"Muje gida ko?" Zuhra dake manne a jikin Muhammad tamkar zata shige jikinsa ta faɗamai haka, domin tagaji da kallon da wannan budurwar take aika masa, ya buɗe baki zai mata magana tai saurin tashi tana gyagygyara Hand Bag ɗinta ta kalli mahaifiyar Fahad murmushi kan fuskarta tace "Mom bari mu ɗan keƙa gida zuwa anjima insha Allahu zamu dawo"
Da fara'arta mahaifiyar Fahad tace "Ba komi ƴannan sannunku da ƙoƙari, ba abunda zance muku saidai nace Allah ya saka da alkhairi"
Yaƙe tayi yayinda ta makama wannan budurwar harara ganin har yanzu taƙi daina kallon Muhammad tace "To mun tafi"
Fita sukai daga ɗakin suka fara tafiya cikin so da ƙaunar juna, Zuhra tuno baki gaba tayi tace "Ni naga alama kallan da waccar ƙatuwar take maka yana matuƙar sakaka nishaɗi, nace ka taso mu tafi amma kamar bakason barin ɗakin" ta faɗa tana ƙoƙarin ɓare mai baki a bainar Nasi.
Murmushi yayi tare da jan kumatunta ya doshi inda motarsa take."Ke har yanzu babu wanda zaki kira mana a danginki, mufa mun gaji da baki abinci kina lamushewa, kamata yayi wani naki ya sani don a runƙa kawo miki naki abincin"
Goge ƙwallar idonta tayi tace "Aramin wayarka"
"Wa zaki kira?" ya tambayeta tana daga cikin Cell.
Shiru tayi ba ansa tana nazari, "Kinga, nifa bazan runƙa wahalad da katin wayana a banza ba kina kiran ƙatti daga ƙarshe ma suƙi biyan buƙata"
Cikin sanyin murya tace "Mahaifiyata zan kira"
Cike da mamaki yace "Dama kinada uwa kika tsyaa tsilka-tsilla, ga dukkan alamu baki shuka abun azziki ba" zaro wayarsa yayi daga aljihu tare da kirann Sargent ya miƙa mata waya yana mai mata gargaɗi karta cinyemai katin waya.2 missed calls tai mata bata ɗauka ba ana ukunne aka ɗauka, saida Azmah ta saki wata irin nannauyiyar ajiyar zuciya, muryarta na cracking tace "Mom..." kasa ƙarasa abunda zata faɗa tayi ta fashe da wani irin kuka mai tada hankalin mai sauraro musamman uwa da ƴarta.
Cikin tashin hankali mahaifiyarta tace "Azmah lafiya kike?, maiya faru kike kuka?, keda waye haka?" gabaki ɗaya a ruɗe take shiyasa ta jera mata wa ƴannan tambayoyin hankalinta a matuƙar tashe."Mom ki yafemin dan Allah, kiji ƙaina kice kin yafemin, ina cikin musiba, ina cikin tashin hankali"
"Look Azmah ki faɗamin abunda ke damunki, gabaki ɗaya kin saka hankalina tashi, maiya sameki, ki natsu kimin bayani" cewar Mahaifiyarta.
Cikin muryar kuka tace "Mom ina Cell an kulleni, kuma Case ɗin ba ƙaramin Case bane gashi naji suna maganar zasu tura maganar Kotu"
Mahaifiyarta sauri tai ta dafe bangon dake kusa da ita tana ambaton sunayan Allah, cikin ƙarfin hali tace "Wani Station aka kaiki?"
Azmah cikin sanyin murya tana maijin kunya mahaifiyarta tazo ta taddata a Cell sannan ɗauke da ciki a jikinta, "Mom na wajan Fly Over ne"
Share hawayanta tayi tace "Okay bari na kira Uncle ɗinku mu taho tare dashi, ki kwantar da hankalinki"
Gyaɗa kanta tayi hawaye na zuba daga cikin idanunta, batare datai aune ba taji an fizge wayar, cike dajin haushinta yace "Wallahi saikin sakamin katina bari mahaifiyar takin tazo, baza'a ƙararmin da Katin waya a banza da hofi ba, kina ganin yanzu na aika aka siyomin na 200 amma inaji suna faɗin One Minute Remain"
Muryarta a dakushe tace "Nagode, insha Allahu zan saka maka katinka"
Taɓe baki yayi yace "Jibeki kamar ta Allah" bai jira cewarta ba yay gaba abinsa yana ta faman yin mita.Yau satin Fahad ɗaya a Hospital cur yaji sauƙi tamkar bashi ba har wani irin kuzari ya ƙara, yay kyau abunshi, kuma yau akai discharging ɗinsa, ga wani irin shaƙuwa daya shiga tsakaninsa da Muhammad Ali a kwanakin, yayinda Zuhra ta cigaba da rainon cikinta, lokacin da suke harhaɗa kayansu a Hospital ɗin Zuhra ta matso Gabda Muhammad murya ƙasa-ƙasa tace "Thank you my sweetheart"
Kumatunta yaja yace "For What?"
"Uhm" kawai tace ganin yadda kallo ya dawo kansu, Fahad da Muhammad gaba sukai har wajan motar mahaifiyar Fahad yayinda Zuhra da mahaifiyarsa suka tattara abubuwan buƙata tare da yima sauran majinyatan sallama, gabaki ɗaya kayan a Boot ɗin mahaifiyar Fahad suka saka, nan mahaifiyarsa taita musu godiya haka zalika Fahad yay musu godiya ƙwarai da gaske, nan kowa ya shiga motarsa suna maijin tsananin kewar juna.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...