page 14

247 23 6
                                    

Zuhra kallanshi tayi tsaf fuskarta ɗauke da murmushi, duk da taso ace zuciyarta taƙishi fiye da yadda take zato amma sai ta samu akasin haka,bai burgeta ba kuma bai mata ba, sede kallan ƙwayar idonshi datayine ya haddasa mata wani sanyi cikin zuciyarta, kallanshi tayi dakyau tace "Malam Fahad kenan, yaudai Allah ya nufa mun haɗu da juna yanzu babu sauran wani ƙorafe-ƙorafe ko"
   Kana kallan fuskarsa basai ance maka yana cikin nishaɗi ba, kallanta yayi dakyau tare da gyra tsayuwarsa yace "Hakane kam, ina fatan za'a karɓeni hannu bibbiyu"
    Harararsa tayi ta gefen ido tace "So kake ƴan matanka suyi caa akaina ko, ai ina tunanik daga yau mun gama haɗuwa"
    Kallanta yayi da sexy eyes ɗinsa kasa cigaba tayi da kallanshi ganin irin kallan da yake jefanta dashi tamkar wani gagarumin ɗan bariki, gyara Veil ɗin jikinta tayi ganin yadda ya yaye ga kuma Bobs ɗinta sun ɗanyi sama ana gani, harara ta maka mishi tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa, wani irin sirirn tsaki taja tare da juyawa zatabar wajan, sauri yayi ya ruƙo hannunta jin wani irin shocking a hannunsa yayi maza zare hannunsa daga nata yana faman yarfe hannayansa, ɗan murmushi yayi ganin irin kallon data waigo tana mishi tace "Kai rashin haƙurin naka harya kai haka, daga haɗuwarmu yau shine zaka nemi ka nunamin kokai wanene, Alhamdulillah tun kafin aje ko ina ka fara nunamin asalin halinka" juyawa tayi ta fara tafiya ranta a ɓace, tabbas Fahad ya shahara kuma ya saba da taɓa macan daba muharramarsa ba.

Fahad yana tsaye sororo harya ga shigewarta gida, kama hannunsa yayi zai masa horo dan gani yake kamar shi ya ja masa wannan aika-aikan, naushin Motarsa yayi baisan lokacin daya saki wata ƙaramar ƙara ba "Ouchh" tare da kama hannun yana hurewa, ya daɗe a tsaye a ƙofar gidan sannan ya numfasa ya buɗe ƙofar baya Driver ya jashi suka tafi.

     Modibbo shida maƙarrabansa ne sukaje suka taro Ogan nasu, kana kallan yaran nasa zaka tabbatar da yau suna cikin farin ciki mara misiltuwa, Direct Area 10 suka nufa suka Tadda su Baffah har sun iso, yanayin anguwad tamkar G.R.A take saidai ba G R.A bane, anguwace wacca ta cika da bishiyoyin mangwaro, Ayaba, Guava, Gorubada sauransu, in damuna tayi ma har shukar Kankana zaka gani a wuraran, gashi akwai tazara mai ɗan tsawo tsakanin mutum da maƙocinshi, kusan gabaki ɗaya gidajan iri ɗayane saidai tsarin gidajan yayi matuƙar kyau da tsari yadda mai karatu baya tsammani, anan Muhammad Alee ya sauka, yayinda su Modibbo sukazo zuwa na musamman domin suyi murnar ganin Ogan nasu tare da yimai sannu da zuwa.
   Gabaki ɗayansu suna Babban Parlon gidan, kasancewa Parlour ne Babba sai3 bedrooms ko wani Bedroom akwai Toilet a cikinsa sai Dinning wanda yana da girma ba laifi sai Kitchen shima yana da girma, haka tsarin gidan yake, sai kuma Compound ɗin gidan daga nan shikenan, gidan yayi kyau sosai, duk wani abubuwan buƙatar rayuwa akwaisu a cikin gidannan.

