*MUHAMMAD ALEE*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*_An tattagoni na dawo Allah yasa kar nai muku wasa😉_*
*01*Kana kallansu basai an tabbatar maka da cewa suɗin ƴan ta'adda bane, dajine wanda ya amsa sunanshi daji, wasu suna zaune suna shaye-shaye yayinda wasu kuma suna tsaye hannayansu da bindigogi suna ta faman waige-waige a dokar dajin tamkar marasa gaskiya, wata ƴar bukka na hango bukkar duk wani abun more rayuwa akwaishi a ciki, bayansu kuma akwai wata ƙatuwar bishiya wacca duk suka ɗaɗɗaure mutane a wajan a ƙalla zasukai goma, ɗaya daga cikin masu bindigoginne yazo inda wa ƴannan mutanan suke ya kalli wani yaro wanda bazai gaza shekara goma sha huɗu ba cikin lalatacciyar hausarsa yace "Ubanki bayashonki, dan mun gaji da ajiyanki a wajannan, aradun Allah mun ƙara maki kwana ɗaya idan har ba akawo kuɗi an ansheki ba kasheki zamuyi mu huta"
Jikin yaron nan ba abunda yake sai kyarma saboda tsananin tsoro da tashin hankali, jikinsa duk shatin bulalane yayinda goshinsa aka jimai rauni da kan bindiga, ba tare daya jira amsar yaron ba ya kaɗa kanshi yabar wajan tare da shiga wannan bukkar, yana shiga cike da girmamawa yace "Yallaɓai, yarinyar dakace ashatota har yanzu uban yarinyar bai bayar da kuɗin ba gashi yanzu mun kwashi kwana biyar dashi, na tabbatar mata da shewar inhar ubanshi bai kawo gobe ba zamu kasheta...."
Kasa ƙarasa maganar yayi ta dalilin wani uban kallo dashi ogan nasu ya jefeshi dashi, ba tare da ɓata lokaci ba yayi saurin barin bukkar yana sinsin dakai, lumshe kyawawan idanunsa yayi tamkar baya ɗaya da dga cikin masu garkuwa da mutane domin fuskarsa sam batai kala data mugayan mutane ba, fuskarsa ta kasance kamilallah da natsuwa, kana kallan yanayinsa zaka ga komai yana yinsa ne cikin natsuwa, wayarsa dake kan wani ƙaramin Stool ya kalla ganin saƙo ya shigo wayarsa yasa shi ɗaukar wayar, message ɗin da akaine yasashi miƙewa tare da ɗaukar makullin mota ya fita daga bukkar nan.
Sauran fulanin ganin ya fito yasasu gabaki ɗaya zuwa inda yake cike da girmamawa, kallan ɗaya daga cikinsu yayi ga dukkan alamu shine babban jagora a cikinsu, yin gaba yayi yayinda shi kuma ya mara masa ba, jingina yayi da jikin motar harɗe da hannayansa a ƙirjinsa yana jiran ya ƙaraso, cike da girmamawa wannan bafulatanin ya ƙaraso inda yake yana faman sinna kai, gyaran murya yayi tamkar bayaso ya furta komi, cikin sanyin muryarsa mai matuƙar daɗi da sauraro yace "Dan Allah Baffah karku taɓa matan can, nasan halinka kaida Modibbo, banaso kuna yunƙurin lalata dasu, karku bari na ƙara kamaku da aikata hakan bazan muku da daɗi ba"
Shiru yayi yana faman haɗiye Saliva ɗinsa daga gani magana na matuƙar yi masa wuya, saida ya ɗauki a ƙalla 5 minutes sannan yace "Ku basu abun buƙata banason kuna dukansu, ajiyesu kawai nace kuyi da zaran an kawo kuɗin fansa mu saki mutum yayi gaba abunsa"
