Rashin Comments ɗinku da Votes shike saka jikina yin sanyi na kasa typing sainai tunanin kamar baya muku daɗine, comments dinku da Votes shike sakani yin posting akai akai koda banyi niyya ba
Zuhra ganin abu ya zuba a ƙasa yana kumfa yasata ɗaga kanta daga ko menene, Azmah ke faman kokawa da hannunta jin an ruƙe mata hannu a bayanta an hanata aiwatar da abunda zatai, a ɗan tsorace Zuhra ta matsa tana ƙarewa Fahad kallo ganin ya ruƙe hannun Azmah gam tana ƙoƙarin watsawa Zuhra Acid ɗin, yayinda har wani saida ya zuba a hannunta amma saboda tanason cika burinta ko kaɗan bataji radaɗin da hannunta yake ba kuma bata lura lokacin da fatar hannunya ta fara saluɓewa ba kasancewar Fahad dantse hannunta ya ruƙe gam, a haka dai suka tsiyayar da Acid ɗin a ƙasa yayin sai faman huci take tana so taga wani mashahurinne ya ruguza mata mafarkinta, waigowa tai suka yaɗa idanu da Fahad ba tare data ɓata lokaci ba ta wanke fuskarsa da mari tana faman yin huci, tare da nunasa da yatsa tace "Ka fita sabgata, ka fita a rayuwata inba hakaba zan maka abunda baka taɓa tsammani zan iya aikata mashi ba a rayuwarka"
Kallan Zuhra tayi ta saki wani irin malalacin murmushi tace "Kin tsallake tarkona na farko amma ki sani bazan taɓa bari ki tsallake na biyun ba, Zuhra na tsaneki a rayuwata bazan taɓa sonki ba har abada wallahi, kuma nai alƙawarin shayar dake baƙin ciki duniya wallahi,bazan taɓa sonki ba, kin auremin wanda duk duniya bani da kamarshi, bani da wanda zuciyata ta kwanta dashi sama dashi, kin lalatamin rayuwata, kin maidani marainiya Alhalin mahaifina yana raye a doron ƙasa, ina mai tabbatar miki sai kinyi babbar dana sani a rayuwarki"
Jikin Zuhra ba abunda yakeyi sai rawa tare da matuƙar tsoron Azmah da halayyarta, dama cutar da ita tazoyi har gida, kallan gefen hannunta tayi wanda Acid ɗin ya wuce ta wajan ya zuba a ƙasa ganin harya fatar wajan ta ɗaye yana mata raɗaɗa mai matuƙar azaba, ƙara ɗaga kanta tayi ta kalli hannun Azmah ɗin ganin gabaki ɗaya ta wankeshi da Acid hannun ya canza halitta lokaci guda yasata jinjinawq Azmah saboda bala'inta ma batajin zafin da hannunta yakeyi.
Kasa magana tayi ta juya ta fara ƙoƙarin komawa ɗaki tana faman sauke ajiyar zuciya akai-akai, tana mamakin hali irin na Azmah so tai ta hallakata kenan, tafiya take tana share hawayan dake zubo mata akai-akai, ganin Muhammad a tsaye ya harɗe hannayansa idanunsa akanta yasata saurin share hawayan fuskarta haɗe da ɓoye hannunta tana ƙirƙiro murmushi, "Ka fito?"
Ta faɗa tana ƙoƙarin danne damuwar datake fama da ita, "Hayaniyar me naji a waje?"
"Ba komi' ta faɗa tana sosa kai, ya ɗauki lokaci yana kallanta, ya tako gabda inda take, hannunta ya ruƙo yace "Muje naga meke faruwa"
Raurau tai da ido tace "Please Yaya ka barta da halinta karkai mata komi"
Kallanta ya ƙarayi da fitinannun idanunsa tare da sa hannunsa ya ruƙo dayan hannun datake ɓoye masa yace "Me tai miki?"
