page 10

251 26 2
                                    

*Assalamu Alaikum, ina muku albishir da maganin sanyi wato infection idan zaku siya maganine me kyau kuma mai ingancine, sahihin maganin sanyi wanda inhar akwaishi a jikinki da yardar Allah zai miki magani cikin lokaci kanƙani,matan aure sunasha, ƴan mata suna sha, haka zalika yaran da suke fama da matsalar sanyi suma zaku iya basu, maza suna sha, gaskiya ɗaya zan iya faɗa muku shine maganin nada kyau, karku tsaya sanya maza garzayo wajan Mum Irfaan domin siyan maganin sanyinki a hannu, siyan ɗaya zakiyi koko sara zaki duk akwaishi, sannan akwai man gashi na al'arabee mai saka tsahon gashi, tsayin gashi, taushin gashi, cikar gashi uwa uba yana maganin dandruff me kike jira ƴar uwa maza tuntuɓi Mum Irfaan domin siyan ingantattatn maganin sanyinki haɗe da Man kitso da sauran abubuwan gyaran jiki, in kina da buƙata zaki iya tuntubata ta wannan numbern 08130515037 plz idan baki shirya ba karkimin magana mu ɓatawa juna lokaci*

Cikin sassarfa ya fito yaga suna inda suke basu tafi ba, ga dukkan alamu sunyi matuƙar farin ciki da ganin junansu, Zuhra ganin ya dawo yasata ɗan sakin Azmah tana kallanshi, haka kawai kirarsa take mata kama dana shi, shima ganin ta maida hankalinshi akanshi yasashi harɗe hannayansa ƙafafunsa sunmai nauyi da yawa, yana tsananin fargaba kar yaje yaga ba ita bace dan tabbas yaga ba ita bace watanta ce zuciyarsa zata iya bugawa da ƙarfin gaske, Azmah ɗan taɓa Zuhra tayi tace "Beb dan Allah kiyi yaƙi da zuciyarki akanshi inhar ta fara raya miki wani abu akanshi, domin kuwa bazai taɓa sauraranki ba har abada, zuciyata ta daɗe da kamuwa da sonshi tun lokacin datai tozali dashi, sede koda wasa bai saurareni ba duk da nasan ya hango zallar soyayyarshi a idona"
  Hankali Zuhra na kanshi take sauraran Azmah, Zuhra tace "Ko kaɗan zuciyata batai yunƙurin kamuwa da sonshi ba Azmah, saidai ƙirarsa da yadda zuciyata ke matuƙar bugawa yasa nakejin wani abu game dashi, yanamin kama da Mijina" gum tayi ta rasa yadda zatai dan batasan wannan kalmar ta fito daga bakinta ba.

    Azmah kallanta tayi da matuƙar mamaki tace "Miji fa kikace?, dama kina da aure ban sani ba?"
Ɗan daburcewa tayi tare da sauri ta kauda kanta akan Muhammad Alee suka fara tafiya ba tare data bata amsar data tambayeta ba, Azmah da ido tabita dashi tanason jin ƙarin bayani tace "Kefa na tambaya, amma naji kinmin shiru"
   Ɗan murmushi Zuhra tayi tace "Tabbas inada miji, saidai Allah yayi masa rasuwa Azmah ta dalilin wani ɗan hargitsi da akai da Familynmu ranar ɗaurin aurena, bayan an ɗaura ne wannan abun ya afku, dan ban manta wayanmu dashi na ƙarshe ya kirani a waya yake shaidamin da yanzu na zama mallakinsa, a lokacin yayi-yayi mu haɗu naƙi yadda nace bazanzo ba saboda nasan halin Ya Sani zai iyamin komai tunda har ya tabbatar da niɗin mallakinsa ce, babu magiyar da baimin ba nace ban zuwa saboda lokacin ina ɗakin ƙanwarsa Jiddah don a gidansu akai komai ssboda mahaifinsa Wan mahaifina ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, saidai mu bama zaune a ƙasarmu Nigeria Daddyna yana aiki a Dubai a wani babban Hospital, shi kuma Ya Sani tun ina ƙarama yake sona impact da soyayyarsa na tashi tun bansan menene so ba, shine ya koyamin yadda zan soshi, munyi wata irin soyayya wanda dagani har shi mun tanadarma kanmu wata irin tsaftacacciyar soyayyar da zamuyi da junanmu, saidai kash wasu mutane saboda son zuciyarsu aka kawowa Familyna hari da ruwan bindigu, ni kaɗai ce na tsira Azmah sai kuma Iyayena da Ƙanina suma dan basa tare damu ne, a gabana Jiddah ta rasu fa, bayan sun aikata fyaɗe a gareta, ta faɗa muryarta na cracking, sannan tace "Bayan ina tsugunne akan gawar Jiddah sai ganin Auntyna nayi wacca nake matuƙar ƙauna a rayuwata itama an harbeta gata da ƙaramin ciki basuyi la'akari da cewa ita ɗin matar aure bacs suka aikata fyaɗe a gareta, shekararta bakwai da aure Allah bai bata haihuwa ba sai lokacin amma haka suka harbeta a cikinta da kuma goshinta" share hawayan fuskarta tayi tana sauke ajiyar zuciya hawaye na malala daga kuncinta.

