page 25

237 20 6
                                    

Daƙyar ta tashi jin yadda jikinta yayi mata tsami ba ɗan kaɗan ba, miƙewa ta fara ƙoƙarin yi saita kasa saboda yadda ƙafarta ke faman yi rawa, komawa tai ta zauna tare da janyo wayarta, ba wanda ya kirata hakan ba ƙaramin mamaki ya bata ba dan a tunaninta Mommy zataita nemanta, duba lokaci tayi taga har ƙarfe sha biyu da rabi na dare, ɗan zaro idanu tayi, ta samu ta lallaɓa a hankali ta shiga bayi danyin wankan tsarki, tana fitowa kayanta ta saka tare da ɗauko Prayer Mat dan gabatar da sallahr Ishsha'i, saida ta idar sannan tai tsuru tana tunanin a inda zata kwanta dan bazata iya haɗa gado dashi ba, wata irin kunyarss takeji ba ɗan kaɗan ba, a hankali ta tashi saijin sautin muryarsa tayi yana cewa "Idan kin idar kizo mu kwanta, kinsan dai ba hali komawa gida yanzu dan dare yayi" dafe goshinta tayi haɗe da taɓe baki tamkar zatakai kuka, ta taso ta zauna gefen gado.
   Ɗan tashi yayi yana kallanta ganin yadda duk ta wani haɗe fuska tana faman kumbura baki, hakan ba ƙaramin dariya ta bashi ba, dariya yayi, tare da zuge mata Zip ɗin rigarta yace "Ke bakisan ana zafi bane"
  Ɗan ruƙe hannunsa tayi tace "Nidai banji sanyi nakeji"
Dariya yayi, sannan ya zage mata riga tare da janyota jikinsa suka kwanta, Zuhra ganin shiɗin ba Bacci yake da buƙatar yiba yasata cewa  "Dan Allah ka bari banjin daɗi ko kaɗan"
  "Hmmm" yace tare da lumshe ido ya ƙara matseta a jikinsa nan da nan Bacci yayi awon gaba da ita, yayinda shi saida ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin bacci ɓarawo yayi awon gaba dashi.

*Washe Gari*
   Tunda sukai Sallahr Asuba suka koma basu suka tashi ba sai wajan sha biyu na rana, Zuhra ganin yadda gari yayi haske ta zabura tare da mutsutstsuke idanun, daƙyar ta iya tashi ta bufa Bathroom ta wanke fuskarta haɗe dayin Brush ganin sabin Brush a cikin bayin, tsayawa tayi jin har yanzu ƙasanta bai daina mata zafi ba, kamar yadda taga yayi haka itama tayi sannan ta ɗan shiga Tub ɗin dan rage jin raɗaɗin datakeji, saida ta ɗauki mintuna masu tsayi sannan ta fito daga ciki tare da maida kayanta fito, kanta a ƙasa dan ko kaɗan bataso su haɗa idanu dashi.
   Yana zaune kan 2seaters yana murmushi ganin ta fito yasashi tashi yazo inda take yana mata sannu, hannayanta tasa a fuskarta duka biyun ta fashemai da kuka, nan da nan hankalinsa yayi matuƙar tashi, ɗan rungumo da ita jikinsa yayi yace "Please kiyi haƙuri, nasan nai miki laifi amma insha Allahu bazan ƙara ba"
  Ƙoƙarin zame jikinta takeso tayi amma ta kasa, zaunar da ita yayi a ƙasa ba abunda yake ce mata sai sannu, tana rungume a jikinsa ya ɗauko Wammers ɗin daya bada order aka kawo musu, buɗewa yayi ya fara serving ɗinsu cikin natsuwa, ɗan satar kallanta yayi ganin yadda fuskarta duk ta koɗe saboda kuka, yayinda ita kuma ko kaɗan bataso su haɗa idanu dashi saboda tsantsan kunyarsa datakeji, a hankali ya ɗibo Arish cikin Fork yakai saitin bakinta, rufe bakin gam tayi idanunta a rufe.
   Kallanta yayi da Sexy Eyes ɗinsa yace "In baki buɗe baki kinci abincinan ba ba inda zaki, kin dawo nan kenan saidai a tattaromin kayanki a kawo, Oya Eat"
  Marairaice fuska tayi tace "Zanci, ammq dan Allah ka fita tukun ni banson ganinka"
  Ƴar dariya yayi ba tare da yayi mata musu ba ya miƙe ya fita, sannan yace "Idan kin gama ki maza ki shirya kizo mu tafi gida, ɗazu Daddy ya kirani yace muna tarene nace masa ah"
   Taɓe baki tayi zata saki kuka yace "Uhmm kiyi kiga abunda zan miki" maida bakin tayi ta tsuke tare da turosa gaba ta faracin abincin dan ba ƙaramin yunwa takeji ba, dan cikinta wayam tajisu tamkar bata taɓa sakamai abinci q cikin cikinta ba.
   Saida ta kammala tsaf sannan ta fito Parlour, ba tare data kalli inda yake ba tayi hanyar fita waje, murmushi kawai yayi shima ya miƙe tare da ɗaukar Keys ya bita a baya.