"Ba komi" shine amsar data bashi ganin gefen hannunta tamkar wacca ta ƙone yasa idanunsa sauya kala, yayinda suka doso wajan Get ɗin yaga tanawa Fahad zagin Tijara dacin mutunci, tabbas Fahad ya tuba da adaa ne bata isa ta nunasa da yatsa ba ba tare daya ɓalla hannun ba, ganin Muhammad yasa ya raɓa gefen Azmah yana ƙoƙarin shiga ciki duk da yaga babu fuska a tattare da fuskar Muhammad ɗin ganin irin kallon dayake jefanshi dashi.Cike da fuskar damuwa yace "Mai yasa kukai saurin yadda da Azmah,da tuni ta kassara Zuhra ta zuba mata Acid a fuska ba"
A ɗan tsorace ya ɗago dakanshi yana kallan Zuhra, Azmah da Fahad lokaci guda zuciyarsa na neman tarwatsewa saboda irin bugun datakeyi da ƙarfin gaske.
Yayinda Azmah ta kafe Muhammad da idanu tamkar tsohuwar mayya tanaji tamkar ta haɗiyesa saboda tsananin ƙaunar datake masa a tattarame da ita, "Acid?" ya faɗa yana kallan hannun da Zuhra take ɓoyewa, a hankali ya saka lallausan hannunsa ya kama hannunta yana so yaga me take ɓoye masa, ganin gefen hannunta ya saluɓe yasa yayiwa Azmah mugun kallo wanda har saida ƴan hanjinta suka kaɗa, sakin hannunta yayi yayinda ya doshi Get ɗin ya rufe ya saka ɗan makulli, yaja Zuhra yakaita ɗakin, wayarsa ya ciro ya tura Message gudun kar Zuhra tasan me zai aiwatar, Box Aid ya ɗauko yayu treatment ɗin hannunta sannan ya jata har Bedroom ya kwantar da ita yana mata murmushinsa mai mugun tsadar gaske, shafaa kanta yahau tamkar wata jinjira wainan yanaso tai bacci, tashi tai fuskarta cike da damuwa tace "Yaya please ka buɗe musu Get suyi tafiyarsu, kuma dan Allah kar kaiwa Fahad komi ga dukkan alamu akwai abunda ya kawoshi mai matuƙar muhimmanci yasa yaci karo da aika-aikan da Azmah take ƙoƙarin aikatawa akaina"
Shiru Muhammad yayi baice mata Uffan ba, dan yau yaci alwashin daga Azmah har Fahad yau sai sun yabawa aya zaƙinta, dan bazai taɓa ɗaga musu ƙafa ba, yana zargin tare suke shine yakeso yay masa pretending.
Zuhra raurau tai da idanunta ganin yaƙi ce mata komi, kwantar da kanta tai kan ƙirjinta tace "Please Yaya dan Allah ka rabu da Azmah komi tai kanta tai mawa"
Jin yadda ƙirjinta ke bugawa yasashi faɗin "Please ki kwanta ko kya samu natsuwa, dole na takawa Azmah burki abunda takeyi is too much, yanzu da Allah ya bata sa'a ta watsa miki a fuskanki ba, wa aka cuta, ni burina kawai ta fita daga rayuwarmu ko a hanya ta ganmu karta nuna ta sanmu"
"Fahad fa?"
Zuhra ta faɗa ta kafeshi da idanunta tamkar da maidashi ciki haka takeji tabbas soyayyar Muhammad a jinin jikinta take.
Kishi ne ya turnuƙesa ba tare dayace uffan ba ya fara ƙoƙarin tashi dan bazai iya jurar yadda yaga ta damu akan Fahad ɗinba akan kar yay mai komi, ruƙo hannunsa tai tace "Kayi haƙuri inna ɓata maka rai, kawai banaso muyi rashin adalcine"
"Uhmm" kawai yace, tare da tsugunnowa saitinta yay mata Light kiss, wayarsa cs ta fara ruri ɗagawa yay yace "Am Coming" yay sauri ya fita tare da kulle Zuhra ɗin akan karta fito.
Fitowa yayi yana takunsa na ƙasaita ko kallan inda suke bayyi ba ya nufa tafkeken Get ɗin gidan ya buɗe, motar Police ce ta shigo harabar gidan sukazo inda yake, nan ya faɗa musu iya abunda ya sani tare da tabbatar sun ruƙe Azmah har sai Kotu ta shiga tsakaninsu.
Nan suka tabbatar masa da angama nan wata mace tazo ta jata suka shigar da ita motar da ƙarfin tsiya ba tare da sun ɗaga mata ƙafa ba, yayinda Azmah sam ta manta da cewar akwai ciki a tattare da jikinta ma.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...