Bayan Driver ya sauke a Kano Line ta ɗauki wayarta ta kira mahaifiyarta ta shaida mata ta shigo cikin Kano, nan tace ta tsaya a inda take gasunan zuwa, samun guri tayi ta zauna tare da kafe wani gurin da idanunta tana jin zuciyarta babu daɗi ko kaɗan, tunowa datayi wayar data saka Sim ɗin Abdul-Jabbar ta barta acan saita tsinta kanta cikin damuwa, dan akwai abubuwa masu matuƙar muhimmanci a cikin wayar wanda ta adanasu, rausayar da kanta tayi jin cikinta ya fara kuka alamun tanajin yunwa.
Ganin wata Mota tayi Parking gabanta yasata kauda kanta, zuge Glass ɗin motar da akaine ta hango Iyayanta a ciki, fuskarta ɗauke da ɗunbin mamaki da kuma tamabaya fal cikin ranta, haka ta taso tamkar wacca zata faɗi ta isa inda suke, da murmushi tabisu tare da buɗd motar ta shiga tayi wani Balanced a kujerar kana kallanta basai an tabbatar maka a gajiye take ba.Abdul-Jabbar na hango abun duniya yayi mishi yawa, duk wasu kaddarorinsa wanda yakeji dasu kuma yake taƙama dasu, matasa sunje sun ƙona masashi tare da barazanar shima tabbas duk randa sukai Ido biyu dashi saisun hallakasa, gashi yanzu Gwamnati ta sallameshi akan muƙamin da yake ciki tare da alƙawarin ƙwatarwa wacca yayi yunƙurin lalata da ita ƴanci, EFCC suna nemansa dan sun tabbatar da cewar yayi sata lokacin da yake kujerarsa ta Minister Of Petroleum, suma haka suka makashi Kotu tare alwashi duk kuɗin daya tattara ya ɓoye saiya fito dasu.
Zama yayi a makeken Parlornsa yayi zugum yana tunani, abun duniya ya isheshi, tabbas yanzu ya shiga hannun Hukumar EFCC ba abunda zai tsira dashi najin daɗin rayuwa, yayi alwashin wulaƙanta Zuhra duk randa sukai ido biyu da ita tare da ɗunbin danasanin abunda ta aikata mishi, yana ɗaki ya kasa fita konan da can gashi Mahaifiyar Azmah ta buɗe mai wuta akan lallai saiya bata takaddar saki ko kuma ta makashi kotu.A gajiye Azmah ta ƙarasa Kaduna ta samu motar da zata sadata da Birnin Gwari, ta gaji matuƙa kamar wacca tayi shaye-shaye haka take tafiya, daƙyar Allah ya kaita inda zata, a matuƙar gajiye ta fara Knocking ɗin Get ɗin gidan nasu, Get Man ne yazo ya buɗe ganinta yasa ya wurga a guje ya shiga cikin gidan dan yaje ya bada labari, Azmah ganin ya shiga ciki yasata rufe ƙofar ta kutsa itama cikin gidan, tana shiga Babban Parlournsu ta hango mahaifiyarta zaune ta rafka Uban tagumi, kai kana kallanta basai an tabbatar maka da cewar tana cikin damuwa ba, jan ƙafa kawai Azmah tayi ta isa inda mahaifiyarta take ta kwanta a jikinta, tana kwanciya akan cinyarta ta fashe da wani irin matsinnancin kuka, a ɗan firgice mahaifiyarta ta kalli cinyarta ganin Azmah yasata sauke wata irin ajiyar zuciya tare da Hugging ɗinta itamata saka kukan ko Allah zaisa ta rage jin raɗaɗin datakeji a cikin zuciyarta.
