Page 32

197 18 6
                                    

Hankalin Doctor ne yayi matuƙar tashi ganin yadda ta faɗi a kife ba tare datai la'akarin da cikin dake jikinta ba, zagayowa yayi yazo inda take tare da kiran nursings kafin kace me har Nursing sun shigo aka fara bata agajin gaggawa.
    Zuhra kallan Muhammad tayi ganim yana ƙoƙarin buɗe sabon gidansu wanda zasu tare saidai gaban gidanne gyara baizo ta kanshi ba, hannunta ya ruƙo yana faman yi mata sannu suka shiga gidan, tsayawa tai cak tana ƙarewa gidan kallo, ganin gabaki ɗaya an canza tsarinsa duk abunda ta sani adaa yanzu babu shi ko ɗaya ga gidan ya ƙarama girma naban mamaki ya zama tamkar wani estate cikin gidan ya haɗu yadda mai karatu baya tsammani ya fita tamkar turawane suka tsara ginin gidan, dawo kanshi tai tana binsa da kallo tace "Ya Amma wannan ba gidan da nasani bane bako, girman yay yawa gashi duk abunda na sani banganshi a gidan ba kamar rushe gidan akai gabaki ɗaya aka fidda wani tsarin"
Murmushi yay mata tare da jan hannunta suka shigo cikin gidan,buɗe ƙofar ɗakin Parlourn yayi batasan lokacin da bakinta ya furta kalmar "Wow" ba ganin yadda duk wasu kaya dake Parlourn Forum ne kama daga kujeru da duk wani abun more rayuwa, ba abunda ɗakin yake sai wani irin haske na musamman wanda aka zuba musu Bulb ɗin zamani, bakinta ya kasa rufuwa ta kasa motsa ƙafarta nan da can murmushi ɗauke a yalwaltacciyar fuskarta, faɗi take "Masha Allah" dariya yay mata ganin yadda yaga duk tabi ta ruɗe na ganin irin tsarin ginin gidan da akai, ɗaukarta yay cak tamkar wata Baby ya ajiyeta a lafiyayyar sofa yana mata dariya ƙasa-ƙasa tare da ɗan nishi yana faɗin "Wasa-wasa mugun nauyine dake...."
   Ganin ta miƙe yasa shi kasa ƙarasa maganarsa yana kallanta yaga sai shafa bangon ɗakin take tana ƙarewa Parlourn kallo tabbas Parlourn ya haɗu iya haɗuwa saika rantse kana birnin duniyane saboda yanayin tsarin da kuma dukiyar daya kashema Parlourn, "Karfa ki zama ƴar ƙauye sai kace bakisan wasu daga Parlourn nan ba"
Ya faɗa tare da ruƙo hannunta yajata zuwa Bedroom, suna shiga Zuhra tace "Wow" komi ja ɗakin Blue da Fari be Set ɗin Gadonne Golden tamkar Gadon da'a ƙerasa da ɗanyan Gold, a hankali suka taka har zuwa bakin Bed ɗin, Bedsheet ɗin Bed ɗin ta fara shafawa saboda laushinsa da taushi a hankali ta haye gadon tare da rungumar Pillow tana sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin kace me bacci yayi nasarar kwasheta, Muhammad yanata bata labarin jin shirun yayi yawane yasashi leƙa fuskarta ganin hartai bacci yasashi murmusawa yace "Ikon Allah daga kwanciya sai bacci kai wannan Babyn namu yazowa da Mommansa kasaala" gyara mata kwanciya yayi ya fita daga ɗakin da duba sauran ɗakunan yaga abunda ya umurta da a saka an saka mai.

     Firgit ta farka tana ƙoƙarin tashi sai taga hannunta saƙale da Drip, ƙoƙarin cirewa kawai take tana surutai tamkar sabon kamu, ta hakane tai nasarar cire Drip ɗin daga hannunta tare da ɗaukar Veil ɗinta tabar Room ɗin, ba inda ta dosa sai neman inda Lap ɗin Hospital ɗin yake, tabbas saita kashe Muhammad kowa yahuta, yayinda ta ƙuduri aniyar watsawa Zuhra Poison saidai duk abunda zai faru ya faru, watace ta nuna mata Lap ɗin sai taci sa'a a buɗe yake sakai tayi ta shiga sai ta hango wata Nurse a ciki, tattaro murmushi tayi ta doshi inda wannan Nurse ɗin take tace "Doctor na kiranki yacemin Emergency call ne" jin haka yasa wannan Nurse ɗin ajiye abunda tazo nema tace "Dan Allah ki zauna anan bari naje na dawo"
Murmushi tayi tace "Ba komi saikin dawo"
Ganin ta fita yasata bazama neman Acid haɗe da Poison cikin lokaci ƙanƙani tai nasarar samunsu, tsayawa tai fuskarta ɗauke da murmushi tana jujjuyasu, tabbas kamar yadda yanzu rayuwarta ta lalace haka zata saka da Zuhra *GARARI A RAYUWARTA* a hankali ta turo ƙofar ta fara leƙe kana ganinta kasan bayada gaskiya ganin babu wanda ke shawagi a gun yasata saurin fitowa daga Lap ɗin ta fara tafiyarta cikin tsanake ba tare data waiwaya bayanta ba har ta fita daga Hospital ɗin, ganin ta fito bakin Titi ne yasata sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya dan ita har ga Allah sam ta manta da batun Doctor na cewar tana ɗauke da ciki, tsaida mai Keke Napep tayi direct anguwarsu Zuhra tai mishi kwatance sannan ta shiga motar ya jata.

    Bayan ya watsa ruwane ya fito daga Baderoom ɗin jin yadda cikinsa ke ƙugi da alamun yunwa yakeji, fitowa harabar gidan yayi tare da buɗe Motarsa ya ɗauko Meat Pie da Yoghurt ya koma cikin gidan, Kallo ya kunna ya maida hankalinsa akan labaran duniyar da akeyi.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now