Da kallo tabi motar ba tare datai aune ba taji wasu irin zafafan hawaye suna sauka akan kuncinta, kakkaɓe Veil ɗin jikinta tayi ganin yadda suka baɗa mata ƙura, ƙara kallan gidansu Zuhra tayi tana mamakin yaushe suka tashi, hannu ta saka ta share hawayanta murmushi yayi nasarar suɓuce mata tace "Kun ɗauki fansar taku gun mahaifina hakan yasa kukayi gaba abunku" matsawa tayi gefen wani gida ta zauna tana tunanin tayaya zata koma gida gashi ta baro wayarta a gida gashi ba kuɗi a hannunta, tazararsu da gidansu Zuhra akwai nisa ba ƴar kaɗan ba, haka ta numfasa tana tunanin a ina zata samu waya don ta kira gida.
Sun ɗanyi nisa kaɗan Muhammad Alee yace "Dakata"
Ba musu yaja burki ya tsaya, fitowa yayi daga cikin motar ya jingina da ita yanajin iskar wajan na mishi zafi saboda halin da yake ciki a yanzu, ba abunda yake tunani sai Zuhransa, "tana ina?" shine tambayar da yayiwa kanshi ba amsa, tsayawa yayi yana lissafi a cikin ƙwaƙwalwarsa, yasan duk inda Zuhra take to tabbas tana tare da Iyayanta ne, jin labarin daya afku da Abdul-Jabbar ya tabbatar masa da Zuhra ɗaukar fansa tazoyi Kaduna, ba inda tunaninsa ya dosa sai yanzu Haka suna Kano don ɗaukar fansarsu wajan Alhaji Bashir Iyan Tama, ɗan murmusawa yayi yanajin sanyi a cikin ransa koba komai yana kyautata zatonsa na haɗuwa da Faɗimarsa duk da yasan garin Kano akwai faɗi da tsawo amma hakan baisa ya karaya ba.Bayan sun gama breakfast ne Zuhra ta tashi ta zauna gabda mahaifiyarta tace "Mommy!"
Hankalin mahaifiyarta tace ya dawo kanta tace "Inajinki menene"
Shiru tayi naɗan wani lokaci sanna tace "Ya Sani wai yana raye"
Ta faɗa tana jiran amsa gun mahaifiyarta.
Mamanta murmushi tayi na ɗan wani lokaci tace "Yaro-yarone, kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo Zuhra?, wai yaushe zaki dawo hayyacinki ne, ina shawartarki da tun wuri wallahi ki cire Sani a ranki tun kafin lokaci ya ƙure miki, kece mafarkinsa kece kullum kinga mai kama dashi ni na tabbata da yana raye da zamu sani Zuhra"
Shiru tayi ba tare datace komi ba, ta ɗauki lokaci mai tsayi sannan tace "Mommy wallahi yana raye bai mutu ba na ganshi kuma shine yayi kidnapping ɗin Azmah"
Dariyar rainin hankali tayi mata tace "Zuhra kenan, kece zaki ga Saninki ban ganku tare ba" ta faɗa tana dariya, domin ita maganar Zuhra ta maida ita shirmene, harta miƙe ta nufa Kitchen ta tsinkayi muryar Zuhra tana cewa "Yanzu ya batun aurena dashi har yanzu yana nan ko sai an gyarashi" ta faɗa fuskarta sam babu alamun wasa.
Mahaifiyarta kallanta tayi na ɗan wani lokaci sannna ta kaɗa kai ta shiga Kitchen ɗin tana mai mamakin furucinta na ƙarshe, tabbas sai an nema mata magani ganin yanzu abun nata ya dawo da har tana murna ta dawo daidai ashe ya tafine kuma yanzu ya dawo.Zuhra tashi itama tayi jiki ba ƙwari ta shiga Bedroom ɗinta, wayar data kashe saboda Fahad ta kunnata yanzu, sokata tayi a caji ta kwanta tana hango lokacin da yake kallanta itama haka, tabbas jikinta ya bata Ya Saninta ne, saidai har yanzu tana mamakin menene ya sakashi harkar Kidnapping, tuno labarin data karanta a BBC ya tabbatar mata da cewar shima fansa yazo ya ɗauka gun Azmah, rungume Pillow tayi tare da runtse ido tana addu'ar Allah ya haɗata dashi tabbas ranar dataiwa Allah godiya mara iyaka.
