page 21.

1.9K 149 29
                                    

💖KINA RAINA💖


By Sawwama A.




Wattpad @sawwama14







Page 21.









"Dan sandan farin kaya kuma?" Maimunatu ta tambaya tana wanke hanunta a cikin bowl. Da sauri Rabi ta iso gabanta ganin tayi nasarar janyo hankalinta da labarin dan kowa ya san mutuncin dake tsakanin maimunatu da khalid.

Cike da zumudi Rabi ta cigaba da bata labari "eh wallahi wai ashe badda kammanni yayi dan su kama alhaji wada saboda ana zarginsa da ajieye miyagun kwayoyi a cikin gidansa shine ya yazo ya kama kofar shagon saboda ya san shige da fice na gidan,ai kuwa ya aka yi ya aka yi muna zaune kawai muka ji karan jiniya ta ko ina a anguwan nan ai fa aka firfito kallo inda jami'an tsaro suka shiga har cikin gidan suka fito da alhaji wada tare da yaran da suke masa hidimomin kwayoyin ga kuma tulin kwayoyin da aka fito dashi har da hodar ibilis,shi kuwa me shago na tsaye hannunsa rike da bindiga sai turanci yake yi abin dai kaman a film gwanin ban sha'awa." Rabi ta karasa maganan tana hadiye yawu dan tunda ta fara maganan sai lokacin ta samu daman hadiye miyau.

Maimunatu kam banda mamaki babu abinda take yi wai Khalid ne SSS abin kam da mamaki kana tare da mutum baka san waye shi ba, shi yasa wulakanci bashi da amfani cos baka san inda mutum zai maka rana ba.

Haka kawai taji ina ma zata ga khalid amma ta san hakan da kaman wuya tunda ya gama abinda ya kawoshi anguwarsu.

Ganin tunani zai mata yawa ya sa ta sallami rabi ta nemi waje ta kwanta.

Maimunatu ta sha mamaki da har aka wayi gari momy bata hantareta ko ta goranta mata wani abu ba haka daddy ya sakko bai nuna mata akwa wani damuwa ba.

A hankal rayuwar maimunatu ta fara dawo dai dai hatta ga tunanin marwan tayi kokarin hana kanta and alhamdulillah tana samun nasara akan haka ta cireshi a rayuwarta sai lokaci lokaci ya kan fado mata a rai.

Sosai take mamakin halayar da namiji babu wanda zai taba cewa marwan yaudararta yake a yanda ya nuna damuwar sa da kulawarsa akanta ashe duk karya ce she was just helping him past time tunda gashi da zamarsa ya kare a kasar ya tafi ko waiwayan ta bai kuma ba ko da a ce irin na dan kwan biyun nan ne,no! Yanda ya bar kasar haka ya bar rayuwarta shiyasa itama ta bar duk wani abu da ya shafi rayuwarsa a cyprus sai abu biyu da ta kasa barinsu kuma ta kasa sanin dalilinta na yin haka.

Agogon da ya bata ya na nan a cikin jewelry box dinta haka teddy bear din shima ta adana sa a cikin drawe dinta kullum tana kara godewa Allah da yasa soyayya bai rufe mata ido ta bawa marwan kanta ba lallai da ta tabbata kukan da zata yi me yawa ne.
Har kullum tana dana sani,da kuka hade istigfarin abinda suka aikata ita da marwan tana tir da wannan halim turawan da ta ara ta yafawa kanta tare gudunmawar marwan dan shinw ummul aba'isin lalacewarta marwan ya cutar da rayuwanta ya koyawa gangan jikinta abubuwa da dama wanda a halin yanzu in sha'awa ta motsa mata bata taba sanin yanda zata yi da rayuwarta.

Ta kan tsinci kanta a matsanacin son kasancewa da marwan ko da kuwa kwamciya a jikinsa ne kawai.
In ta tsimci kanta a wannan halin sai dai tayi ta kuka tana aikawa da marwan Allah ya isa.

Ganin zaman gidanta na yawa babu inda take zuwa tunda ba a resume school ba ya sa ta cewa daddy tana so ya kaita ziyaea danginshi da na mamanta sosai yayi murna dan dama shi daddy irin mazan nan da in ba wai kai ka nuna kana son abu ba hankalinshi baya kai mishi ayi.

Ai kuwa a satin ya shirya mata tafiya ta tafi ziyara sosai danginta suka yi farin ciki da ganinta kowa sai nan nan yake da ita.

Itama taji dadin shiga cikin yan uwanta ta sake da cousins dinta sun sharing numbers.

Daga nan kuma gidan uncle sufyan ta tafi tayi kwana biyu mami matarsa kamar zata hadiyeta hakan yayi wa uncle sufyan dadi sosai,abinda take so shi ake yi a gidan. Haka kawai zai ce ta shirya ya fita da ita outing wurare dabban dabban sai hotuna suke yi a wayarsa kaman wasu couple tun tana jin kunya har ta sake.
Bata tashi dawowa ba sai da school aka resuming ta dawo ta fara karatunta ka'in da na'in sam bata kula shirgin maza duk saurayin da zai zo da sunan yana sonta zata fatattakeshi saboda nacin samari ta koma masifaffiyar karfi da yaji dan bata son sam abinda zai hadata da mayaudara a cewarta.

In tace haka sai course mates dinta ko cousins dinta suyi ta mata fada suna cewa ai ba ko wani namiji bane mayaudari ko me take nufi? Aure ne ba zata yi ba kome kasancewar basu san marwan ba mutum daya ne ya san da labarin marwan ba kowa bace face jalila da zumuncinsu ya cigaba.

Babu wanda ya san labarin marwan sai ita,ita kadai ta san irin kin da maimunatu take yiwa marwan dan ta tabbatar mata ko a lahira bata kaunar ganin ko me kama da marwan saboda ya cutar da rayuwarta marwan yayi mata miki me wuyar warkewa.

A wannan yanayin ne maimunatu ta samu ta kamala karatunta inda ta samu BSc dinta akan kasuwanci sosai babanta yayi farin ciki da samun wannan ci gaban yayi kuma alfahari da ita a ranshi yana ganin  maimunatu zata tallafa masa a sha'anin kasuwancinshi ita kuma a nata bangaren sam bata sha'awar aiki a karkashin daddy dan ta san abinda zai kara hura wutan tsana a tsakaninta da momh kenan yanzu ta samu abu ya sassauta bata so abinda zai ballo mata ruwa,abin gabanta yafi karfin rigimar momy.

Tana fara service zata fara raba cv dinta ko kuma zata yiwa uncle sufyan magana in lokacin yayi.

Wata rana tana kwance tana karanta wani littafi 'RUMASA'U' a wayarta tana jinjina irin halin kuncin rayuwar da tauraruwar littafin take ci wayarta ta fara ringing dubawan da zatayi..............

KINA RAINAWhere stories live. Discover now