page 6

331 24 10
                                    

Jikinta a matuƙar sanyaye tai sallama ta shiga ɗakin mahaifiyar tata, da sallama ta shiga sannan ta samu waje ta gaida iyayan nata, bayan sun amsa tai shiru kanta a ƙasa tana sauraronsa, dan a halin datake ciki ko kaɗan bazata iya dogon magana ba, saboda mahaifiyarta ta taɓo mata wani taɓo wanda warkewarshi a gurinta ba ƙaramin babban abu bane, shiru ne ya biyo baya naɗan wani lokaci sannan mahaifinta ya miƙa mata wasu takaddu wanda yayi printing ɗinsu yace "Ansa"
  Hannu biyu ta saka ta amsa tana faman jujjuya takaddun ganin gabaki ɗaya Information ɗin Abdul-Jabbar, Bashir Iyan Tama da kuma na ɗansa Fahad, batasan lokacin da murmushi yayi nasarar ƙwace mata ba, hakan datayi ba ƙaramin mamaki yabawa Iyayanta ba musamman mahaifiyarta datasan halin datake ciki iyanzu.
   Shiru Zuhra tayi yayinfa eyelashes ɗinta jiƙe suke da hawaye suna ƙoƙarin sauka ƙasa, saida ta ɗauki lokaci mai dan tsayi sannan ta dubi mahaifinta tace "Daddy!, nai maka alƙawarin komai naku zai dawo da yardar Allah, saidai inaso ku ɗauki yadda da aminci ku bani, inaso dole sai nayi nesa daku zan ɗauki wannan matakin, sede inaso kusa a ranku duk inda nake ina tare da addu'arku tare da kariyar Allah..."
   Mahaifiyarta saurin katseta tayi da cewar "Ina zaki?, me kike nufi?, kina nufin zaki tafi ki barmu ki tafi ke kaɗai wajan cimma burunmu?"
   Murmushi tayi tace "Hakan nake nufi Mommy, inhar ina tare daku to tabbas sai an gano gaskiyar abunda muke ƙokarin aikatawa saboda Daddy, sun sanshi farin sani, kuma yanzu Alhaji Abdul-Jabbar yana ƙoƙarin so yaga sun gana da Daddy kina tunanin duk randa yaga Daddy zai barmu mu shaƙi numfashi na ranar?, na zauna nayi nazari Mommy dole idan zan ɗauki fansa akan Abdul-Jabbar sai nayi nesa daku, yana can yana fafutukar yadda zai samamin makarantar jami'a, ta hakane zan samu damar zama a Hostel ba saina runƙa zuwa wajanku ba har sai na cimma burina"
    Numfasawa tayi tare da kallan mahaifinta tace "Daddy!, inaso kaimin wannan alfarmar, insha Allahu zan tsare mutuncin kaina bazan abunda zakuyi Allah wadai dashi ba, kuma kaga mu bamuyi rayuwar wannan ƙasar ba bare yasan cewar niɗin ƴarka ce, bazai taɓa tsammanin muna Nigeria ba bare yayi tunanin munzo ɗaukar fansa"
   Shiru dukkaninsu mahaifan nata sukai suna nazari, sun ɗauki a ƙalla minti biyar babu wanda yace uffan, numfasawa mahaifinta yayi yace "Wata biyu kawai ya rage mana a nan garin sannan mu nufa Kano kina tunanin zaki nasara akan Abdul-Jabbar a wa ƴannan ƴan watannin?, kinsan hatsarin dake da Abdul-Jabbar kuwa?, mutum ne mai matuƙar hatsarin gaske"
   Jim Zuhra tayi tace "Insha Allahu zan samu nasara akanshi, fatana dai ku runƙamin kyakykyawar addu'arku kamar yadda kuka sabamin ita a duk inda nake"
   Dukkaninsu sukace "Allah ya baki sa'a, amma kiyi taka tsantsan sosai"
  Murmushin jin daɗi tayi ganin iyayan nata sun aminta da ƙudurinta.

