page 2

344 24 2
                                    

*MUHAMMAD ALEE*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
 

    
                             *02*

Washe gari da sassafe su Modibbo suka kama hanyar zuwa Kano, yayinda duk wani shiri da zasuyi sunyi shi tun kafin su isa Kanon, lafiyayyan gida suka kama wanda yake bayan gari irin anguwannin nan da babu ruwan wani da wani, Direct gidan suka nufa suka huta gajiya sannan Modibbo ya fara shirin aikin da aka kawosa, cikin lokaci ƙanƙani saiga Modibbo ya ɓadda kamarsa tamkar bashi ba, ga wani dressing da akai masa na mussaman haɗe da Makeup wacca duk wanda yaga fuskarsa zayyi tunanin Mahaukacine wanda ya ɗauki shekaru masu ɗunbin yawa yana ciwon hauka, haƙoransa wani abu da aka shafa musu bazaka ƙara ganinsu ba dan ƙyama, shi kanshi daya kalli kanshi a madubi saida ya sarawa Joseph ganin irin namijin ƙoƙarin da yayi wajan canza masa kamannin kamar bashi ba, nan take ya fito ya fara tafiya har anguwar Alhaji Bashi Iyan Tama duk da akwai tazara ba ƴar ƙarama ba, mutane da dama suka ganshi sukan gudu,ba tare daya damu ba ya cigaba da tafiyarsa har ya isa anguwar da Alhaji Bashir Iyan Tama yake, kaf faɗin Kano zan iya cewa banga anguwa mai kyau da tsari irin anguwar ba ko gidan Gwamnati sai haka, saida ya kalli hoton hannunsa tsaf sannan ya kalli gidajan anguwannin ya hango wani gida iri ɗaya sak da hoton dake hannunsa, hakan na nufin nan ne gidan Alhaji Bashir, ba tare da ɓata lokaci ba ya doshi gida wani gu ya samu can gefen gidan ya zauna yana tsince-tsince, idan ka ganshi saika rantse mahaukacin gaskene, saidai duk abunda ke faruwa a anguwar a kan idonsa, duk da anguwar manya-manyan mutanan masu kuɗi ne hakan baisa Modibbo yin dabarar shiga anguwar ba duk da masu gadin da suka kewaye anguwar, ganin yanayin yadda Modibbo yake saika rantse baisan abunda ke faruwa ba amma kar yake.

*GIDAN ALHAJI BASHIR IYAN TAMA*
   Abun mamaki duk girman gidan duk kyanshi bayan Get Man ba kowa a harabar gidan, wannan babban Part na hango mai kyan gaske, wani matashi ne ya fito daga wajan bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba, hannunsa ruƙe da kwalbar Wine da rana tsaka babu tsoron Allah a tattare dashi yayinda kaf ma'aikatan gidan suka ɓoye saboda rashin mutuncinsa da tijara, mata ma'aikata kuwa tuni sun samu gun da zasu fake saboda kar suyi gigin fitowa su haɗu da *Fahad Iyan Tama* ɗa namiji ƙwaya ɗaya da Allah ya mallakawa Alhaji Bashir saidai wannan ɗa bai samu tarbiya ba ko kaɗan, rayuwarsa gabaki ɗaya Abroad yayita yaro ne sangartaccan gaske wanda aka ruga aka sangartashi da dukiya, bai shakkar shigo da mace har cikin gidan yayi Sex da ita koda kuwa mahaifiyarsa na tsaye ƙofar ɗakinsa, hakan bazai sa ya daina abunda yakeyi da mace ba, yayinda ko ƙanninsa idan har sha'awa ta ciyowa baiƙi yace zai kwanta dasu ba, danma mahaifiyarsa a tsaye take kawai ya rugada yafi ƙarfinta ne saboda Alhaji Bashir, shi a ƙazamar rayuwarsa yadda kasan bunsuru haka yake, inhar ƴar aiki tai masa tas zai iya bata umarni akan tazo part ɗinsa dan yayi lalata da ita, ta dalilin hakane Fahad yasa mata marasa gata *Gararin rayuwa* a rayuwarsu, wasu su faɗa karuwanci wata saboda baƙin ciki saboda ita ɗin ba kowa bace ciwon zuciya ya kamata, ciki na Fahad a garin Kano yayishi babu a dadi ga ƴaƴan mutane kuma babu wanda ya taɓa ɗaukar ƙwaƙwƙwaran mataki.

   Security's guda biyune suke biye dashi wani ya buɗe mishi mota ya shiga ɗaya ya zauna a matsayin Driver yayinda ɗaya ya zauna a Seat ɗin mai zaman banza, cikin gaggawa Get Man ya buɗe gidan, motar ta fita a guje kamar yadda ya umarcesu.

Modibbo ganin an buɗe gidan Alhaji Bashir yasashi saurin tsayawa a tsakin Titi yana tsince-tsince tamkar mahaukacin gaske, Driver da sauri ya wani ja wawan burki dan ko kaɗan bai kuka d Modibbo ba saida ya kusan zuwa inda suke, Fahad wani tsaki yaja tare da faɗin "Wannan wani irin iskancine wawaye jakuna" ya faɗa yana huro musu hanci, duk da suna ƙasanshi zagin da yake musu ba ƙaramin damunsu yake ba, amma babu yadda zasuyi, Driver ɗinne cikin kwantar da murya yace "Kayi haƙuri ranka ya daɗe saura kaɗan na kaɗe wancan mahaukacin" ya faɗa yana nuna Modibbo wanda yake tsaye a tsakiyan Titi hankalinshi kwance yana tsince-tsince, cike da zafin nama Fahad ya fito daga motar yana famab hura hanci, yana zuaa inda Modibbo yake ya juyo dashi ya sharara mai mari, ya ƙara marinsa a ɗayan kuncin, tsirtar da yawu yayi yace "Wawa mahaukaci kai bakasan kana tsakiyan Titi bane zaka kama ka tarewa mutane hanya, dalla matsa kaba mutane wuri kafin in bige banza da hofi" jan Modibbon yayi gefen Titi tare da tsiyaya masa ragowar Wine ɗinsa yayi cilli da kwalbar nan gefen Titi, komawa yayi cikin mota ya shiga nan suka jashi suka tafi abunsu.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now