Tana fita adaidaita ta tsayar tahau, tare da alwashin raba Muhammad da Zuhra.
Zuhra a hankali ta zame jikinta dana Muhammad, yayinda gabaki ɗayansu sunasm cikin tsananin son su kasance da junansu, ɗan kallanshi tayi itama kallan nata yayi da jarababbun idanunsa, ɗan matsawa gefe tayi tare da gyara ɗan kwallin kanta da Zip ɗin rigarta, kanta a ƙasa tace "Yaya bari naje nasan Azmah na jirana, kuma nasan zataji ba daɗi"
Tasowa yayi a kasalance yana faman harɗa ƙafa tamkar wanda zai faɗi ƙasa, kusa da ita ya zauna kamar zai shige cikin jikinta tare da kamo hannayanta yana wasa dasu, cikin kasalalliyar muryarsa yace "Please Zuhra, kin fiso naita wahala a rayuwata ne?, yaushe yaka mata ki ban dama a matsayina na mijinki"
Duk da Zuhra itama yanzu tana tsananin son kasancewa dashi dalilin irin yadda yake tafiyar da ita na kwanakinnan ya tabbatar mata da cewa ba abunda yafi komai daɗi face ka auri wanda yake sonka kaima kake sonshi, saidai ko kaɗan bazata taɓa bashi haɗin kan da yake buƙata ba har sai ta tabbatar da cewar auransu da gaske yana nan koko sai an gyara.
"Nasan me kike tunani Zuhra, kina tsoron ace auranmu ya lalace bayan kin bani haɗin kanki ko?"
Shiru tayi ba tare data ce Uffan ba, ƙara ɗan matse mata hannu yayi yace "Tambayarki nake"
Gyaɗa kanta kawai tayi alamun "Eh", murmushi ne ya suɓuce masa yace "Auranmu na nan fa, domin kuwa na tabbatar da haka, don haka ki saki jikinki da mijinki ki samu aljanna kawai"
Zuhra kanta a ƙasa tana kallan yatsunsu yadda yake wasanni dasu, "Ya Muhammad, ko kaɗan daa aure baya gabana, duk da nasan bansan menene romance ba a zahiri saidai ƴan kwanakin nan kanaso ka sakamin son romacing yadda baka tsammani,na fara sabawa da hakan, ni nasan kana tsananin buƙatata amma dan Allah muyi haƙuri da juna har sai munji me Daddy zai yanke akan haka"
"Faɗima..." dakatawa yayi jin ana knocking, kallanta yayi itama kallan nashi take, ba abunda suke tunani sai waye wannan.
Zuhra kallan Bed ɗinsa tayi ganin yadda suka hargitsa tamkar wanda sukai wasan danbe, ɗan zaro ido tayi tamkar mara gaskiya cikin whisper Voice tace "Waye?"
Ɗage kafaɗa yayi alamun shima bai sani ba, cikin sauri ta tashi ta fara gyara gadon duk da bai wani yi neat sosai ba amma ta gyara ba laifi.
Zama tayi akan 2seaters ɗin dake gurin kusa da ƙofa tana wuri-wuri da idanu, Muhammad kuma jallabiyarsa ya saka akan ƙananun kayansa ya nufa ƙofar dan buɗewa, ganin Daddy saida gabansa yaɗan faɗi, kasa matsa mai ƙofar yayi ya tsaya a bakin ƙofa tare da gaishe dashi, ba tare daya ansa ba yace "Mu shiga ciki muyi magana na kira wayanka a ƙalla 10 missed calls naga bakai picking ba"
Wani irin Saliva Muhammad ya haɗiye ya ɗan matsa mai ya wuce, wata irin kunyace ta ziyarceta wacca bazai iya fasaltata ba.
Shiga yayi dan ko kaɗan bai lura da Zuhra ba, fitowa tayi daga Bathroom tana sharce hannayanta tace "La Daddy kaine" ta faɗa tana pretending, ɗan satan kallanshi tayi taga yadda yakr faman sadda kai ƙasa, "Ya Sani!" ta kira sunanta tana ƙara yarfe hannayant, ganin bai kalleta ba yasata cewa "Yawwa na gama wanke maka Bathroom ɗin"
Ɗan ɗago da kai yayi yana maijin daɗi yadda ta fidda shi cikin ruwan sanyi, danshi ko kaɗan duk wata dabara kulle masa tayiTana fita adaidaita ta tsayar tahau, tare da alwashin raba Muhammad da Zuhra.

Ɗan ɗago da kai yayi yana maijin daɗi yadda ta fidda shi cikin ruwan sanyi, danshi ko kaɗan duk wata dabara kulle masa tayi, "Ba tare daya ƙara ɗaga ido ya kalleta ba yace "Okay"
Ya fara ƙoƙarin zama a ƙasa yayinda ita kuma ta doshi hanyar fita, dariya kawai abun yaba Daddy, ganin zata fitane yasashi kiranta na cewar "Zo kema"
Cikinta ne ya ɗan ɗuri ruwa, ta fara sosa kai tamkar mara gaskiya, dawowa tayi ta zauna itama kanta a ƙasa.
