page 32

2K 196 58
                                    

💖KINA RAINA💖








By Sawwama A.







Wattpad @sawwama14






Page 32.





Daki maimunatu ta wuce ranta na yi mata tukuki gaba daya sai fruits salad din ya fice a ranta kuka ta fashe dashi ganin momy taci nasara akanta daman ta san dalilinta na takalanta fada kenan ai.

Shiru tayi tana kwance tana kallon roofing dakin tunani ne kala kala a ranta wayarta ce ta fara ringing a hankali ta janyota kasancewar tana kusa da ita Taheer ke kira dan guntun tsaki ta ja a hankali ta picking wayar tare da yin sallama
"Pretty shine kika gudu kika barni ko." Yayi maganan cike da shagwaba dan murmushi ta saki tace "ba guduwa nayi ba T kaina ke ciwo shine mubeena tace in dawo gida." Dan jim yayi jin ta ambaci sunan mubeena kaman wanda aka tsikara yace "ya salaam pretty sorryyyy buh ya jikin naki? Hope kan ya bar ciwo?" Limshe ido tayi tana murmushi dan ita tabararsa dariya yake bata tace "da sauki Taheer." Turo baki yayi kaman yana gabanta yace "uhm uhm ni dai T zaki ce min kaman yanda kika fara." A hankali ta dan yi dariya tace "T it is then."
"Yauwa nagode yanzu dai bari kar in kara miki ciwon kan kiyi bacci me dadi and also dream of me ko?" Cikin murmushi tace "ok,nagode nima" kiss ya blowing mata sannan ya kashe wayar dariya tayi tana kallon fuskar wayan yana tuna mata da zamanin zamanta da marwan a cyprus gabanta ne ya fad'i tunowa da tayi Marwan fa ya dawo rayuwarta and da alama ba zai barta ta shaki numfashi mai dadi ba.

Moment dinsu na dazun ta tuno yanda ya wani cukuikuyeta dan ya raina mata wayo Allah sai yanzu ta kara tabbatar da tantirancinsa limshe idanu tayi tana comparing marwan din da da na yanzu marwan din da is a lil bit slim wannan is muscular kilan yanayin training ne na sojoji hmm she cant believe marwan soja ne toh tun suna tare ne ko bayan sun rabu ne cos apart from sanin da tayi shi doctor ne kuma yana studying medicine ba abinda ta sani game dashi bata ma taba sanin yana da sisters ba ko wani company hmmm.

Cigaba tayi da comparison dinta marwan da ta sani yana barin a very short beard wannan kuma babu gashi ko d'is a fuskansa he looked more huge kasancewan dama akwai tsawo to yanzu ga muscles sai dai a fuska he look younger idanunsa masu bata tsori sun kara girma sai yanzu take ganin kamansu da mubeena idanun nan nasu kwal kwal nashi ma ya fi nasu girma
Duk yanda ta so kar maganganun mubeena su dawo mata na rayuwar marwan sai da ya dawo mata she feels used,played ita ba komi bace facce wawuya one of his flings da bai samu ya keta ba yanzu da ya ganta shine zai dora daga inda ya tsaya.

Kuka ta fashe da shi tare da juyawa ta kife kanta a jikin pillow kuka tayi me yawa wanda ya saukar mata da zazzabi me zafi daren ranan ko runtsawa bata yi ba saboda zazzabin da ya rufeta sai rawan dari take haka ta kwana cikin mawuyacin hali sai gabannin asuba bacci ya dauketa bata farka ba sai wajen 10am jikinta a sanyaye ta sakko daga kan gadon tana me tausayin kanta ace an ga har goma tayi bata fito ba babu wanda ya leka yaga halin da take ciki? Yatsunta ta sa ta goge kwallan da ya zubo mata maraici bai yi ba da uwarta na nan ai da ta san halin da take ciki yanzu da mutuwa tayi kilan sai tayi wari za a san ta mutu.

Da wannan tunanin tayi alawla ta fito a zaune tayi sallah dan jikinta ba kwari wayarta ta dauka dan ta gayawa mubeena ba zata samu daman zuwa ba missed calls dinta ta gani Allah sarki mubeena dama haka rayuwa yake sai ka ga naka bai damu da kai ba amma wani bare ya dauki lalurarka ya sa akanshi.

Mubeena na zaune tare da Marwan a office dinta wayarta tayi kara murmushi tayi tace "kagani ma ita take kira dama na san haka kawai ba zata ki zuwa ba." Dan dama yanzu yake mata korafin ina sexretary dinta sun sani sarai ba ya son wasa da aiki,zuwa yayi ko ganin fuskar maimunatu yayi sai ya tarar da table dinta empty ba mamaki shi take gujewa.

Ajiye wayar tayi fuskarta da alamun damuwa tace "wallahi yayana jikin nata ne har yanzu." Dan tabe baki yayi dan shi ya sani sarai shi maimunatu ke gujewa ba wani rashin lafiya he just pray ta gama fake ciwonta kafin week din nan ya kare dan zashi military office dinsu na ibadan week me zuwa cikin kulawa yacewa kanwarsa. " kar ki damu she will be ok." Safeena ce ta dan knocking kofar kafin ta shigo gaisawa suka yi da mubeena kafin cikin yauki tace "yah ga nan sajidda diyar hajiya baraka ta haura office dinka." A hankali ya furta "wtf!" Ya mike tsaye ba tare da ya saurari kowa a cikinsu ba ya fice.
A tare suka ja tsaki sai kuma suka sa dariya ganin sunyi tsakin a lokaci daya mubeena ce tace "wallahi na tsani yarinyan nan su suke kara dulmiyal da yayana duk da dai yanzu ba ya biye musu amma ina tsoron shedan kar ya rinjayeshi."

A zuciya safina tace ni da zan samu ko da wannan sigan ya kalleni ai da naji dadi a fili kuma tace "hmm kema dai mubeena akwai son kai mace na bata namiji ne ai sai dai ma shi namijin ya rinjayi mace."
Dafe kai mubeena tayi tace "ke baki gane ba wallahi duk iskancin namiji sai mace ta bashi dama,mace kuma yanzu yanzun nan zata iya seducing namiji ta sigogi da dama kuma ya fada tarkonta shi yasa nake ganin in mata zasu kame kansu zina zata ragu." Gyada kai safeena tayi cike da gamsuwa tace "toh Allah ya dada shiryar damu ameen."

KINA RAINAWhere stories live. Discover now