    Azmah shiru tayi tana jinjina wannan lamarin ta kasa magana, jingino da Zuhra tayi kan kafaɗarta ganin sun fara hango Titi tace "Me kukai musu?"
   Ɗan kallanta tayi da idanunta wanda suka sauya kala tace "Azmah kenan, kome mukai musu mun cancanci haka daga garesu?, ba komai mukai musu ba face suɗin azzalumai ne kawai macuta, akan gonar Kakanmu sukai haka wai sunaso zasuyi wani Company su kuma sukace bazasu saida ba sunyi-sunyi sunƙi saida musu, daga ƙarshe suka zuba ma'aikata aka fara gyara Gonar kasancewar Babbar Gonace dan anguwa guda ce tana da matukar girma yadda bakya tsammani, su kuma iyayanmu suka makasu a kotu kasancewar gabaki ɗayansu kowa yana da hanya hakan yasa mu mukai nasara akansu, ashe abun yayi musu matuƙar ciwo tare da ɗaukar alwashin sai sun hallaka ahalinmu

Azmah shiru tayi tana nazari can kuma tace "Su waye suka aikata muku hakan?"
  Murmushin ƙarfin hali tayi, yayinda suka tsaida Mota suka shiga Zuhra bata ƙara cewa Uffan ba, Azmah tace "Ki faɗamin inaso insan wani abune, sannan kuma zan faɗa miki kema abunda baki sani ba"
  Ganin sun ɗauki hanya cikin motar yasa Zuhra murmushin takaici tace "Ki manta kawai"
  Azmah tace "Ki faɗamin Faɗima"
  A ɗan razane ta kalleta tana mamakin a ina tasan ana kiranta da wannan sunan, sannan a iya saninta Ya Sani ne kaɗai ke kiranta dashi, kallan Azmah tayi sai take gani kamar tasan wani abu game da ita.

   Azmah dariya tayi duk da zuciyarta tsantsan tsanar mahaifinta ce ta dirar mata tare da tausayin kanta na cewar bazata taɓa samun Muhammad Alee ba har abada, ganin Zuhra ta kafeta da ido yasata saita kanta tana so ta maida hawayan da suke ƙoƙarin sauka daga idanunta, numfasawa tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace "Mahaifina, da babban abokinshi Bashir Iyan Tama sannan tare da ɗansa Fahad Iyan Tama ne suka aikata muku haka ko Zuhra?, Mijinki be mutu ba yana raye domin shine wannan wanda yayi garkuwa dani wato  Muhammad Alee...."

   Azmah bata ƙarasa ba taga Zuhra tayi wata irin zabura idanunta gabaki ɗaya a waje labarin ba ƙaramin tarwatsa mata ƙwaƙwalwa yayi ba, ba tare data ƙarajin wani ƙarashen labarin ba tamkar wata zararra tace "Driver Wait" ta faɗa da wata irin murya wacca ita kanta batasan tana da ita ba, Driver saida ya kusan sakin kan Motar saboda yadda taimai magana, sauran fasinjojin kuwa su a tunaninsu ko batada lafiya ne, Driver daƙyar ya samu guri yayi parking Zuhra ta fara ƙoƙarin fitowa, Azmah ruƙeta tayi tace "Ina zaki" ba tare data kalleta ba ta sauka akan motar ta tsaya a bakin Titi tana neman Machine ko Mota, tunowa datayi cewar baya kaunar ya ganta akan machine yasata tsayawa tama jiran mota, ganin Azmah zata fito yasata cewar "Please ki tafi gidanku zamuyi waya, sannan zaki ga result ɗin da mahaifinki ya aikata dan Allah karki Challenging ɗina domin halinsa ne" ta faɗa muryarta na rawa, so take ta samu damar yin kuka ko zata samu sauƙi akan abunda takeji a cikin zuciyarta, tafiya ta farayi ba tare data kara waiwayan Azmah ba saida tayi nisa sannan ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi ta kasa yadda cewar Ya Saninta ne ke Kidnapping sannan shine yake rayuwa a cikin wannan Dajin har har yanzu ta kasa yadda da cewar shine, tanaso taje ta tabbatar da gaskiyar maganar Azmah saidai jikinta tabbas na bata cewar shine saboda bugawar da zuciyarta takeyi tayi yawa, ganin Taxi yasata tsaidata ba tare data jira sunyi ciniki ba tai masa kwatancan gidan Man da zai kaita ba abunda takeyi sai kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tayaya za'a mata Ya Saninta ne ke rayuwa cikin Dajin nan, hannu tasa aka tana mai matuƙar tausayin kanta kwata-kwata shekarunta 18 amma take shiga wannan tashin hankalin a rayuwarta, Driver na sauketa ta ciro kuɗi ta bashi duk da kuɗinshi baikai haka ba amma haka ta miƙa masa ta kutsa wannan Dajin tama tafiya tana share hawayanta, ganin ta hango Bukkarsa yasata ƙara sassarfa tana haɗawa da gudu-gudu, cikin lokaci ƙanƙani ta isa wajan gabanta na  faɗuwa zuciyarta na neman tsinkewa, tamkar wacca bata da laka a jiki haka ta dafa Bukkar tana tsoron t shiga taga da gasken shiɗinne, tabbas in shine bazata taɓa yafewa kanta ba, dafe ƙirjinta tayi tanaji tamkar zuciyarta zata fito zaboda tsananim fargaba, saita kanta tayi tare da goge hawayan fuskarta ta shiga Bukkar idanunta a runtse tana mai matuƙar jin tsoron buɗesu.

*Kuyi maneji wallahi banda caji🥴 gashi Cazana ta lalace duk ni kaɗai*

*Yawan Comments, Yawan postings akai-akai*

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now