Baffa duk maganar da yake masa kansa ƙasa yana sauraransa cike da girmamawa, cikin hausarsa ta fullanci yace "Shikenan Oga an gama insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba"
Tashi yayi daga jikin motar ba tare daya ƙara cewa uffan ba ya shiga motarsa bundle ɗin 1k ya ciro ya miƙa masa yace "Zaka iya aiken Joseph cikin gari ya siyo muku abubuwan da kuke buƙata naga ba kuɗi a hannunku"
Ansa yayi da hannayansa guda biyu tare da yimai kirari, shi kuma ya shiga motarsa ya figa ba tare daya ƙara ce masa Uffan ba.*KADUNA STATE*
*_Birnin Gwari_*Ganin yadda Student ke fitowa daga cikin makaranta zai tabbatar maka da cewar tashi akai, wasu ƴan matane su uku suka jero gabaki ɗayansu sunyi kyau matuƙa Hijab ɗin Islamiyar ba ƙaramin kyau yayi musu ba, sede gabaki ɗayansu babu kai cewa kowa Uffan saidai kana kallan fuskokinsu zaka tabbatar da basu da matsalar rayuwa, saida sukazo gab da inda ake ajiye motoci wata ta yaye Hijab ɗinta ta miƙawa ɗaya daga cikinsu wani littafi tace "Karɓa naga anzo ɗaukarki kar in manta na tafin miki dashi gidanmu na banu"
Wacca aka miƙa ma Book ɗin ansa tayi tai murmushi tace "Besty kenan kedai akwaiki da tsoro maye dan kin tafi dashi gida"
"Uhmm" kawai tace wacca aka kira da Besty tana ƙoƙarin barin wajan, ɗan ruƙo Hijab ɗinta tayi tace "Wai me kike nufi?, nufinki bazaki hau muyi dropping ɗinki a gida ba"
Ƴar dariya tai har saida ɗan siririn wutsiryata ta bayyana tace "Azmah kenan, ni wallahi dariya kike bani" ɗan leƙawa tayi tana hango anguwannin tace "Kalla fa ina hango gidanmu me zai kaini hawa mota kuma?, a beg ku tafi kawai"
Ɗan ɓata rai Azmah tayi fuskarta ba walwala tace "Dan Allah Amina ki mata magana"
Amina ɗan taɓe baki tayi tace "Ai kunfi kusa" domin kuwa ba ƙaramin tsanarta Amina tayi ba ganin yadda Azma take matuƙar ji da ita"
Azmah tace "Au haka ma zakicemin?" ta faɗa tamkar zatai kuka, banza da ita Amina tayi ta zagaya ta buɗe Seat ɗin baya ta zauna tana faman hura hanci.
Zuhura murmushi tayi ba tare datace uffan ba ta buɗe motar itama ta shiga yayinda Azmah ta mara mata baya suka shiga, Driver ganin sun shiga ya tada motar suka tafi, domij kuwa inda sabo ya saba tsayawa su gama musun su, shidai harga Allah Zuhra na matuƙar burgesa ganin yadda take da hankali da natsuwa, tafiya kaɗan yayi yay Parking a ƙofar gidan su Zuhura, Zuhra cikin sanyi murya tace "Nagode Besty ku gaida gida"
Murmushi Azmah tai mata yayinda Amina ita kuma taja wani dogon tsaki tare da gyara zamanta, tana ƙarewa gidansu Zuhura kallo tare da tsirtar da yawu, ganin babu ƙofa ma a gidansu Buhu akasa aka rufe ƙofar gidan dashi, yayinda katangar gidan bata da tsayi ko kaɗan inhar kana da tsaho saika hango duk abunda ke cikin gidan, girgiza kai Azmah tayi yana mai mamakin hali irin na Amina.
Da Sallama Zuhra ta shiga cikin gidansu, fuskarta ɗauke da murmushi ta matsa inda mahaifiyarta take girki a tsakar gidan tace "Mama Ina wuni?"