   Muhammad Alee yana cikin ɗaya daga cikin Bedroom ɗin ɗakin yayinda Baffah ya jera masa kayansa cikin wardrobe dadai sauran abubuwan buƙata, fitowa yayi ƙugunsa ɗaure da Towel hannunsa kuma yana ruƙe da ɗan ƙaramin Towel yana goge sumar kanshi wacca tasha gyara take ƙyalli.
   Zama yayi a gefen Bed tare da sakin wata irin ajiyar zuciya, kana kallanshi basai ance maka a gajiye yake ba, bayan ya gama goge jikinsa ya nufa wajan Dressing Mirror ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya gama shafa mayukan nashi haɗe da fesa turaruka masu ƙamshin gaske da tsada, jallabiya kawia ya saka sannan ya nufa Parlour dan zuwa gunsu Modibbo duk da idan suna tare ba wai magana yake saka musu ba cikin hirarrakinsu amma ba ƙaramin jin daɗin kasancewa dasu yakeyi ba.
   Tun da ya nufo wajansu suke masa kirari a haka har ya samu waje ya zauna, ya ɗauki lokaci a ƙalla zaikai biyar sannan ya juyo ya kalli Modibbo yace "Ina fatan mun sameku lafiya?"
   Cike da girmamawa yace "Lafiya ƙalau ranka ya daɗe, labarin Fahad Kaji shiru ko...."
   Dakatar dashi yayi da hannunsa yace "Ba yanzu ba, ka bari sai an kwana biyu daga zuwanmu"
   Sosa ƙeya Modibbo yayi yace "Ina neman Afuwa ranka ya daɗe"
   Shirune ya biyo baya yayinda su kuma suka kunna kallo suna kallan ƙwallo suna hirarakinsu lokaci zuwa lokaci.
    Tashi yayi yace "Anan zaku kwana ko zaku wuce naku gidan?"
Baffah kallanshi yayi naɗan wani lokaci ganin yadda ya hango tarin damuwa a cikin ƙwayar idanunsa, kauda kanshi yagi ganin irin kallon da Baffah yayi masa,Buɗan bakin Baffah yace "Anan gabaki ɗaya zasu kwana"
   Ba tare daya ƙara ce musu Uffan ba ya shiga nashi Bedroom ɗin ya saka Key ya kwanta.

   Idanunsa na kallan sama tar yana tunanin Zuhra, ba abunda yake tunanowa sai kalmar nan da ake kira da rashin sani, akace yafi dare duhu, tabbas Zuhra na Kano domin jikinsa ya daɗe da bashi haka, saidai babu ta inda zai fada nemota yasan inyace ma zai nemoga to ba ƙaramin wahala zai ba kanshi ba, hannunsa ya saka a bedside drawer ya ɗauko wayarta, ya ɗauki lokaci mai tsayi yana kallan hoton screen ɗin wayarta, hannunsa ya saka akan wayar yana mai shafa fuskarta yanajin ba daɗi cikin zuciyarsa ko kaɗan, samu yayi ya kwanta duk da yunwar dayake fama da ita amma haka ya haƙuri saboda yanayin da yake ciki bazai iyacin abinci ba.

   Zuhra tunda ta koma gida taga ba kowa a Parlourn hakan ya nuna mata cewar kowa ya tafi ya kwanta kenan, ƙarasawa ɗakinta tayi itama ta kwanta tana tunanin meya kamata taiwa Fahad a rayuwarsa,  budget na farko data fara shine, dole zata saki jikinta dashi sannan ta saka mishi wata irin zazzafar soyayyarta wacca duk me tace masa zai iya aikatawa dan kawai ya sakata farin ciki, idan har hakan ta tabbata abunda yaka mata tayi shinr ta sakashi ya ɗauko mata duk wasu kadarori na Bashir Iyan Tama hatta Companys ɗin da yake taƙama dasu, da kuma wanda suka tarwatsa musu Familynsu saboda shi, bayan yayi mata haka sannna zata sakashi yayi bincike akan accounts ɗin mahaifinsa ya faɗa mata, ta hakane zata gane irin adadin yawan kuɗin Iyan Tama, idan har Allah ya nufa ta anshe kadarorinsa dukiyarsa ita kuma a lokacin zata fara yaƙar Fahad.
    Murmushi tayi tana karkaɗa ƙafarta hannunta ɗauke da Biro da Takadda, tuno ko waye Fahad da hatsarin dake gareshi yasata dole tayi taka tsantsan wajan karya saba taɓa mata jiki, dole zata ja mishi kunne akan karya sake kuma karya kuskura.
    Ɗaukar wayarta tayi a kunne ganin tunda ta shigo gida yake faman danna mata kira kasancewar wayar tana Silent, bayan ta ɗauki wayarne tayi shiru tana sauraransa.

