page 24

1.9K 192 64
                                    

💖KINA RAINA💖











By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14









Page 24.









A rikicd take bin rubutun dake rubuce 'The famous dictective Dan fulani is getting hitch on 19/5/20' cikin rawar jiki ta bude notifications dinta duk inda ta bi abinda yake threading kenan hotunan khalid tare da wata farar budurwa tsayuwa fadan kyan yarinyan ma b'ata baki ne fara ce kal da ka ganta kaga bafillatana usul.

Hotunan gasu nan birjik in different styles da ka gansu kaga masoyan da suke son junansu.
Kur ta kurawa wani hoto da suke tsaye ya rike kugunta suna kallon juna suna dariya.

Sam maimunatu ta kasa tantance halin da zuciyarta take ciki abu daya ta sani mamakin khalid ne ya cikata menene dabararsa na furta mata kalman so? Toh ko dai wasa yake mata ta dauki abin da gaske? Lallai kuwa da ya mayar da ita shashasha.

Tana cikin wannan tunanin ya bude murfin motar ya shigo yanayin da ya ganta ya sha jinin jikinsa.

Kwata kwata ba haka ya so abin ya zo ba,one thing with being famous kenan  abu daya na fita shikenan naka ya kare,ya so ace ya bayyanawa maimunatu soyayyar amma ya rasa ta inda zai fara fada mata yana sonta da aure amma sai ya auri y'ar uwarsa kafin ya aureta,amma me bayan ya ja kunnan Habiba sosai akan kar ta fitar da pre wedding pictures dinsu sai a week to bikin amma saboda kunnen kashi ne ta turawa laure kanwarsa ita kuma ta dora a stories dinta na social media daga nan kuma 1 to tell ten,10 to tell others.

Wayarta ya leka ya ga hoton da take kallo take ya rintse ido yana addu'a ranshi,bude idon da zai yi ya ga idon maimunatu k'ur akan fuskarsa tana murmushi kafin yayi magana tace "congratulations Allah ya sanya alkhairi" daga haka ta sa hannu ta bude murfin motar tana shirin sa kafarta a waje ya rik'o hannunta tare da fad'in "wait!" Kallon hannunsa da yake rike da nata ta kalla sannan ta kalleshi abinda bai tab'a attempting yi ba kenan da sauri ya saketa ta fice.

Cusa hannunsa yayi cikin kwantaccen  suman kanshi na asalin fulani yana cakudawa shi kam yanzu ta ina zai fara? Baya son ya rasa maimunatu a karo na biyu gaba daya yayi shirme da bai gabatar mata da maganan aure ba har maganar ya fito bai sani ba zata amshe shi a haka ko yaya?

Ya san ba karamin sa'a yasha ba da bata kwasa mishi mari ba,dan ba ko wacce mace bane zaka gama gayawa kalman so kuma ta tsinci maganar aurenka a lokacin,ba ko wacce mace bacce za ta dauki abin da sauki da yawa zasu fassarashi a rainin wayo which shi gaba daya ba nufinsa ba kenan.

Ya so ace bayan ya gama zayyana mata soyayyarsa sai ya fito mata da kalubalen da ke tunkararsu sai wannan wayar da ogansa yayi mishi ya katse masa hanzari har abubuwa suka jagule masa, wayarsa yake kallo kaman ya danna kiran layinta sai ya fasa "she needs space ya fada a hankali." Da wannan tunanin ya ja motarsa ya bar kofar gidan

A bushe take jin zuciyarta tana jin ita kam inshaaAllah ta gama kuka akan wani d'a namiji just when she thought she is going to be happy boom sai ga pre wedding pictures dinsa ke yawo
Hhhhh toh ya aka yi ma bata taba zaton haka ba.

Sam bata wani ji haushinsa ba,she did'nt expect after like five years da tafiyanta babu labarinta ya zauna babu wata a rayuwarsa yana zaman jiranta alhalin bai san zata dawo ko ba zata dawo ba and bama soyayya suke yi ba
Haushinta daya yana da daman fada mata hakan bayan haduwarsu  amma bai fada ba sai ma ya fito da wani salo wai yana sonta,yana sonta ya hadadu yake nufi kenan ko me? Lallai yana bori

Kara juyi tayi akan gadonta tana latsa wayarta duk inda ka duba hotunansau kawai kake gani da wanda ya sani posting hotunan suke dan tabbas hotunan sunyu kyau sun dauku da yake an dace daga angon har amaryar kyawawane na bugawa a jarida who is she to compete with this damsel? Kara kallon smile din dake kwance akan fuskar yarinya mai suna Habiba tayi a fili tace "lucky you."

Message din Mubeena ne ya shigo wayarta ta status.

Miss Mubeena :_"ke wai da gaske dama ba soyayya kuke yi da dan fulank ba?"_
Murmushi ta yi tare da bata amsa da
_"eh"_
Miss mubeena :_"yanzu naga prewedding shots dinsa a tweeter sai da gabana ya fadi."_
Dariya maimunatu tayi ta replaying mata da
_"toh gabanki ya daina faduwa ba soyayya muke ba balle kice ya yaudareni._" taji kaman ta gaya mata abinda ya faru tsakaninsu sai taga rashin amfanin haka kun santa da zurfin ciki.
  Emojis na sad faces ta turo mata can kuma ta turo da
Miss mubeen : _"Allah ya sani na soki da bawan Allahn nan and fron the way he ia looking at you wallahi yana sonki and zaki ce na fada miki muna tare."_
Shiru tayi taba kara nanata karanta message din mubeena dan tabe baki tayi tace "toh in ma yana sona sai dai ya hakura with the way they are looking happy ba zan zo in shiga ciki ba."

Shiru tayi tana tunanin yanda kawai ta hakikance khalid na sonta deep down tana jin shi zata aura she is just waiting for him to confess his love to her dan kaman yanda mubeena tace her love is written all over his face ba mubeena kadai ke fadan haka ba duk wani da zai gansu tare sai yayi maganan yanda yake nuna kulawa akanta.

Call dinshi ne ya kara shigowa wayanta for the tenth time kife wayar tayi a kirjinta dan bata shirya yin magana dashi ba yau sai da ya gama ringing ta dago da wayar.
Haka tayi ta juye juye har kusan sha biyu tana shirin kashe data dinta taga mubeena tayi status,na farko ta bude
_happy birthday to best brother in the whole wide world._
Sai na gaba kuma hoto ne da yaki budewa saboda network a kasa an rubuta _yau kam i will post ur picture ko da na 5 mins ne_

Haka nan taji tana son ganin hoton mamallakin moh interprises.
Kiran uncle Sufyan ne ya shigo wayarta murmushi tayi dan ta san tayi laifi ya bar kasan ko sau daya bata kirashi ba.

Picking call din tayi bakinta dauke da sallama.


#team khalid
#team marwan
#team sufyan

Alhamdulillah gobe birthday na.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now