💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 22.
Murmushi ta saki tare da ansa kiran a hankali tace "uncle sufyannnn." Limshe idanu yayi yana jin muryarta na ratsa kwanyarsa.
"Munari! Munari kin k'i ki ban dama,why maimunatu?" Wani murmushin tayi tace "uncle sufyan kenan,ya su mami da sauran yan gidan?" Girgiza kai yayi kaman yana gabanta hade da zuba uban tagumi yace "as usual kina avoiding maganar nan maimunatu,na tabbata in har kika ban dama mami da kike tsoro will never be a problem na rasa tsoron me kike ji,ko ni ne dai ba kya so nayi miki tsufa?" Dariya tayi a nitse cikin kunya tace "ni wallahi umcle sufyan kana sa ni jin kunya."
Murmushi yayi yace "ke dai munari fadi gaskiya kawai ba wai mami ke baki tsoro ba nine nayi miki tsufa,daddynki fa ya girmeni,baki ganin sai yanzu farooq ya shiga jami'a ke kuwa duk da delays din da kika samu amma har kin gama,kinga ko ai ban kai daddyn mu shekaru ba."
Zuwa yanzu kam dariya take yi sosai dan ita dariya abin yake bata da mamaki wai uncle sufyan ke sonta har ma yake kokarin yaga ya burgeta ko da yake ba abin mamaki bane namiji ne shi su ba kunya garesu ba akan diya mace. Ba ta ce komi ba ban da "hmm uncle kenan."
Ya san ba zata taba bashi sahihin amsa ba ya san tana jin nauyin tace mishi bata sonshi ne and yet ba zata taba iya auransa ba,shi ya rasa dalilin da ya sa mata suke son haramta abinda Allah ya halasta saboda wata al'ada ya sani sarai in ya samu abdul da batun yana son diyar sa ba tarr da kyafta ido ba zai bashi ita but shi baya son yi mata dole yafi son on her own ta soshi ta yarda da auransa which he doubt hakan zai taba faruwa.
"Uncle ya office daddy yace kwana biyun nan aiki yayi maka yawa, gashi muma mun kusan shiga camp." Dan tattare gira yayi yace "oh haka ne fa i almost forget,ai ke kina Abuja abinki so baki da matsala, kinje kin duba company din da zaki yi serving kuwa? " dan tabe baki tayi tace "uncle i thought kai zaka kaini." Rolling idanunsa yace "sai kace wata baby? At 23 sai an raka ki? Its an official visit dole ki nuna jajircewanki akan abinda zaki je yi." Gyada kai tayi kaman tana gabanshi tace "toh shikenan uncle insha Allahu zan yi kokari inje *moh interprises* in gabatar da kaina."
Kayataccen murmushi yayi yacw "good thats my girl." Murmushi itama tayi tace "uncle kenan" da haka yayi ta jan ta da tadi tana amsashi sama sama dan ita sam bata son ta bashi impression din zata aureshi don ta san yanzu kowa maganan auranta ne ya tsone mishi ido tunda ta gama makaranta sam bata san ya zata yi ba.
Ba wai ta rasa manema bane ah ah haka kawai ba ta son abinda zai hadata da wani namiji marwan ya riga ya tambara ya'ya maza a wajenta yayi mata tabon da ya kasa warkewa,shine mutum na farko da ta taba so a da tayi tunanin khalid shine first love dinta sai da ta hadu da marwan ta gane ba son khalid tayi ba kawai a wajensa ne ta samu attension shi yasa.
Murmushi tayi tuno da khalid for quite sometimes tana following dinsa a social media,yes yanzu tana da accounts da social media tana following dinsa on twitter,facebook,instagram da dai sauransu tana ganinshi amma shi baya ganinta.
Yayi kyau ya kara zama well polished dan bafillatani tutor dinta sosai tayi missing dinshi ta san yanzu ma wata kila ya manta da ita.
So tari ta kan attempting yi mishi magana ta dm but ta kasa sai dai kawai ta bi tweets dinsa da sauran posts dinsa ta liking ta sani ba zai taba tantanceta a cikin dumbin likes dinsa ba ita kuma bata taba commenting akan wasu abubuwan da yake sawa ba she doubt in ma zai wa comments dinta kallo biyu duba da yanda yammata ke throwing kansu a kanshi. Murmushi ta saki Khalid kenan me shago ta fada a fili ko rufe baki ba tayi ba wayarta tayi wani marayan kuka dariya tayi tunowa da tayi a zamanin da khalid kadai ke yi mata flashing lallai khalid ya kware wajen basaja. Yanzu kam ta san ba kowa bace da ya wuce Rabi yar aikinsu kuma abokiyar hiranta dan har yau maimunatu bata da wata shakikiyan kawa in ka dauke Jalila itama da yanzu take shirin yin aure a dai dai lokacin da maimunatu take cikin camp kwarai tayi bakin cikin rasa bikin jalila toh amma ya bawa zai yi.