💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 37.
Juma@ mufeeda to all Muslims ummah!
"And who are you to tell me what to do?" Ta fada tare da hard'e hannunta a kirjinta.
Tsaye ya mik'e daga durk'uson da yayi ya dafa table suits dinsa ya gyara yana murmushi yace "Ni ne Marwan mamallakin maimunatu,you know that better than i do." Baki ta tab'e tace "maimunatu bata da mamallaki har yau,sai mijin da ta aura shine zai zama mamallakinta but as for now babu wani d'a namiji da yake da iko dani."Ba tare da jin zafin magananta ba ya zagaya ta inda take tsaye yace "ni zan aureki miemie,a shirya nake na aureki ko da yau ne pls miemie ki daina wahalar damu ki sassauta wannan fushinnda kike yi mu fuskanci juna,me yasa kika bar cyprus? Ko kuma dont answer that let bygone be bygone pls miemie i really do love you and you know that." Ya karasa maganan cikin muryar da ya san yana kashe mata jiki.
Kwayar idonta ta saukar kasa hakan ya tabbatar mishi da trick dinsa worked,sosai maganganunsa da muryar da ya using ya ratsata amma in ta tuno da wahalar da ta sha na rashinshi duk sai taga marwan ba sonta yake tsantsan mayaudari ne kawai.
Wata yar karamar dariya tayi ta zaga ta fita daga tarkon da yayi mata tace "Marwan ni da kai mun sani ba ka sona jikina kawai kake so yanzu da kaga ba zaka samu ba shine zaka bullo min ta maganan aure? Toh anki a aureka marwan,ba ayi! Wai kai wani irin mara zuciya ne nace bana yi ko dole ne? Ni bana sonka ko wancan lokacin ma da na yaudaru a hannunka dan ban san me nake yi bane saboda haka ka fita hanyata bana sonka kuma ba zan tab'a sonka ba!" Ta karasa maganar ta na haki dan ji take kaman ta gudu ta boya kar ya dira a kanta.
"Karya kike yi munafuka! Karya kike yi! Kina sona kuma sai kin aureni,wallahi wallahi wallahi kinji na rantse maimunatu and ba zaki sa ni kaffara ba da iznin Allah i will make you mine sai ki aureni kin dau cikina kin haifa min yara."
Cikin ihun masifa tace "Allah ya tsareni da haifan yaran mazinaci wallahi ni ba zan aur....." Dal ya dane bakin dafe bakinta tayi idonta taf da hawaye a hankali tace "wannan mugunta ne." Kai ya gyada yace "eh saboda ba zan iya dukan mace,macen ma wacce nake so!"
Zumbura baki tayi tace "malam ni ka daina cewa kana sona dan jikina kake so ba ni ba,mugu kawai mayaudari,dan iska."
Waro mata kwala kwalan idanuwan sa da suje ladabtar da ita yayi yace"ni kike zaki?" Ita kanta bata san ta inda courage ya zo mata ba ta murguda mishi baki tace "kai ba mayaudari bane dan iska? Da ka samu dama da tuntuni ka gama da rayuwata shine yanzu zaka lallabo ka wani zo min da kalmar so da aure toh ka sake lale wannan jikin....." Ta nuna jikinta "ya fi karfin mallakarka.""In anyi magana sai kice jikinki nake so wanda in da naso ajiya dana a cikinki tun shekarun baya da na ajiye ke kin sani i never press akan son kusantarki da na dage babu abinda zai hana baki bani ba kin san me yasa? Saboda kema kina son abinda nake miki you enjoy every part of it,ai ba forcing dinki nayi ba you always moan my name and hold me tight in ecstasy ashe duk mu biyun yan iska ne Allah kadai ya san sleepless nights din da that i had dan in tayaki rike virginity din naki da naga kina so kaman ranki,duk dan karki accusing dina wata rana da sha'awarki kawai nake tsk tsk tsk had i know i would have fuck you to my satisfaction yanda ko ance miki maimuna rabu da Marwan sai inda karfinki ya kare." Ya fada a hankali yana limshe ido dan gaba daya ta sa mishi ciwon kai,kansa wani irin sarawa yake yi
"Ni ba yar iska bace,kaine dai dan iska ka koya min iskanci Allah ya tsiratar dani ba wai dan baka ga daman uhm uhm.." Tama rasa kalmar da zata using "uhm yin abu dani bane Allah ne ya kare ba wai iyawarka ba."
Bai ce mata komi ba ya juya ya fita dan ya lura in ya biye mata ranshi ne zai yi ta baci.
Yana fita reception din company din masu gulman abinda ya faru suka yi dip kaman anyi ruwa an dauke,bai saurari kowa ba ya saka kai ya fice securities dinsa suka mara masa baya. He cant believe takanas ya taso dan ya sakata a idanunsa saboda ya kasa samun sukuni amma ta sashi a gaba ta yaba masa magana son ranta.
Kansa ya dora kan kafadarta cike da damuwa yace "mami tace bata sona,tace ba zata aureni ba."
