💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 39
Waro idanu maimunatu tayi bata san lokacin da ta damko hanun mubeena ba tace cikin rawar murya tace "ban gane ta kawar da budurcinki ba yau mun shiga uku,fyade yayi miki ko mi?"
Girgiza kai mubeena tayi fuskanta dauke da murmushin takaici idonta cike da kwalla tace babu ko daya.
"Kin sani Tahir kanin baban ikram ne ko?" Gyada kai maimunatu tayi cike da zakuwa numfashi ta sauke tace"Alhaji buba daura shine mahaifinsu abokine wajen daddyn mu tare suka yi secondary har university daga baya kuma kowa ya kama aikinsa inda alhaji buba yake aiki a state govt na Katsina yayin da daddy ke aiki a nan Abuja.
Amma ana ziyarta juna sosai a haka har alhaji buba ya dawo abuja da zama yaransa biyu yah Abdul da Tahir da girmanmu suka dawo abuja inda lokaci daya yah abdul ya nuna yana son adda mufliha iyayenmu sunji dadi sosai ba a jima ba aka sha bikinsu kasancewar ta riga da ta gama makaranta lokacin shima yah abdul din yana aikinsa.
Ban wani san Tahir ba cos time din yana Australia yana masters dinshi bai tashi zuwa ba sai lokacin bikinsu adda mufli tunda ya kyallara idanunsa akaina shi kenan ya hanani sukuni na san zuwa yanzu kim san cewan Tahir mutum ne me barkwanci da saurin shiga rai tun ina ja mishi aji har nazo na saki jiki dashi muka fara soyayya me zafi.
Dan Tahir ya rungumeni ko ya pecking dina ba wani abu me wuya bane a wajensa tun ina nokewa har na saba da intimacy din namu ya zamana ko bai rungumeni ba ni zan shiga jikinsa in sakar masa shagwaba iri iri.
A cikin wannan yanayin ne abin namu ya kara tsamari inda ta kai ta kawo Tahir zai kissing dina son ranshi wani sa'in har hannunsa suyi yawo cikin jikina
Wallahi hakan ba karamin tsoratani yake yi ba amma in na duba yanayin girmansa da kasashen da ya ziyarta da kasashen da yayi karatu sai in ga hakan ba komi bane a wajensa.Wata ranar monday lokacin ina gab da zana finale exams daidai da lokacin da ya rage saura 2 weeks Tahir ya koma makaranta shima ina cikin makaranta yazo ya daukeni,bai zarce dani ko ina ba sai gidan adda mufliha kasancewar sunje bikim suna ita da momynsu Tahir din so gidan babu kowa girki ya sa nayi mana yana tsokana na in munyi aure haka zamu zauna mu biyu a yanzu haka ma jin shi yake kaman munyi aure.
Bance komi ba banda dariya da nayi bayan na gama girki ina wanke abubuwan da na bata ban ankara ba tsam naji an daukeni bai direni ko ina ba sai dakin dake manne da palon cakulkuli ya fara min ina dariya tare da kokarin zillewa sai da ya kashe min jiki sannan ya fara aika min da wani romance me zafi da kashe jiki.
Ban ankara ba ya rabani da kayan jikkna tare da nashi kafin in farga da abinda yake yi tuni ya fara neman hanya rokan sa nake yi amma sam bai saurareni ba sai da ya samu biyan buqatarsa." Ta karasa fadin haka tare da fashewa da wani irin kuka maimunatu ma kuka take yi bakinta na furta innalillahi sabida ji take yi wannan labarin shigen nata.
Marwan kam notin kansa tuni sun kunce daga kafarsa yayi da niyyar shiga inda suke sai yaji mubeena ta cigaba da fadin" ko kin san tun daga ranan Tahir ya mayar dani kaman matarsa?" In na nuna mishi ban son abinda yake yi sai ya hau fushin ai shi zai aure ni (katuwar kalmar yaudarar kenann Allah ya raba na gari da mugu) shi in banda lokaci ya kure da babu abinda zai hana bai tafi dani a matsayin matarsa ba.
Haka ya kwashe sauran kwanakinsa yana moreni har ya tafi. Toh sai de me? Yana tafiya sai ya canza min baya kirana ko na kirasa sai ya ga dama ya dauka in kuma ya dauka dai yace min karatu yake yi zai nemi ni toh fa shikenan ba zan sake jin duriyarsa ba.