*Washe gari*
Gabaki ɗaya su Zuhra suna ɗaki daya sunayin Break fast, Jin sallamar Azmah yasasu gabaki ɗaya fitowa sukabar mahaifin Zuhra gudun kaf Azmah ta ganshi, da murmushi Azmah ta ƙaraso harabar gidan ta tsugunna ta gaida mahaifiyar Zuhra, amsawa tayi kadaran kadahan ba kamar daba datake sakin mata fuska, Zuhra kallan Mahaifiyar tata tayi amma taga ko inda take bata kalla ba, Azmah bata lura da haka ba hakan yasata miƙewa ta janyo hannun Zuhra suka shiga ɗakinta, Zuhra bin ta tayi da ido har suka isa ɗakin, murna fal cikin Azmah tai sauri ta ɗauko Hand Bag ɗinta ta ciro Admission ta miƙawa Zuhra tana maijin daɗi, Zuhra karɓa tayi ganin da gaske fa Mahaifin Azmah yake yasata zaro manyan idanunta ta ƙwalla uban ƙara kamar da gaske ta fita a guje taje ta nunawq Mahaifiyarta, rungumeta tayi tace "please Mom ki saki ranki kar Azmah ta fara tunanin wani abu, ki nuna tsantsan murnarki a matsayinki na mara ƙarfi wacca take buƙatar taimako hakan zaisa na samu nasara wajan aikina" tana gama raɗa mata ta janye jikinta tana faman juyi da murna a gidan tafkar har cikin ranta take hakan.

   Mahaifiyarta itama murmushi tai yayinda take danne zuciyarta game da tsanar dataji tanawa Azmah ta matso kusa da Azmah tai mata godiya ba ɗan kaɗan ba.
  
    Azmah murmushi kawai tayi tace "Haba Mama dani da Zuhra ai duk ɗayane babu wani godiya tsakanina daku"
   Yaƙe Mahaifiyar Zuhra tayi tare da faɗin "Hmmm" ta samu kujera ta zauna tana jiran Azmah ta tafi.
    Azmah kallan Mahaifiyar Zuhra tayi tace "Mama Allah yasa yau na taka sa'a dan gun Baba nazo muna tare da Daddyna"
   Murmushin ƙarfin hali tayi tace "Aiko bakici sa'a ba, dan mahaifinsu yau san mako yayi uban gidansa ya aikesa can Lagos suyo kayayyakin gyara"
  Ɗan ɓafa fuska Azmah tayi tace "Gaskiya naga alama kwana biyu bana takan sa'a, shikenan, Mama idan ya dawo ki sanar dashi Daddyna ya gama kammalawa Zuhra komai na makaranta, har Hostel ya kama mata yace zirga-zirgan bashi da amfani"
  Murmushi kawai mahaifiyar Zuhra tayi tace "Allah ya saka da alkhairi, insha Allahu zan sanar masa idan ya dawo.."
   Azmah katseta tayi da cewar "bashi da waya a hannunsa ne?"
  Dariyar manya tayi tace "Haba Azmah muna fama da ciki wata waya kuma zai ruƙe, amma insha Allahu ya kusan siyan wayar saboda lalurar yau da kullum"
  Gyaɗa kanta tayi tare da ƙara zage Hand Bag ɗinta, Techno ta ciro ƙirar Android mai kyan gaske ta miƙawa Zuhar tace "Student, ga waya nasan dole zaki buƙaceta kodan Assignment"
  Karɓar wayar Zuhra tayi murmushi shinfiɗe a fuskarta tana jujjuya wayar, kallan Azmah tayi tace "Bansan d wani irin baki zan miki godiya ba, saidai nace Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya ɗauraki kan maƙiyanki"
   Murmushin jin daɗi tayi tace "Ameen, zaki ga numberna nai miki saving, insha Allahu zuwa anjima zan kiraki kema na saka miki katin"
  Jinjina kai tayi tana maijin ƙaunar Azmah a cikin rayuwarta, Azmah sallama tai musu ta tafi.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now