Mahaifiyarta kallanta tayi cikin so da ƙauna tace "Lafiya ƙalau ya makarantar?"
"Alhamdulillah" cewar Zuhra ta miƙe ta shiga wani ɗaki dake cikin tsakar gidan ƙofar ta galan-galan ce ciki ɗaya ga dukkan alamu nan ne ɗakinta, bata ɗauki wani lokaci mai tsayi ba saiga ta canza kaya jikinta sanye da ƙaramin Hijab ga dukkan alamu ya saba irin wannan shigar a cikin gidansu, duk da gidan babu Kitchen a tsakiyan gidanne aka saka duwatsu guda shida ko wani side guda uku hakan na nufin murhun tuwo da miyane, janyo ƙaramar kujerar dake kusa da kwatan tsakar gidan tayi tace "Mama yau Yusha'u bai gyara kwatannan bako?" ta faɗa tana ɗan toshe hancinta jin yadda wari keɗan busowa zuwa hancinta.
Mahaifiyarta hankalinta kacokan yana kan dankalin hausan datake dafa musu tace "Zuhra kema kinsan halin Yusha'u in bake ba ko mahaifinku ba bai jin maganata"
Ƙwafa tayi ta ɗauko ƙuli-ƙuli ta zuba a cikin turmi ta fara daka cikin natsuwa, tace "Mama saina zane Yusha'u yau, kinga ƙofar gida ma duk datti" ta faɗa fuskarta sam ba walwala.
Murmushi mahaifiyarta tayi tace "Kunfi kusa"
Haka suka cigaba da sarrafa abunda zasuci cikin natsuwa da tsafta.Azmah hararar Amina tayi tace "Munzo"
Ba tare da Amina tace Uffan ba ta buɗe ƙofa ta fita yayinda ta tunkari wani tamfatsetsen gida wanda ya amsa sunanshi gida, murmushin kawai Azmah tayi yayinda ta jingina da kujerar motar tare da lumshe idanu, tuni Driver ya kunna motarsa ya cigaba da tafiyarsa.
Wata anguwa suka nufa wacca bazaka taɓa cewa a cikin birnin gwari take ba, anguwace ta kece raini wannan yana wane wannan, tabbas tsarin anguwar ya haɗu duk wani ɗan Adam yana da burin ya ganshi cikin wannan anguwar mai cike da tsari, wani gida suka tunkara wanda kaf cikin anguwar ya fisu kyau da girma, gidane na alfarmar gaske, Driver yana danna horn aka wangale taftsatsen get ɗin gidan, girman gidan bazai faɗu ba, ko wajan parking space za'a saka mota a ƙalla wajan goma sha biyar sannan da wani ƙaton fili, yana gama parking ta fito kana kallanta kasan ta gaji dan tsakaninsu da Islamiyarsu akwai ta zara ba laifi, a gajiye ta nufa Part ɗin gidan, sallama ɗauke a bakinta ta shiga Parlourn, ganin mahaifinta yana sakkowa daga Step ɗin bene yasata shagwaɓe fuska tace "Dad badai tafiya zakai ba" ta faɗa tamkar zatai kuka, da murmushi ya ƙaraso inda take tare da Hugging ɗinta yace "My Daughter kenan ko hutawa baki ba amma kin fara yimin tambayoyi haka"
Ƙara mannewa tai a jikinsa tamkar ance za'a ƙwace mata shi tace "Dad shiyasa banason siyasa, kwata-kwata baka kula dani yadda yaka mata fa, ni kaɗaice ƴarka but saika runƙa nunamin halin ko in kula" ta faɗa hawaye na sauka akan kuncinta, tuni hankalinsa yayi matuƙar tashi dan ko kaɗan bayason abunda zai samu ƴa ɗaya tilon ƴarsa, shafa bayanta ya hauyi yana faɗi "Haba My Daughter wa nake nemawa wa kuɗin inba kebe, kiyu haƙuri nai miki alƙawarin bazan daɗe ba, karfa ki manta al'ummar Birnin gwari na buƙatata, kawai zanje fadar shugaban ƙasane ana nemanmu urgently"