Alhaji Abdul-Jabbar da Get Man ɗinsa ne suka shigo Parlourn suna faman maida numfashi tamkar wanda sukai gudun tsare, ganin Azmah jikin mahaifiyarta yasa jikinsa yin sanyi amma still zuciyarsa ba karaya ba, ƙarasawa yayi inda suke yanas ya taɓa ƴarsa ko zai rage jin raɗaɗin da yakeji na wannan duniyar datayi masa rana, jin Motsi a bayansu yasa Mahaifiyar Azmah tsayawa cak da kukan datake, ganin Abdul-Jabbar yasata tashi a fusace tace "Fitarmin daga ɗaki"
Tsayawa yayi bashi da niyyar fita yana ƙarewa Azmah kallo ganin yadda tayi baƙi ta rame, muryarsa na rawa yace "Dan Allah ki bari inga ƴata..."
Kallan da Azmah tabishi dashi ne yasa gabanshi mummunan faɗuwa tare da tsananin mamakinta na yadda ta jefeshi da irin wannan kallan a matsayinsa na mahaifinta, sannan ya hango tsantsan tsanarsa a cikin zuciyarta, tashi tayi fuuu tabar wajan ta shiga nata Bedroom ɗin, tana shiga ta faɗa kan Bed ɗinta ta fara rera kuka, gashi tana da buƙatar tayi wanka amma tashin hankali datake ciki tare da azabtacicciyar soyayyar Muhammad Alee ne yasata kasa taɓuka komai, idan ta tuno cewar Muhammad Alee bashi da kowa baida komai face Zuhra tana shiga tashin hankali me tsananin gaske, haka ta kwanta tana jin zuciyarta na mata zafin gaske, jin jikinta yana mata tsami ga wani tashi-tashi dataji tanayi saboda ranar da akwa kwaɗa yau yasata tashi ta shiga Bathroom dan watsawa kanta.Zuhra kallan Iyayan nata tayi tana kallan gidanda suke ciki, gidane na gani na faɗa kuma na kece raini, ga dukkan alamu bayau bane karo na farko da suka sabayin rayuwa a cikin sa, bayan tayi wankane tazo ta zauna akan Dinning danyin Dinner, kallan Parlourn kawai takeyi tana faman jujjuya Spoon ɗin dake hannunta.
Mahaifiyarta ce ta kalli yanayin datake ciki tace "Zuhra!"
Kallanta tayi da idanu tace "Kici abincinki mana, nasan kinajin yunwa"
Zuhra rausayr da kanta tayi tace "Mommy...."
Sauri tayi ta dakatar da ita tace "Kici abincinki, nan gidan mahaifinki ne wanda yake dashi a Kano, sauran bayanin kici abinci ki huta zuwa gobe zan miki cikakken bayani"
Kallan mahaifin nata tayi taga ya bita da murmushi, murmushin itama ta maida mishi, sannan ta tsakura abincin ta miƙe, kallan iyayan nata tayi da ƙaninta tace "Good night" barin gun tayi zuciyarta na faman azalzalarta na ta sanar da Iyayanta gaskiyar lamarin data snai game da Yayanta Sani, haka ta danne zuciyarta taje ta kwanta tanaso ta tabbatar da maganar Azmah.*Washe Gari*
Azmah ganin haske ya fara haske idanuntand yasata tashi tana faman mutsitstsike idanu, mahaifiyarta ce ta shigo tace "Kizo kinyi baƙi"
Yamutsa fuska tayi tace "Mom yanzu da sassafennan su waye sukazo nemana"
Ɗage kafaɗa tayi tace "Nima bansani But yaron yace Muhammad Alee ne kira...."
Bata bari ta ƙarasa faɗa ba tai saurin mirginowa daga kan Bed ɗin da take, ta shiga Bathroom ta wanke fuskarta, goge fuskar tayi ko mai bata shafa ba ta ɗauko Veil ta saka a kanta tana neman barin ɗakin.
Mahaifiyarta da mamaki take kallanta, harta sa ƙafa zafa fita tace "Azmah!"
