page 21

252 24 17
                                    

Dakatar da ita yayi da hannayansa tare da jefa mata kallan tsana, "Excuse me" itace kalmar daya faɗa mata yana ƙoƙarin raɓawa gefenta ya wuce.
   Raurau tayi da idanunta tace "Dan Allah ka tausayawa zuciyata Muhammad, wallahi na faɗa soyayyarka wanda babu wanda zai iya fiddani saikai, please ka tausayamin" ta faɗa tana goge hawayan fuskarta.
Murmushi rainin wayo kawai yayi mata yayinda zuciyarsa babu komai face tsantsan tsanarta, sai yanzu ma yake daya sani na shiga rayuwarta da yayi gashinan yanzu tana so ta takura masa, ganin bata da niyyar bashi hanyane yasashi komawa inda ya fito, jin hannunta cikin nasa yasashui juyowa a fusace tare da nunata da ɗan yatsa, idanunsa ne suka sauya kala cikin wata irin murya yace "Be careful" yana faɗan haka ya fara tafiya cikin sassarfa.
  Share hawayan fuskarta ta ƙarayi tace "Ka tafi, amma ka sani da ƙafarka zaka dawo guna kana roƙona akan dan Allah na karɓi soyayyarka, anan ne zaka gane cewar shayi ma ai ruwane"
Maganarta ce ta dakatar dashi daga tafiyar da yakeyi, juyowa yayi yana mai mata tafi fuskarsa ɗuke da yalwataccan murmushi, harya buɗe baki zayyi magana kenan sai kuma ya fasa ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ba abunda yake tunani sai kalamanta, ganin yadda ta faɗa cike da Confidence hakan na nufin akwia shirin da zatai kafin haka, tabbas yasan kaidin mace bashi da daɗi ko kaɗan amma ya zama dole ya dakatar da Azmah akan duk wani shirme datake ƙoƙarin yi akanshi.

  Azmah ganin ya tafi yasata durƙusawa a wajan ta fashe da wani irin matsinancin kuka, tabbas tasam zuciyarta tana dakyau amma soyayyar Muhammad tanaso ta lalata mata duk wani karamci na zuciyarta, yanzu ji take ba abunda bazata iya aikatawa akan Muhammad Alee ba koda kuwq zata rasa ranta ne, tare da alwashin zata iya salwantar da Zuhra dan ganin burinta ya cika, saidai tana matuƙar jin tsoron Allah amma wani ɓangare na zuciyarta ba abunda yake faɗa mata sai sharri, dafe zuciyarta tare da girgiza kanta tana faɗin "Bazan iya aikata shirka ba, ya Allah ka tausayawa zuciyata karta faɗa mummunan hali, ya Rabbi ka dubeni da idanun Rahama ka bani juriya da dangana na rashin Muhammad Alee" kuka ta cigaba da rerawa a haka har ta samu ta rarraba ta fita waje tare da tsayawa a Titi dan taran Keke Napep, ciwon daya daɗe yana nuƙurƙusan zuciyarta ne ya dawo tare da alwashin ko zata mutune ta ɗauki ɗan marar mantawa da Muhammad Alee har abada, saidai zuciyarta sam bazata lamunci rabuwa dashi ba.

     Gabaki ɗaya ranshi a jaguke yake, danme yasa Azmah zata shigo rayuwarsa alhalin yanzu yaba tare da mafi soyuwa a zuciyarsa, shi tsoronsa ɗaya ma kar Zuhra ta gane abunda Azmah take ƙoƙarin yi tabbas zai fuskanci ƙalubale a wajan Zuhura.
   Dan jingina yayi da jikin kujera yayinda yake danna Horn a hankali dan Get Man yazo ya buɗe masa Get, idanunsa  a lumshe yana jiran a buɗe masa, ganin ya buɗe masa Get ɗinne yasashi shiga ciki ya nufa Parking Space, hango wata tsaleliyar mota da yayi kuma kamaf Zuhra na ciki yasa gabanshi ɗan faɗuwa, saida ya zo kysa dasune ya gane Fahad ne a ciki tare da Zuhra, ɗan furzar da iska yayi tare da lumshe fararan idanunsa haɗe da cije jajayan Lips ɗinsa, numfasawa yayi ya fito daga cikin motarsa duk da motar Fahad gata ga tashi ne, ko kallan inda suke bayyi ba ya fara tafiyarsa cikin isa da taƙama tamkar ɗan basarake, direct Part ɗinsa ya nufa tare da banko ƙofa yana wani irin huci, hargitsa lafiyayyar sumarsa yayi ya zauna gefen Bed yanajin wani irin kishi na nuƙurƙusarsa, sajanshi yaɗan shafa yanaso ya dake amma ina ya kasa, tashi yayi ya fito daga ɗakin nasa, direct Balcony ya nufa kasancewar tana gab dasu Zuhran ya fara zarya agun, tamkar hankalinsa baya gun amma gabaki ɗaya hankalinsa kacokan yana tattare dasu, ganin tsayuwar bazai masa ba yasashi janyo kujera ya zauna tare da zari wayarsa ya fara danne-danne tamkar hankalinsa nakan wayar.