Wayarta ne ya fara ruri tasan ko ba'a faɗa mata ba Fahad ne domin kuwa shi kaɗai yake da numbernta Sim ɗin nashine na musamman, saida yayi mata missed calls biyu sannan ta ɗauki wayar, wata irin ajiyar zuciya Fahad ya sauke tare da numfasawa, cikin sanyin murya yace "Niko wani irin laifi nayi har haka da za'a hukuntani, kin kashe wayarki koda wasa idan na kira bana samunki so kike ki haukatar dani"
Hararar wayar tayi ba tare datace komai ba, Fahad yace "Me yayi zafi haka, dan Allah kiyi haƙuri gimbiya sarautar mata"
"Ya kake?" shine abunda Zuhra tace masa, lumshe ido yayi tamkar yana ganinta yace "Ina lafiya, bana samunki a waya"
Yatsina fuska tayi tace "Yanzu ai ka sameni ko?"
Tamkar soko yace "Eh, ya Kaduna?"
"Kano dai zakacemin, dan jiya na sauka a cikinta"
Fahad tashi yayi daga kwancan da yakeyi yace "Are you sure?" ya faɗa fuskarsa ɗauke da tsantsan farin ciki.
"Zan maka ƙarya kenan?" cewar Zuhra.
Ƴar dariya yayi yace "Nina isa, a Kano kina wani gun ne?"
"No bansan anguwar ba wallahi ka bari idan na tambaya zan sanar dakai"
Cike da zumuɗi Fahad yace "Please ki tambaya mana yanzu"
Zuhra tace "Okay, let me come"
Katse kiran tayi tare da kashe wayar gabaki ɗaya ta lumshe idanu, lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba da ita.Baffah suna tafiya yace "Yanzu a ina zamu sauka idan munje Kanon kaga mun kusan zuwa"
Hankalinshi naga Titi yace "Da nace zamu sauka a gidan Dad ɗina wanda suka gina shida Uncle but banso na zauna a gidan kasan gidan nada girma mu kama Hotel kawai tunda ba daɗewa zamuyi ba"
Baffaj yace "Baka tunanin kosu Zuhra suna can a zaune suma?"
Shiru yayi naɗan wani lokaci sannan yace "Bana tunanin haka Baffah saboda baza suso Alhaji Bashir yaji labarin suna gidan ba dan na tabbata ya baza mutanansa akan su runƙa lura da gidajan, saidai ina zaton kamar yadda suka ɓadda kama a Kaduna haka nake kyautata zaton zasu ɓadda kama anan garin Kano"
Rausayar da kai Baffah yayi ya cigaba da tuƙinsa, ba tare da sun ƙara yiwa juna magana ba.Tsaf Fahad ya gane kwatancan da Zuhra yayi masa, kana kallansa zaka tabbatar da cewar yana cikin farin ciki mara misltuwa, wankan kece raini ya ɗauka tare da kalle kanshi tsaf ko akwai wani abu daya kwafsa ya gyara, da murmushi ya fito yau isar da yakeyi a gidan nasu ma bayyi ba, Security ɗinsa guda ɗaya ya kira suka kama hanyar tafiya ko part ɗin mahaifiyarsa bai shiga ba suka tafi.