Tsayawa Azmah tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "Na'am Mommy, nasan kina da tarin tambayoyi a kaina, ki bari idan na dawo zamuyi magana dake" da murmushu tabar ɗakin, tunda ta fara tafiya gabanta ke faɗuwa, tana tunanin meya kawoshi wurinta har a wannan lokacin sannan tayaya yasan gidansu, koda yake batai mamakin sanin gidansu da yayi ba.Tura Get ɗin gidan tayi ta hango wata tsaleliyar mota, ko ba'q faɗa mata ba tasan shine a ciki, a hankali ta fara tafiya tamkar wacca ƙwai ya fashewa a jiki har ta isa motar, Knocking ta fara taga an zuge Glass ɗin kusa da ita, batasan lokacin datai tuntuɓe ba ganin fuskarsa ta bayyana, tabbas sai yanzu tagane cewar Muhammad Alee namiji ne na ƙarshe samun irin a cikin maza sai mutum yaci matuƙar wahala tamkar allura ne a cikin teku haka take masa kallan.
Ganin irin kallan banzan daya jefeta dashine yasa ta daidaita natsuwarta, shiru tayi kanta a ƙasa ta kasa haɗa idanu dashi dan tabbas ta kuskura idonta yaƙara yin tozali dashi to zuciyarta zataviya tarwatsewa lokaci guda.
Muhammad Alee ba abunda yae fargaba sai karya tambayeta ina take tace batasan inda take ba, duk da zuciyarsa na bashi ƙwarim gwiwa akan tunda ya samu Azmah to tabbas yaga Zuhransa.
Ɗan gyaran murya yayi yace "Ya kk?"
Muryarta na rawa tace "Lafiya ƙalau"
Ganin yadda ta hargitse yasashi sassauta muryarsa yace "Ina ƙawarki Faɗima?"
Ɗan kallanshi tayi a tsorace tace "Bakwa tare?" ta faɗa cikin tashin hankali.
Shima cikin tashin hankali ya maida mata da tambaya yace "Kamar yaya?"
Wani irin gumi ne ya fara tsatstsafo mata ta rasa ta ina zata fara yimai bayani, ganin yadds ya kafeta da idanune yasata ƙara tsorata yace "Magana nake miki"
Cikin dakiya Azmah tace "Bayan mun soma tafiya ta fara bani kaɗan daga cikin tarihinta shine na tabbatar da cewar kaine Ya Sanin data ke faɗamin ka Rasu shine nace mata ai kaine wanda kai garkuwa dani, muna mota tasa aka sauketa ta kutsa cikin dajin domin son ganinka dan ta tabbatarwa da kanta kaine ba waninka ba"
Shiru yayi yanajin wani irin raɗaɗi cikin zuciyarsa, yanaso yayi controlling zuciyarsa akan Azmah amma ya kasa, ji yake tamkar ya shaƙeta ta mutu kawai ya huta, daurewa yayi tare da taimakon addu'o'in da yake jerowa cikin zuciyarsa, cikin ƙarfin hali yace "Tom shikenan, maybe ta dawo gida ko zaki kaimu gidansu?"
Ɗaga kanta tayi tmda sauri ta buɗe bayan motar ta shiga dan nuna masa gidansu Zuhra nan Driver yaja suka tafi.Koda sukaje gidansu Zuhra ta shiga taga babu kowa babu komai alamun yanzu an daina rayuwa a gidan, cikintane yayi wani iri ƙugi gabanta na faɗuwa, cikin sanyin jiki ta fito tace "kamar sun tashi fa" ta faɗa Voice ɗinta na Cracking.
Kallan gidan yayi tare da ƙarewa gidan kallo, shifa har yanzu bai yadda cewar su Zuhra sunyi rayuwa a wannan kangon gidan ba, shiru yayi baice komai ba ganin wani yaro ya kirashi saiga yaron yace "Nan gidansu waye?"
Ya faɗa yana sauraran yaron, yaron yace "Gidansu Abokina Yusha'u ne da Auntynsa Zuhra" sauri yayi ya runtse idanunsa yay saurin juyawa ba jin yadda idanunsa suka kawo ruwa, motar ya shiga Driver ya jashi tare da faɗawa Azmah ƙura a jiki suka tafi suka barta a wajan ba tare da sun waiwayi inda suke ba.*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...