   Tunda yayi parking motar ta kasa fitowa daga cikin motar, zagayowa yayi yazo inda take yace "Fito muje man...."
Bata bari ya ƙarasa ba sai ta faramai kuka bil haƙƙinta, cikin muryar kuka tace "Ni bazan iya haɗa ido da Mommy ba wallahi, nasan tana ganina zatasan munyi iskanci"
  Maganar tata sosai ta bashi dariya yace "Iskanci kuma ana zaune lafiya?, maye haɗinmu da iskanci kuma Faɗima, to bari kiji ai da zaran Mommy ta gano abunda ya faru to ina mai tabbatar miki saita sakaki gaba intai miki aiki babu hutu, gwanda ki saki jikinki ki daure kiyi kamar ba'ai komai ba"
   Shiru tayi tana tunanin maganarsa, kallanshi tayi da Oily Eyes ɗinta tace "Ka tabbatar hakane?"
Gyaɗa mata kai yayi fuskarsa ɗauke da yalwataccan murmushi yace "Tabbas, shawarar da zan baki shine ki dake kiyi tafiyarki Normal kamar yadda kike da karta gqne tace gobe zaki tare a gidana"
   Share hawayan fuskarta tayi tana ƙoƙarin fitowa tace "Muje"
Raɗa yayi mata a kunne yace "Sannan inhar taga kina sadda kai ƙasa to zata gane abunda ya faru, kiyi ƙoƙarin kunyi mu'amala da ita kamar yadda kukeyi da"
Gyaɗa kanta tayi tare da ƙara share hawayan fuskarta suka cigaba da tafiyarsu cikin natsuwa, saida akazo saitin Part ɗinsane yayi sauri ya janyota gefe rumfa yayi mata da hannayansa yana ƙare mata kallo yayin kanta na ƙasa ta kasa ɗaga ido su haɗa idanu, cikin daddaɗar muryarsa yace "I Love You" bai jira cewarta ba ya saka bakinsa cikin nata yayi mata wani hot kiss mai tsayawa zuciyar duk wanda akaimawa shi, "Ki kulamin da kanki" shine abunda yace mata ya fara tafiyarsa cikin taƙama da ƙasaita ya nufa Room ɗinsa.
  Zuhra bin bayansa tayi da ido tana ƙare masa kallo yayinda wata irin zazzafar soyayyarsa dake nurƙurƙusa a cikin zuciyarta.
   Cikin sanyin jiki itama ta doshi Part ɗinsu gabanta na faɗuwa gudun haɗuwa da mahaifiyarta, tana tura ƙofar Parlourn taga babu kowa a cikinsa, a hankali ta lallaɓa ta nufa nata Bedroom ɗin, tana shiga tai wata irin ajiyar zuciya, direct bayi ta shiga ta ƙarayin tsarki da ruwan ɗumi dan ba ƙaramin jin daɗinsa takeyi ba dan yana matuƙar rage mata raɗaɗin datakeji.
  Tana fitowa kwanciya tayi kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita.

   Fahad kallan Azmah yayi bayan ya gamajin duk wasu bayananta akan Muhammad Alee da Zuhra, "wai kina nufin Zuhra itace wacca ranar bikinta mukaje muka far musu?" ya faɗa yana tsareta da idanu gabanshi na tsananta faɗuwa.
  Dariyar rainin hankali Azmah tayi tace "Tabbas Zuhra itace wacca kaida mahaifinka dakuma maihaifina kukaje kukaiwa Familynsu cin kashi wanda ba kowa zai ɗauka ba, sannan Zuhra Matar Muhammad Alee ce, domin kuwa tarihi ya tabbatarmin suna matuƙar son junansu"
   Cikin zafin Nama Fhad ya naushi Bango nan take yaji wani irin raɗaɗi, lumshe ido yayi ya buɗesu Tar akan Azmah yace "Kina nufin Zuhra matar aurece?".
  Ƙaramin tsaki taja yadda bazai jita ba tace "Kai menene amfanin Matar aurece ko Budurwa, ina sanar dakai kayi gaggawar karɓar dukiyarka daka rugada ka danƙa mata a bisa rashin sani sannan ka kama kanka tun kafin su fara yi maka taggu"
  Tsaki yaja yace "Banda bukatar dukiya a halin da nake ciki yanzu, kinsan yadda Zuhra take a cikin zuciyata kuwa?, kinsan wani irin matsayi na bata a rayuwata kuwa?, Tunanina, Mafarkina, Burina shine naga na mallaki Zuhra a matsayin Matata tayaya kuma zakizomin da wata irin magana na cewar Zuhra matar wanice ba tawa ba"
  Murmushin gefen baki tayi tace "Shawarar da zan baka itace, idan har kanason ka ɗauki fansa,to ka ɗaura ɗanmara domin ganin mun yaƙesu, tasa Mahaifina na gidan Kaso yayinda naka mahaifin ke kwance a gadon asibiti yana fama da shanyewar ɓarin jiki, shawara ta rage game shiga rijiya"
   Tana gama faɗin haka ta juya tabarshi a gun tamkar mutum mutumi yayinda tashin hankali ya ziyarcesa lokaci ɗaya, ba abunda yafi tayarmai ds hankali sai Zuhra matar wanice, tabbas zai ɗauki mummunan mataki akan Mijin nata, yayinda zuciyarsa harta fara hangoma kanta tsantsan tashin hankalin da zata shiga na rashin Zuhra.

