa da haifanta bata yi ba dan duka duka bata fi 30 years ba.

Murmushi tayi ta mayar da kanta ta kwantar jikin seat tana tuna wayarsu da uncle sufyan kafin ta sakko da kayanta kasa.

"Munari kin koreni karfi da yaji,kin daureni da jijiyoyina i never know u are this smart."

Murmushi tayi dan ta san me yake wa hakan amma sai  tace "ni kuma yau me nayi uncle?"

"Meye ma baki yi ba maimuna? Kin cewa mahaifinki na san da zuwan manema auranki shi yasa nace ya tambayeki,haba munari wannan ba cin fuska bane?"
Dan turo baki tayi tace "ah ah uncle sam ni ba zan taba iya ci maka fuska ba kawai na rasa madafan da zan dafa ne da daddyna ya tambayeni sakon da kace zan bashi,uncle sosai ka saka ni a tsaka mai wuya wannan hanyar ita kadai ce mafitana dan ba zan taba iya kallon idon mahaifina ince mishi amininka wai yana sona da aure ba. Uncle ka auna ka gani pls."

Goron nunfashi ya sauke yace "toh ai shikenan maimunatu Alllah ya sa hakan shi yafi alkhairi yanzun kam ai dole in janye ina ni ina takara da cptn moh yaro matashi me ji da kuruciya sannan ga yan kobonsa a aljuhu wannan ai mijin manyan mata ne irin maimunatu."

Murmushi tayi tace "hmm uncle kenan." Yace "ahan zata fara ba,na barki lafiya mrs moh." Daga haka ya kashe wayar itama tsaki ta ja da ta tuno da marwan da matsalarsa wannan ya sa ta kashe wayrta gaba daya ta wurga ta kan gado ta cigaba da shirin wanda yayi sandiyar manta wayar tata gaba daya.

Tsaki tayi a fili aunty khadija tace "ya dai? Ko duk haushin manta wayr ne ko ana fargaban haduwa da dangi?" Dan murmushi tayi tace "wayar dai aunty." Murmushi tayi mata tace "karki damu gobe sai mu sa daddynki ko a motane ya turo mana dashi kar surukin mu ya kira bai ji ba hankula su tashi " dariya tayi tana boye fuska tace "ni Allah ba wani suruki kawia dai ban samu na gayawa boss dina bana za ayi expecting ganina a aiki gobe ." Duk da ta san ko bata yi tafiya ba bata da niyyan zuwa office ba ita da office sai ranan clearance dinta na karshe .

Aunty khadija ta katseta ta hanyar cewa "uhn uhn ke dai abinda naji ance ma boss din naki gaba daya shine surukin namu."
Waro idanu tayi tana mamaki a hankali tace "daddy ya koyi surutu..."

KINA RAINAWhere stories live. Discover now