Wannan ne karo na farko da Fahad zai tunkari mace yaju gabanshi ya faɗi abunda bai taɓa ba a tsahon rayuwarsa, lumshe ido yayi jin yadda zuciyarsa take harbawa, a daidai ƙofar gidansu Zuhra sukai Parking, wayarsa ya ɗauko ya danna mata kira saida ta kusan katsewa sannan ta ɗauka, nan ya shaida mata da yana ƙofar gidan, ba tare data bashi amsa ba ta kashe wayar.Kallan mahaifinta tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "Dad zan fita waje, Fahad ne yazo"
A ɗan tsorace ya kalleta yace "Mai yasa baki faɗamin ba kafin ki aikawatar da hakan, kinsan sanar dashi wannan gidan gab yake da tarwatsa Plan ɗinmu"
Kallanshi tayi sai kuma tayi shiru, tace "Kayi haƙuri na ƙosa na fara aiwatar da abunda ya kawomune shiyasa ba kasa haƙura da sai mun ɗauki lokaci kafin mu fara tunkararsa"
Kallanta yayi fuskarsa sam babu alamun fara'a yace "Ai matsalar Bashir yasan wannan gidan namune, ke a tunaninki duk randa ya tabbatar da cewar wasu na cikin gidannan bazaiyi ƙwaƙwƙwaran bincike akan hakan ba"
Shiru tayi can kuma ta numfasa tace "Daddy bazaiyi tunanin haka ba, domin sunji, sun karanta kuma sun tabbatar da ahalin Muhammad Alee sun rasu ta sanadiyyar harin da ƴan bindiga daɗi suka aiwatar, kawai zayyi tunanin wanine ya murɗe gidan amma ina kyautata zato bazai taɓa kawowa mune a ciki ba insha Allahu"
"Hmmm" kawai yae tare da ce mata "Ki kula sosai, sannan ki tabbatar kin kare mutuncinki, Fahad yana da matuƙar hatsari yadda bakya tsammani"
Cike da ladabi tace "Insha Allahu Daddy zan kiyaye" Veil ɗinta ta saka sannan ta nufa ƙofar gida tanaso yau idonta ya gane maga Fahad Iyan Tama.
Fahad ba inda ya ƙurawa ido sai Get ɗin gidansu Zuhra, ganin ta fito baisan lokacin daya furta kalmar "Woww" ba, yayi karatu a Abroad haka zalika yayi ƴan mata kala-kala, iri-iri amma babu wacca ta taɓa tafiya da zuciyarsa farat ɗaya ba irin Zuhra, wani irin zazzafar soyayyarta ce tayi tasiri cikin zuciyarsa, wata iri tsaftacacciyar soyayya yake kwadayin suyi shida ita, tunda ta taho idanunsa na kanshi yayinda ita kuma ta duƙar da kanta ko kaɗan bataso tayi tozali da fuskarsa dan ba ƙaramin tsanarsa tayi ba, in bazata manta ba kalmar Yayarta ta ƙarshe itace akan Fahad, tana kyautata zaton shine ya aikata fyaɗe akanta ba kowa ba, duk da taso faɗa mata abunda Fahad ɗin yayi mata amma ta kasa amma tabbas da sunanshi tabar duniyar nan lokacin da harshashi yayi nasarar samunta a ciki, idanunta ne suka sauya launi, koda wasa bataso ta kalli Fahad amma babu yadda ta iya, dolene ta ɓoye tsanar da take mishi kar ya gane.Da sallama ta isa wajan, Fahad amsawa yayi idanunsa na yawo a jikinta dan ko kaɗan bayaso ya gifta idanunsa akanta dan bayaso daya gifta yaga ya tashi daga nannauyan Baccin da yakeyi.
Gaishe dashi tayi cikin natsuwa, amsawa yayi tare da nuna mata mota akan su shiga daga ciki, girgiza kanta tayi tanaso ta haɗa ido dashi amma tana tsoron kar ya hango tsantsan tsanar datake masa, a hankali taɗan ɗaga idanunta ta kalleshi saita maida kanta ƙasa, batai tsammani haka Fahad yake ba, to tabbas jinshi yafi ganinshi, dan muryarsace mara daɗi amma a zahiri Fahad yana da kyau daidai gwargwado saidai bazaka taɓa haɗashi da Muhammad Alee ba,saidai Fahad babu wanda zai kirashi da mummuna yana da kyanshi daidai shi, sai Dimples ɗinshi da suka ƙara bayyana kyanshi gefe da gefe ko murmushi yayi sai sun lotsa sosai, ba sede muryarsa ce ta kwafsa ta yadda ta canza tamkar ta manyan mutane giyar daya maidata tamkar ruwa itace ta buɗe mai murya, sede yanzu tunda yayi tozali da Zuhra yake ƙoƙarin ɓoye komai na ɓatancin dayake aikatawa.Kuyi maneji
More comments more typings*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...