Wata rana na kirasa sai nayi sa'a ya picking ina mishi magana sai naga kaman ba a cikin hayyacinsa yake ba infact ina iya jiyo saund din kiss in nace kana jina sai yace uhmm? Mmm ke da ga karshe ma sai naji saukar numfashin mace hakan ya nuna min yana tare da wata macen ne ashe Tahir sha'aninsa kawai yake yi ya manta da wata mubeena a irin wannan yanayin ne na gane yazo Nigeria bashi da abin debe kewa ne yace yana sona har ya hillaceni ya samu abinda yake so.Tun daga wannan ranan ban kara bin ta kan Tahir ba na cigaba da sabgogina ina neman tuban Allah nayi kuka har naji ba dadi katsam ba sai na fara ciwon mara ba me azaban radadi ga wani itching da gabana yake yi yana fitar da ruwa me kauri ba nasha anti biotic sai abu yayi kaman ya tafi sai ya dawo gashi banga period dina ba ai sai tsoro ya cikani.
Ba shiri na nufi general hospital dan ban ma san wani a gida ya fuskanci halin da nake ciki sai aka yi rashin sa'a likitan da zan gani na mijine kallo daya nayi mishi zuciyata tayi wani irin bugawa wani kunyarsa duk ta lullubeni tambayata yayi me ke damuna nace ciwon mara ya tambayeni ko na al'ada ne na girgiza kai toh fa tun daga wannan duk tambayar da yayi min na kasa ansawa yayi yin duniyar nan amma ni mubeena na zama kurma a gaban likita dan wani mugun kwarjini yayi min.
Karshe dole da nurse ya hadani tayi min tambayoyi sannan taje ta gaya masa tests ya rubuta min naje na yi na dawo na kawo mishi ya dade yana kallon reports din kafin ya dago yana kallona
"Kin taba aurene?" Shine tambayar da yayi min wanda ya hautsina tunanina shikenan ni mubeena yau na yo cikin shege. Cikin rudu na girgiza mishi kai tare da fara hawaye tissue ya cire ya mika min yace "toh meye kuma na kuka daga tambaya? In baki taba aure ba me ya hadaki da STD (sexual transmitted disease) waro idanu nayi na kife kaina jikin table dinsa ina kuka sosai tare da sambatun da ni kaina ban san me nake fada ba da kyar likitan nan ya shawo kaina na fada masa me ya faru ya tausaya min sosqi ya kuma yarda ni ba fasika bace ya dade yana min nasiha tare da nuna min illan abinda na aikata.Magunguna ya rubuta min tare da allurai sannan ya ansa number na yace bayan 2 weeks in dawo.
Haka nayi ta shan magani da allurai har na warke ranan da yace in dawo na koma aka kuma yin test inda saura kadab ya rage a jikina kawai ba tare da shawara dani ba yasa wannan nurse din tayi min stitches ko da ta dubani ta fada mishi bana buqata wallahi ba karamin kunya ne ya rufeni ba. Na san taimakona yake sonyi.A haka shakuwa me tsanani ya shiga tsakanina dashi gefe daya soyayyar na nukurkusa na amma bani da yanda zanyi tunda shima bai fito yace yana sona ba har sai da muka kwashi shekara guda dashi sannan ya fada min yana sona yana kuma son in bashi izni ya nemi aurena ban tsaya wani jan aji ba na yarda aka sa auranmu 18 months wanda yau bai fi saura 5 weeks ba.
Bayan sa auran mu da watanni biyu Tahir ya dawo inda ya tsinci labarin aurena a bakin yayansa ya so ya ci min mutunci da barazanan in ban dawo gareshi ba duk wanda na aura ba ganin mutuncina zai yi ba tatas nayi mishi na huce haushinsa da nake ji ranan shine yanzu zai lallabo yace yana sonki dan ya rainawa kansa hankali dan Allah maimunatu ki rabu da Tahir wallahi bana son abinda zai taba mut...."
Bata gama rufe baki ba taji an shakota tare da kyalla mata mari ko kafin ta dawo hayyacinta an jata zuwa office dinta an rufo kofa......
Manage