Haka rayuwa taita tafiyarwa su Zuhra a garin Kano yayinda wata irin shaƙuwa mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin Fahad da Zuhra, yanzu duk wanda yasan Fahad to tabbas yasan Zuhra idan har kanason kaga kyautar Fahad ko yalwatacciyar fara'ar Fahad to kayi masa kirari dana Zuhra, Familynshi babu wanda bai santa ba, duk da Fahad yasha yunƙurin ce mata zai turo magabatansa sai tai saurin dakatar dashi, mahaifiyarsa kuwa ba ƙaramin jin daɗin haɗuwarsa da Zuhra tayi ba ganin yadda yaron nata ya fara natsuwa ba kamar daba, yanzu duk wani harkar mata ya jinginar da ita, haka zalika baishan Wine saidai abubuwan shaye-shaye wanda ba'a rasa ba, shima koda wasa bai taɓa barin Zuhra ta sani ba, yanzu ƴan aikin gidansu sun samu sukuni ba kaɗan ba, suna shawaginsu san ransu, duk da Fahad ya kasance jarabban namiji bai fasa halinsa na kula matan banza ba saidai ya mugun ragewa ba kamar daba, sannan yanayinsa cikin taku kar Zuhra ta gane.
Yau ta kasance Sunday yayinda Fahad yacewa Zuhra ta shirya zai kaita Shoprite dan ta siya abubuwan buƙata, ba haka taso ba dan ita ko kaɗan bataso tana yawo da Fahad saidai ba yadda zata iya saboda cikar burinta, tashi tayi taje ta shirya simple make up tayi haɗe da saka doguwar riga sai Veil data saka, sai Hill ɗin takalminta kasancewar Zuhra mayyar saka Hill ɗin takalmi ce, ganin wayanta na Ringing ya tabbatar mata da cewar shine yazo yana jiranta.
Fitowa tayi taga ɗakin taga Ƙaninta Uti ne kawai a Parlourn kallanshi tayi tace "Kai Mommy fa?"
Ba tare daya kalleta ba yace "Tana Bedroom"
Juyawa tayi ta nufa Bedroom ɗin mahaifiyarta, tana ƙoƙarin zama akan Bedside drawer kenan taso ta faɗi ganin yadda takalmin ya turguɗeta.
Mahaifiyarta tace "Ke sai kace dole saka wannna takalman in baki wasa ba sai wataran yayi kiki targaɗe".
Cikin muryar shagwaɓa tace "Mommy!, please ki daina cewa haka mana, dama nazo na faɗa miki ne zan ɗan fita Outing but bqzan daɗe ba zan dawo"
Kallanta tayi da mamaki tace "Outing kuma?, dama kinsan garin Kano banda labari?"
Murmushine ya bayyana a fuskarta tace "No zamuje nida Fahad ne, wallahi Mommy shiya tursasamin akan dole sai naje, yaya zanyi dole naje kinsan ranar Monday ɗinnan yace zai kawomin Takaddun wasu filaye na mahaifinsa".Shiru Mamanta tayi na ɗan wani lokaci sannan tace "Zuhra ina tsoron Allah ina tsoron kaidin Fahad, kinsan nidake aka zauna aka warware mana zare da abawa akan Fahad yana da hatsari mai muni, banso kuna kasancewa waje guda banason wani mummunan abu ya sameki"
Lumshe ido Zuhra tayi tace "Da yardar Allah, Allah bazai taɓa ba Fahad damar yimin wani abuba, sannan jikina na bani ba abunda Fahad zai iyayi akaina, saboda na gina mishi soyayyata da bulo na ƙarfe mai samun iya ruguza wannan soyayyar sai mutum ya shirya"
Nahaifiyarta jifanta tayi da Pillow ɗin dake kusa da ita tai saurin matsawa ya sauka ƙasa tare da fitowa daga ɗakin tana dariya ƙasa-ƙasa, ɗan ɗaha muryarta sama tayi tace "Mommy saina dawo" ta faɗa tana ƙoƙarin barin Parlourn.Hangoshi tayi a Parking space hannunsa rungume a ƙirji kanshi a ƙasa yana jiranta, da murmushi ta ƙarasa gurinsa tana cewa "Aimin afuwa ranka ya daɗe"
Kallanta yayi da idanunsa wanda suka sauya kala saboda yadda yau ya tashi da mugun feelings don kuwa rabonshi da mace ya ɗan kwana biyu Beb ɗin da take rage masa zafi bata nan tayi tafiya zuwq Abuja, gashi yanzu Fahad ba ko wace mace yake tayawa ba, hakan yasa ya daure saidai yau tashin hankalin da yake ciki yafi na ko yaushe, ganin irin kallan da yake jifanta dashine yasata ɗan tsarguwa da kanta, haɗe fuska tayi tace "Wannan kallan fa?"
Ɗan sauke hannunsa yayi yana ƙoƙarin buɗe mata ƙofa baice mata Uffan ba ta shiga, da kallo Zuhra ta bishi dashi dan tunda suke bata taɓa ganinshi a irin wannan yanayinsa ba.
Motar ya shiga yana ƙoƙarin tayarwa dan duk karta gane halin da yake ciki, dan yasan tabbas yayi yunƙurin gwada mata wani banzan hali a yanzu zata iya daina sauraransa kwata-kwata, gashi shi son tsakani da Allah yake mata, yana mata wani irin tsaftaccaiyar soyayya dan koda wasa bayaso ya saba taɓa mata wani sashen na jiki ba tare daya aureta ba.
Hakan da yayi mata yasa kanta ɗaurewa, kallanshi ta kumayi taga ko kaɗan bayaso su haɗa idanu "Fahad!" sunan data kirashi dashi tana kafeshi da kyawawan idanunta masu mutuƙar hargitsa duk wani lafiyayyan namiji bareshi da yake cikin mawuyacin halu.
Cikin sanyin murya yace "Na'am" hankalinshi naga tuƙin da yakeyi yana ƙoƙarin fita daga gidansu.
"Meke damunka?" ta ƙafa jefo mishi tambaya, murmushi ne ya suɓuce masa yayinda Dimples ɗinsa suka lotsa gabaki ɗaya yace "Ba komai ba"
Gyara zamanta tayi bata ƙara ce mishi uffan ba, a haka har suka ƙarasa inda zasu don yin siyayya.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...