    So uku Zuhra tana kama Handle ɗin ƙofar danta fito amma Fahad ya hanata, ganin tunda ya lura da shigowarsa yasa Zuhra gabaki ɗaya hargitsewa, tsantsan tashin hankali ya bayyana a fuskarta.
   Koda wasa Fahad bai gane Muhammad Alee ba, hakan yasashi tambayarta "Wai wanene wannan?"
   Rufe idanunta tayi sannan tace "ƙanin mahaifiyata ne"
Jin haka yasa Fahad yaɗan samu natsuwa tare da sakin fuska ba kamar ɗazu ba, ƙara kallan Muhammad Alee tayi tasan tabbas ranshi yayi mugun ɓaci ganin har yanzu bata fito ba.
    Ɗan ɓata fuska tai tace ma Fahad "Bari naje nasan Mommy nacan tana jirana" tana gama faɗan hakan tai wuf ta fito tana sauri tana famab harhaɗe ƙafa.
  Muhammad ganin ta fitone yasashi saurin tashi agun tare da juya mata baya shima ya fara ƙoƙarin shiga Part ɗinsa.
   Zuhra ganin haka yasata ɗan ƙara sauri tanaso ta cin masa bata damu da Fahad dake zaune cikin motarsa ba dan tabbas tasan yau ta ɓata mishi rai matuƙa, ɗan lungun da zai sadashi da Part ɗinsa ya nufa yana sauri dan ko kaɗan bayaso ta cin masa.
Ganin da gaske sauri yake yasata haɗawa da gudu tai saurin ruƙo hannunsa, jin yadda yayi saurin raba hannunsa da natane ya tabbatar mata dayau tata ta ƙare, kallanshi tayi fuskatar tamkar wacca zatai kuka tace "Please Yaya" ta faɗa muryarta na Cracking.
  Ko kallan inda take bai kalla ba sai ƙoƙarin buɗe ɗakinsa kawai yake, Zuhra tana ƙoƙarin shigane yasashi kallanta da idanunsa wanda suka sauya kala, cikin dishewar murya yace "Dakata, jeki kula da baƙonki"
  Yana faɗan haka ya banko ƙofar saura ƙadan ya haɗa da hannunta, bin ƙofar tayi da kallo tare da sauke wata irin ajiyar zuciya, murɗa Handle ɗin ƙofar tayi taji ya saka mata Key, itama tuni tahau dokin zuciya tabar wajan tare da alwashin bazata ƙara bin ta kanshi ba, koda ta dawo wurin taga Fahad harya tafi taɓe baki tayi ta nufa hanyar Parlour ɗinsu, Direct ɗakinta ta nufa ta kwanta, tashi tayi ta shiga Bathroom dan watsawa kanta ruwan zafi, bayan ta kammalane ta fito jikinta ɗaure da Towel doguwar riga kawai ta saka mara nauyi kasancewar ana zafi yau ta hau gado ta kwanta.
  Yayan tane ya faɗo mata a rai tasan bata kyauta masa ba, kuma dole yayi kishinta inhar yana sonta da gasken gaske, tuno irin kallab daya watsa matane ya tabbatar mata da cewar yana jin haushinta.
    Uti ne ya banko ɗakinta yana huci, harta buɗe baki zatai mai jaraba kenan sai taji yace "Aunty Azmah ce tazo"
  Ɗan zaro manyan idanunta tayi tace "What?" ta faɗa tana dafe ƙirjinta.
  "Wallahi itace tazo tana Parlour" ya faɗa yana maida numfashi.
  Tashi tayi tace "Muje"
Bayansa tabi tana zuwa sai hango Azmah tayi tai kyau matuƙa taci gayu tankar ba ita bace ta gama rusa kuka ɗazu ba, da murmushi Azmah ta tari Zuhra yayinda Zuhra yaƙe kawai tai mata, taga Azmah ta ƙara komawa ƴar gayun gaskene, ga kyanta ya ƙara bayyana duk da bazata taɓa kamo ƙafar Zuhra ba, wani murmushin ta jefeta dashi tace "Ko baki murnar ganina bane"
  Yaƙe Zuhra tayi ta ƙaraso inda take tace "Ai na kaza yadda cewar ba mafarki nake ba, kece yau a Kano, ya KD ko ince Birnin Gwari?"
   Ƴar dariya Azmah tayi tace "Ai nafi 2 Months a garin Kano, kinsan Daddy na yana gidan kaso, so shine Mom ta tattaro komai nata ta dawo gidan iyayanta"
  Murmushi kawai Zuhra tayi tana ƙoƙarin ɗauko mata ruwa, ganin Muhammaf Ya shigo dagashi sai wani gajeran wando iya gwiwa wanda farar fatarsa ta bayyana yasa Zuhra ɗan ɓata fuska dama sai addu'a take akan Allah yasa karya fito saboda Azmah.
  