"Abunda yasa na haɗaku shine na tambayi Malamai mabanbanta akan yaya auranku yake a yanzu sunce auranku na nan daram saboda ƙaddarace ta rabaku ba da gangan kuka raba kawunan ku ba, dan haka nan da sati biyu mai zuwa zaku tare a gidanku, insha Allahu yau za'a fara aikin cikin gidan tunda an daɗe ba'ai amfani dashi ba, tunatarwata a gareku shine kowa yayi taka tsantsan domin kuwa daa da yanzu ba ɗaya bane" juyowa yayi yana kallan Zuhra yace "Ban yarda ba kuma ban lamunta ba Fahad ya ƙara zuwa ki fita ki tsaya dashi ba, kuskuren da mukai a baya ma Allah ya yafe mana, dan haka kibi mijinki dau da ƙafa insha Allahu zaki ga ribar yin haka"
Gabaki ɗayansu wani irin annurine ya bayyana a fuskokinsu, duk da kawunansu na ƙasa, harya tashi sai kuma ya dawo ya kalli Muhammad yace "Abunda Zuhra ta fara kaine zaka ƙarasheshi"
"Insha Allahu" cewar Muhammad.
Fita yayi ya barsu a ɗakin dan gabaki ɗayansu kansu na ƙasa har saida sukaji ƙarar rufe ƙofa.
Zuhra lulluɓewa tayi da Veil ɗinta tana dariya ƙasa-ƙasa.
Muhammad dariyar jin daɗi kawai yayi mata, yace "Oya jeki kar Daddy yaji kin daɗe a ɗakin nan"
Ba musu tai sauri tabar ɗakin dan batai tsammanin haka daga garesa ba, ta ɗauka yau mai rabashi da ita sai Allah, tuno yadda ta ganshi lokacin da Daddy yazone abun yayi mugun bata dariya, cikin murya irin wacca tai dariya tace "Ya Sani da kunya"
Dariya ta cigaba a haka harta ƙarasa Part ɗinsu ta saɗaɗa ta shiga ɗakinta kar mahaifiyarta ta ganta.Gabaki ɗaya gidan kana kallanshi zaka tabbatar da ana cikin tashin hankali, kaf ma'aikatan gidanshi saida ya tarasu tare da matayansa yana huci, Copy ɗin muhimman takaddunsa ya zazzage yana kallansu ɗaya bayan ɗaya yace "Ubanwa ya shiganmin Bedroom harya samu damar ɗibarmin kaf takadduna, wallahi tallahi kunji na rantse sai kun fitomin dashi inba haka ba ran kowa zayyi mummunan ɓaci"
Mahaifiyar Fahad taɓe baki tayi tace "Alhaji ka kira kowa na gidannan hatta matan baka ƙyalesu ba, amma saboda kai duk inda kake saika nuna halinka nason zuciya baka kira Fahad ba, waya sani shiya ɗauka yayi facakarsa dasu"
Wata irin harara ya maka mata daidai lokacin da Fahad yake ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa hannunsa ruƙe da makullin mota ga dukkan alamu fitama zayyi, ganin cincirundan mutane yasashi ɗan jan burki ya tsaya yana kallansu, "Mommmm" ya faɗa yana jan sunan yace "Me akeyi haka?"
Harara ta watsa masa tace "Kaima kazo kabi sahu, waya sanima kaine ka ɗauka aka wani taramu dan kawai a ci zarafinmu"
Ɗan waro manyan idanunsa yayi yace "Me kuma aka ɗauka?"
Ɗan tsaki taja sannan tace "Kadarorin mahaifinka mana"
Alhaji Bashir har ya buɗe baki zaice yi tafiyarka sai ji yayi yace "Au wai takaddun nan"
Gabaki ɗaya kallone ya dawo kanshi hatta Alhaji Bashir da hankalinsa ya tashi, cikin rawar murya yace "Yawwa Son ashe suna hannunka, maza jeka ɗaukomin su"
Ƴar dariya Fahad yayi, saiya tuno yadda sukai da Zuhra.
*_"Sweetheart ina tunanin takaddun daka bani zan baka ka maidawa da Daddy su kawai, saboda nasan idan har ka aureni zai baka aiki haɗe da maƙudan kuɗaɗe dan mu huta, karka damu zan baka su amma incase duk lokacin daya tambayeka takaddun suna ina kace masa suna hannun Muhammad Alee's family"_*
Ɗan murmushi yayi yace "Daddy ka kwantar da hankalinka, takaddunka suna nan lafiya ƙalau domin kuwa na danƙasu a hannun Muhammad Alee's Family...."
Bai gama magana ba sai ganin Alhaji Bashir akai a yashe a ƙasa tamkar wani matacce, gabaki ɗayansu hankalinsu ne ya tashi musamman Fahad ana faman jijjiga Alhaji Bashir.
Hankalin Fahad kuwa ba ƙaramin tashi yayi ba domin ko kaɗan bai kawo abunda yace bane mahaifinsa yana kwance a ƙasa, Baba mai gadi ne yace "Ku matsa in gani" ɗan jijjiga Alhaji Bashir yayi tare da tattaɓa wasu guraran na jikinsa, shiru yayi naɗan wani lokaci kafin ya ɗago da kai yace ......*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...