   Leƙawa Mahaifiyar Zuhra tayi ta hangota kwance tana Baccinta hankalinta kwance, ƙwafa tayi ta maida ƙofar ta rufe kalaman Mijin nata na mata yawo a kunne na karta sake ta hantareta ko kuma tai mata faɗa na bin Muhammad Alee datayi, shi a nashi ganin sunyi matuƙar ƙoƙari tare da kawaici hakan yasa suka nemawa kansu hanya mafi sauƙi na barin gidan da sukai dan kasancewarsu da junan, Mommy ba abunda take fargaba sai haɗuwarta da Muhammad dan ba ƙaramin kunyarsa takeji ba, tasan ko ba'a faɗa mata ba Muhammad ya
Rugada da yasan Zuhra a matsayinta na matarsa, ita ta rasa yadda zatai shiyasa ta nemi hanya mafi sauƙi dan ganin sun tare a cikin satinnan dan bazata iya da rashin kunyarsu ba.

   Se bayan Azahar Zuhra ta farka, duba wayarta tayi taga Missed Calls ɗin Muhammad, murmushi kawai tayi tare da tashi tai alwala tai sallah, fitowa Parlour tayi jin yadda cikinta ke bukatar abinci, tana fitowa ta hango Mahaifiyarta zaune hankalinta ya karkata da kallan wani Film mai dogon zango, yayinda ƙaninta yana zaune yana latsa Laptop, ganin Zuhra yasashi tashi daga inda yake yace "Laaa Aunty ashe kin dawo?" ya faɗa murna fal cikin ransa, murmushi Zuhra tayi tace "Ƙanina na kaina kenan, na dawo"
"Ina tsarabata?" yace mata yana faman yin murmushi.
  "Tana ɗakina ka bari idan naci abinci zan ɗauko maka" tana gama faɗan haka hankalinta ya koma ga mahaifiyarta tace "Mommy Yunwa nakeji wallahi" ta faɗa kamar zatai kuka.
   Mahaifiyarta idanunta nakan TV tace "Kije Kitchen ki duba" harta fara tafiya tace "Na Ya Sani fa?"
   Numfasawa mahaifiyarta tayi gani take kamar rashin kunya ma take mata, ba tare data kalleta ba tace "Yusha'u ya kai masa"
  Gyaɗa kanta tayi ta fara tafiya yayinda Mahaifiyarta ta maida hankalinta kacokan akanta, tausayin yarta ne ya kamata gani take har yanzu Zuhra yarinyace ƙarama saidai yadda take tafiya tabbas aikin gama ya gama,ajiyar Zuciya ta sauke tareda faɗin "Allah ya baku zuri'a ta gari, ubangiji ya kareku daga sharrin maƙiya da mahassada"

   Muhammad tunda yaci abinci hankalinsa gabaki ɗaya ya koma kan Zuhra, shi yanzu bayaso ya shiga ciki don ya tabbata bazai iya haɗa idanu da iyayanta ba, saidai tabbas da zasuyi mishi adalci ɗaya shine a bashi Faɗimarsa su kasance tare, ya nuna mata kulawa ta musamman, ƙara juyi yayi akan tamfatsetsen gadonsa kanshi na kallan Slips yana tuna Moment ɗinsu da Zuhra a daran jiya, ya daɗe yana tunani sai kuma aikinyi ua faɗo masa arai, tabbas dole ya tashi ya bazama neman aikinyi domin samun abunda zai ruƙe Zuhra da ita, tuni ya fara tunani me zayyi da uban kuɗaɗan da yake dasu ganin ya fara juyasu sun fara zama kwabo da sisi, da wannan tunanin Muhammad Alee ta wuni.

Fahad kallan wasu Gaggan ƴan daba yayi ya miƙa musu hoton Muhammad Alee yace "Banaso ku ji mishi rauni yayi jinya a rayuwarsa, abu ɗaya nakeso daku shine ku kashemin shi har lahira"
  Karɓa sukai suna ƙare mishi kallo, Ogansu yace  "Zaka bada miliyan Uku, domin Kisa yana da matuƙar tsada a gurunmu"
  Fahad yace......

*#Comments*
*#Subscribes*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now