    Fahad sallama yayi mata amma tayi shiru abunda bai taɓa yiba koda wasa yayiwa mutum sallama, ƙara nanata sallamar yayi duk da akwai wasu haruffan da bai faɗa daidai ba amma yayi ƙoƙarin a matsayinsa wanda bai sallama a duk inda yaje, daga Hi sai Hello Guys wannan ɗabi'ar tana ɗaya daga cikin ɗabi'unsa wanda sukai mishi mugun kamu, ganin yayi sallama har sau uku bata amsa ba yasashi ƙara sassauta muryarsa yace "Dan Allah kiyi haƙuri, wallahi bansan lokacin da Shaiɗan yayi galaba akaina ba, nayi ƙoƙarin yin Controlling ɗin kaina amma na kasa, Please Zuhra Forgive me wallahi sonki ne yakaini ga aikata haka"
   Shiru yayi yana jiran amsa daga gareta, dan tabbas fushin datai dashi ba ƙaramin tashin hankali ya sakashi ba, ya kasa sukuni har zuwa yanzu da yake bata haƙuri, domin kuwa bada haƙuri ba ɗabi'ar Fahad bace, ko waye zaima laifi a duniyar nan bai isa ya bashi haƙuri ba koda kuwa mahaifinshi ne ko mahaifiyarsa, shi kanshi ba ƙaramin mamakin kanshi yakeyi ba akan Zuhra ganin yanaso ya zama Useless a wajanta.
   Cikin sanyin murya ya ƙara cewa "Please My Princess"
     Numfasawa tayi tace "Okay naji, but promise me bazaka kuma ba"
Voice ɗinsa na rawa yace "I Promise you"
Sautin murmushinta ya jiyo ta cikin wayar shima saiya tsinta kanshi dayin murmushi, alhalin Fahad baisan damuwar kowa ba inba tashi ba haka zalika baisan farin cikin kowa ba in ba nashi ba, amma yau ya kasance yana maijin daɗi cikin zuciyarsa don yaji Zuhra tana cikin farin ciki.
   Zuhra sakin jikinta tayi dashi sosai suka sha soyayya, Fahad Bashi ya barta ba har saida yaji tayi shiru alamun tayi bacci sannan ya katse wayan.
   Tashi yayi yana maijin daɗi cikin zuciyarsa ya buɗe Fridge harya ɗauko kwalbar Wine ya maidata yana murmushi yace "Inaso muryata ta dawo kamar yadda take da, koni banajin daɗin muryar bare kuma Zuhra duk da nasan daurewa kawai takeyi" maidawa yayi ya ɗauko Normal ruwa yasha ya kwanta ba tare da yayiwa kanshi addu'a ba.

   Mahammad Alee ganin har rana ta fito yasashi tashi da sauri yana  zai fita zuwa wani gun,a gurguje ya kammala komai ya kurɓa ruwan Tea ɗin Da Baffah ya haɗa masa sannan ya kallesa yace "Ko zakazo muje"
  Baffah cikin hanzari yace "Bari nazo" dan haka kawai Allah ya haɗa jinin Baffah Da Muhammad Alee tun yana a matsayin me gadi a gidansu haka Muhammad Alee yake baro Part ɗinsa yazo ya zauna a kujerar da yake zaune koda bazasuyi hira ba, kuma duk wani abun alkhairi idan zayyi na marasa ƙarfi shi  yake faramawa shi, ta hakane ya gina soyayyarshi a zuciyar Baffah yake masa son tsakani da Allah, dan ko kaɗan bayaso a cutar dashi duk da shekarun nasu bazai wuce ɗaya ba.

A gurguje Baffah ya fito dan kar ya gaji da jiranshi ya tafi ya barshi, "Muje ko" yace masa ya juya ya fara tafiya, Muhammad Alee yace masa "Makullayan gidanan na kusa mu biya tacan"
   Shiru Baffah yayi yace "Gaskiya na ɓoyesu saidai ka jira na ɗauko inhar ba sauri kake ba"
  Tafiya ya farayi yace "Muje kawai, next time maje kawai"
  Binshi yayi a baya ya buɗe masa motabya shiga shima ya zaga ya shiga ya jasu suka bar anguwar.

*More Comments more typings*

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now