Hannunta ta dora bisa kansa tace"haba marwan ka zama namiji mana ka nutsu ka fada min me ya faru."Rintse idanu yayi ya kwashe yanda suka yi da maimunatu ya fada mata,itama nata idon ta rufe tana tunanin yaushe marwan zai bar wannan wutar cikin.
A hankali ta dago kanshi ta riko fuskansa da hannunta dukka biyu tace dubeni nan marwan bude idonsa yayi me kama da na mahaifinsa ya tsura mata ido mur ta sha tace "yaushe zan fada maka abu kaji? Ina ce nace maka ka barta har sai an nemi iznin iyayenta? Shine kaje ka aiwatar da son ranka ko? Toh madallah sai kaje ka nemawa kanka auren kai da karan kanka." Ta saki fuskansa tare da kau da kai.
A matukar rude ya dire guiwowinsa a kasa ya dafa nata yace " dan Allah mami kiyi min rai na tuba,na bi Allah na biki wallahi ba taurin kai bane na rasa yanda zanyi ne ina tsananin son miemie gashi ta kasa fuskantata mami ya zanyi? Mami dan Allah a dau wani mataki in ba haka zan iya rasa raina ko nutsuwata " ya fadi haka tare da dora kansa bisa cinyanta yana ji dama hawaye zai zubo masa ko zai ji saukin abinda yake ji.
Wani tausayinsa ne ya kama mami ta wani bangaren taji ina ma miemie zata ga halin da ta saka marwan kila ta tausaya mishi ta saurareshi,kila hakan zai ankarar da ita tsananin son da Marwan yake yi mata. Ta wani bangaren kuma ba zata so ta ganshi haka ba so vulnerable a ta dalilin soyayyarta ko dan kar tayi amfani da soyayyar wajen cutar dashi.
Kaman daga sama yace "mami wallahi ba sha'awarta nake ba,sonta nake yi mami zan iya zama da ita ko a yaya take amma taki ganewa mami tace ba zata aureni ba,ba zata hada zuriya da mazinaci ba,mami nafa tuba na tuba mami kullum cikin istigfari nake mami ni kam ma bana iya yiwa wata macen wannan kallon tun a kanta mami,ita kad'ai ne bana iya resisting tabawa...."
Cikin tausayawa tace "inda matsalar take kenan marwan ka daina taba ta ka daina kai hannunka jikinta ka tabbatar mata da tubanka,har kullum ina gaya maka ka bar wannan halin banzan saboda akwai ranan nadama amma sam baka ji ba yanzu gashi tun ba aje ko ina ba jikinka na gaya maka (ni kam nace bai ma yi nadama ba tukun) yanzu ka kwantar da hankalinka a halin yanzu ina ganin in daddynku bai gana da mahaifinta toh yana gab da ganawa dashi."
Da sauri ya dago kanshi fuskarsa fal annuri yace "mami pla kar kice min da wasa kike yi." Wani harara ta galla masa tace "ashe na dawo abokiyar wasanka." Shafa suman kansa da yake a saisaye yayi yana murmushi yace "sorry ma'am."
A ranan duk inda maimunatu tayi ma'aikatan company din binta suke da kallo kowa so yake ya san me ta taka tayiwa marwan wannan tijaran kuma har yanzu take cikin ma'aikatar amma babu daman tambayanta tun da ita tun dama can ba wani shaharariyar alaka ne tsakaninta da ma'aikatan wajen ba sosai suke shakkanta wasu na mata kallon mai girman kai wasu kuma na mata kallon miskila tunda tana girmama kowa daidai gwargwado in ka ga mai kushe ta ma is just envious.
Da dare tana kwance a dakinta tana kallon hotunan auran khalid dake ta trending a internet kiran daddy ya shigo wayarta kan tazo kasa yana nemanta.
Dogon hijabi ta zira kan kayan baccinta ta fita zuciyarta na dokawa adduanta daya Allah yasa ba uncle sufyan bane ya ballo mata rigima.
A zaune kan 3 seater ta sameshi shi da sarauniyar tasa kamar ko yaushe can gefe ta rakube ta gaishe dasu.Gyaran murya daddy yayi yace "mamana dazu da safe nayi baki." Dan tattare giranta tayi amma bata ce komi ba. Ya cigaba "sun zo min da son samun izni na,na zuwa nemawa yaransu marwan auranki,nace hakan ba wani matsala bane amma su ban lokaci sai na gana dake tunda baki sanar min da zuwansu ba shin ke kika turo su da amincewanki suka zo ko kuwa."
Tunda ya ambaci marwan ta gigice dan sam bata taba zaton marwan zai biyo mata ta haka amma in ya san wata bai san wata ba.
A hankali daddy yace "ke nake sauraro maimunatu " cikin inda inda tace "amm ni dai ni daddy toh ni dai ah ah." Cikin confusion yace "ban gane ke dai ah ah ba,ki min bayani dalla dalla."Cikin saurin magananta da sai tana rude yake fitowa tace "ni dai daddy bana sonsa............"
Una comments sai a slow these days 😭