Azmah ta ɗan shagala da kallan Muhammad har saida Zuhra taji kamar ta ɗaura hannu aka ta rusa ihu, samun kujera yayi can nesa dasu ya kira Uti dan ko kaɗan bai kawo da wata a Parlourn ba bayan Zuhra.
   Azmah cikr da kissa tamkar yau ta saba ganinshi tace "Ya Muhammad ina yini_?" ta faɗa tana faman sadda kanta ƙasa, ɗan juyowa yayi ya kalleta, abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, miƙewa yayi ba tare daya ansa gaisuwarta ba, ya kalli Zuhra data tsaya a tsaye tana kallansu yace "Ki kawomin Shayi dakina"
  Ɗaga kanta tayi da sauri ta nufa inda Azmah takr ta aje mata Drinks da ruwa ta tafi Kitchen, Allah-Allah kawai take Lipton ɗin yayi ta kai masa, yayinda Azmah ta cika tamkar ta fashe, fitowa tayi hannunta ruƙe da Cup ta kalli Azmah tace "Ina zuwa" Azmah miƙewa itama tayi tace "Muje na rakaki" kallanta tayi sororo tanaso ta gano wani abu game da Azmahr, ɗan tsuke Fuska tayi tace "Bari na kai masa na dawo, kinsan ba kowa yakeso yana zuwa Part dinsa ba" sauri tayi tabar wajan ba tare data jira abunda zatace mata ba.
   Ɗan tura ƙofarsa tayi ta hangosa zaune ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, ganinta yasashi tashi a tsanake ya rufe ƙofar tare da karɓar Cup ɗin hannunta ya aje, ƙugunta ya kama fuskarsa sam babu walwala yace "Zuhra bakyajin magana ko?, banace ban yadda Fahad ya runƙa zuwa gunki ba, wato ma da kika ganni bama ki fitoba saida kika ɗauki wajan 30 minutes sannan kika fito ko"
  Ɗan rau rau tayi da idanu tace "Yaya please kayi haƙuri, dole zan saurari Fahad kuma zan kare mutuncin kaina, Fahad ya canza ba kamar yadda ka sanshi ba a da, inaso na samu damar sanar dashi gaskiyar lamarinne saboda banso in runƙa ɓata mishi lokaci"
   Bige mata baki yayi sannan yace "Banson ganin da Fahad, inba haka ba zan miki abunda baki tsammanin zan miki shiba a gidannan, kinji dai na faɗa miki, ita kuma waccar a ina tasan gidannan?"
  Tsuke fuska Zuhra tayi tsantsan kishi ya bayyana a fuskarta tace "Oho nima na sani, nasan gunka tazo ai"
  Dariya maganar ta bata tare da ja mata kumatu yace "In baki wasa ba aure zanyi tunda ko kaɗan bakya bani kulawarki, kuma ke kanki kinsani nafi kowa buƙatarki a rayuwa"
  Hawaye suka taru a idanunta tace "Yanzu saboda bana baka kulawa kake kiramin zakai aure?"
Ta faɗa tare da rushe mishi da kuka haɗe da bugun faffaɗan ƙirjinsa, dariya yahauyi mata yana ƙoƙarin ruƙe hannayanta yace "To dakata, inhar na sakaki kimin abu kinamin keda kishiya har abada"
  Goge hawayan fuskarta tayi tace "Da gaske?"
Lumshe idonsa yayi tare da buɗesu ya ware hannayansa alamun tazo, ba musu ta fada jikinsa gabaki dayansu suka saki ajiyar zuciya, ɗan kallanta yayi da idanunsa wanda suka fara sauya kala, cikin muryar raɗa yace "Kiss me" ba musu ta saka bakinta saitin nashi ta fara kissing dinsa a hankali yayinda hannunsa na bayanta yana ƙokarin cire mata bra, kallanshi tayi shima kallan nata yayi saurin runtse ido kawai tayi ganin yadda ya fara tafiyar mata da salon nasa.

   Azmah kallab agogo tayi taga wajan awa ɗaya kenan da tafiyar Zuhra babu ita babu alamunta, wani irin mugun kishine ya turnuƙeta haɗe da tsanar Zuhra, batai aune ba saiji tayi hawaye ya sauka akan kunjinta, sharewa tayi ta dauki Hand Bag ɗinta ta fito ba tade datayiwa kowa sallama ba, wayarta ta ciro ta kira wata ƙawarta datayi a Kanon tace "Kina ina?" shiru tayi ba amsa sannan tace "Okay to mu haɗu tabbas naga alamu shwararki itace mafita a gareni zaki rakani wurin dan fara aiki cikin gaggawa akan Zuhra da Muhammad" katsewa wayar tayi tana faman maida numfashi kamar wacca tai danbe.

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now