Share hawayan fuskarta tayu ta sulale daga jikinsa ta zauna akan 2 seaters ɗin dake cikin Parlour ba tare data ƙara ce masa Uffan ba ta fara ƙoƙarin cire socks ɗin dake ƙafarta.Mahaifiyarta da murmushi ta nufosu yayinda hannunta ruƙe yake da TeaCup tana ɗan jujjuyawa tace "Daddy and his Daughter, in banda abunki Azmah ni ban faɗi haka ba saike me uba, wato ni bana miki amfani a gidannan ko?, fine tunda abun hakane"
Ɗan kallanta tayi tace "Mommy bani da lokacinki sai weekend, a gidannan banda abokan hira daga servant sai wayana, ni ba ƙani ba ni ba wa ba dole zanji ba daɗi a gidannan" kana kallan yadda take maganar zaka tabbatar da abun yana matuƙar ci mata tuwo a ƙwarya, shiru iyayan nata sukai babu wanda ya ƙara cewa uffan, Azmah ganin sunyi shiru yasata ƙwaƙulo fara'a tace "Mom, Dad bari naje ɗaki na canza kaya" ba tare data jira amsarsu ba ta wuce nata Bedroom ɗin.Shiru yayi idanunsa a lumshe hannunsa ruƙe da wani hoto, kana kallan hoton zaka tabbatar da Family ɗayane, jin an shigo yasashi buɗe fararan idanunsa yace "Modibbo bana hanaka shigomin ba sallama ba" ya faɗa muryarsa a sanyaye, cike da girmamawa Modibbo ya bashi haƙuri tare da komawa bakin bukkar yayi sallama ya shigo, miƙa masa hoton yayi yace "Zakaje jahar Kano zakai aiki a ƙalla na wajan wata biyu, dole saika ɓadda kama kafin mucinma burunmu, ina nufin zaka zauna a anguwar da Alhaji Bashir Iyan Tama yake, zakai shigar mahaukata har sai ƴan anguwar sun tabbatar dakai ɗin mai taɓin hankaline, bayan haka zaka zauna a ƙofar gidanshi a ko wani lokaci, idan har matarsa ko ɗansa sukai kuskuren fitowa kai garkuwa dasu"
Shiru yayi dan ga dukkan alamu magana mai tsayi ba ƙarami aiki take bashi ba, yayinda Modibbo ya natsu yana sauraran Ogan nasa, haɗiye Saliva ɗinsa yayi sannan yace "Ka kiyaye sosai aikin nada haɗari sosai, kai kanka kasan waye Alhaji Bashir Iyan Tama"
Cike da girmamawa yace "Da yardar Allah Oga zan kiyaye kuma zanyi aiki cikin nasara"
Gyaɗa kai kawai yayi, sannan yace "Ku shida zaku tafi, inyaso saika runƙa kawo musu duk wani Information daka sani game da gidan, zaka iya tafiya"
Modibbo harya kai bakin ƙofa yaji yace "Gobe insha Allahu zaku tafi, ungo wannan" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe wata locker dake kusa dashi Bundle ɗin ƴan dubu-dubu ya ɗauko masa guda huɗu ya miƙa masa yace "Kuyi maneji dashi, idan ya ƙare zaka iya kirana, but karku manta kar wanda yayi gigin kirana da wayan hannunku, ku samu wata ta musamman da ita zamu runƙa communicating daku"
Cikin girmamawa yace "Angama ranka ya daɗe" karɓa kuɗin yayi da hannu biyu ya fita tare da shaidawa abokanan tafiyar da zasuyi akan gobe zasu wuce Kano zasu bar garin Katsina.*#Votes*
*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*Am back😉
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...