Page 30

229 22 1
                                    

Gabaki ɗayansu sun kasa taɓuka komai ko wannansu yana cikin farin ciki mara misltuwa, kwanciya sukai ko wanne na fuskantar ɗan uwansu, babu alamun bacci a idon ɗaya daga cikinsu, gashi lokaci yaja, "Faɗima" Muhammad ya kira sunanta, kallanshi tai da fararan idanunta ba tare datace Uffan ba, "Kinsan Mahaifin Fahad Allah yay masa rasuwa jiya da daddare amma yau akai jana'izar?"
  Shiru tai saika rantse da Allah tasan da maganar mutuwar alhalin koda wasa bataji labarin mutuwar ba sai yanzu, ganin yadda ko gezau batai ba bare jimami, ruƙo hannunta yayi yana wasa da zoben hannunta yace "Ko kin san da mutuwar ne?" ya ƙara jefo mata wata tambayar.
   Girgiza kai tayi alamun a'a, can kuma ta numfasa tace "Allah ya ƙara nauyin ƙasa..."
  Jin Muhammad yace "Subhanallahi" ne yasata dakatar da abunda take faɗa, kallanshi tai taga babu wani abu sai kafeta yayi da kyawawan idanunsa, "Faɗima musulmi ne fa, mai yasa bazaki bishi da kyakyawar addu'a ba?"
   "Yaya Musulmi fa kace?, yana aiki da musuluncine, musulmine zai ketawa matar aure haddi tare da faɗawa ƙananan yara ba tare da yardasu ba"
Runtse ido yayi yanajin babu daɗi cikin zuciyarsa, yasan maganar datake ta ahalinsu ce, ya ɗauki aƙalla minti uku sannan ya buɗesu akanta yayinda idanunsa har sun sauya kala daga farare zuwa launin brown.
   Ɗan matsowa tai kusa dashi jikinsu na gogan na juna, hannunta ta saka cikin lallausan gashin kanshi wanda ya gaji da gyara, a hankali take tafiyar da hannunta izuwa wuyansa, hura mai iska tai a fuska cikin salo na burgewa tace "Dan Allah karka tuna komi" ta faɗa itama muryarta na Cracking.
  Baice mata komi ba, saidai bakinsa yay nauyi idanunsa sai sauya kala suke yayinda ƙwayar idanunsa ta cika da ƙwalla saidai yanaso ya dake ya zama namijin gaske.
   Bakinta nakan nashi bakin a hankali tace "Please Yayana Be a Man, dan Allah"
Ta faɗa tana ƙoƙarin saka bakinta cikin nasa, a hankali ya zare jikinsa da nata tare da juya mata baya yana mai tuno Iyayanshi yanzu Bashir Iyan Tamane ya hallaka masa nashi zuri'a gashi shima har lokacinsa yayi ba tare daya jima a duniyar ba.
   Hawayan datake yaƙi dasune suka sauka akan kuncinta ganin ya juya mata baya, kuma ganin yanayinshi datayi ya tabbatar mata da yana cikin damuwa mai tsananin, share hawayan fuskarta tayi, tana kallan bayanshi, sosai tai ƙoƙarin Controlling kanta amma ta kasa, a hankali tace "Kayi haƙuri inna ɓata maka rai" daƙyar ta samu takai maganar tata ƙarshe jin yadda kuka ke ƙoƙari ƙwace mata.
  Muhammad jin muryarta haka yasashi ya waigo ba tare daya shirya ba, "Faɗima!"
Ya kira sunanta yana ƙoƙarin jingina da Bed ɗin tare da kamo kafaɗarta yana kallanta, "Mai ya faru?" ya tambayeta yanajin babu daɗi "Ba komi" ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace hannunsa daga kafaɗarsa, kwantawa tai itama ta juya mishi baya ba abunda take saukewa sai ajiyar zuciya.
   A hankali tace "Allah yay musu Rahama Ubangiji yabi musu hakkinsu"
   "Ameen" yace shima ya kwanta a bayanta tare da rungumeta tsam tamkar wacca akace mai za'a ƙwace masa ita, cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dasu, Asuba tagari masoyan asali.

"Bangane abunda kake nufi ba, a matsayinka na Commissioner of police ace baka da alfarmar da zaisa ka fitomib da Daddy na" Azmah ta faɗa ranta a matuƙar ɓace jin jawabinsa da yayi mata na cewar mahaifinta bazai taɓa fitowa a gidan yari ba har sai lokacin da aka ɗibar masa yayi.
   Cikin muryar lallama yace "Ba haka nake nufi ba Gimbiya sarautar mata, kinsan Case ɗin Daddynki ba ƙaramin Case bane, yanzu gwanda mutum yayi sata da ace anyiwa wata fyaɗe yanzu ƙungiyar masu fyaɗe tana da matuƙar ƙarfi a duniyarnan gabaki ɗaya ba a Nigeria ba, zaki sata a sakeki salin alin amma kinga Fyaɗe Case ɗinshi kafin ya mutu yana da matuƙar wuya"
   Turo baki gaba tai ranta sam babu daɗi tace "Wallahi bazan iya zama dakai ina biya maka duk wata buƙata takaba alhalin ni tawa buƙatar ƙaramar alhaki kaƙi ka biyamin ita, dan haka duk randa ka shirya biyamin buƙatata zaka iya kirana" miƙewa tai daga Office ɗin tare da ɗaukar Hand Bag ɗinta ta fita, shi kuma Gogan ba abunda yake sai faman ƙwala mata kira koda wasa bata juyo ba bare ya saka ran zata ansa mishi.
  Ganin ta tafine ya bushe da dariya yace "Allah ya raka taki gona, yanzu menene a jikin naki da mutum zaizo in banda surarki, domin ciki kuwa salam kike tamkar ruwa mai zartsi kunga kam ba daɗin sha zayyi ba" komawa yayi ya cigaba da aikinsa hankali kwance tare da hamdala sun rabu da ƴar anaci sunan daya saka mata kenan cikin ruwan sanyi da salama.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now