Page 26

288 18 10
                                    

Fahad yace "Miliyan Uku kuma haba kuɗin yayi yawa, ku kunsan irin iftila'in daya afka ma mahaifina tayaya zakuce in baku 3 millions, ni wallahi ko miliyan ɗaya bazan iya bayarwa ba" yafaɗa yana faman huro hanci yana huci tamkar zai dukesu.
   Ogan nasu murmushi kawai yayi sannan ya canza fuska ta koma irinta asalin ruƙaƙƙun ƴan daba yace "Bar wajannan kafin mu canza maka halitta, an faɗa maka a banza muke ɗaukan ra mutane dame zamuji, da zunubin da muka ɗibarma kanmu koko da matsiyatan kuɗinka, to wallahi tallahu kaji na rantse a 3 millions ba abunda zamu rage in hakan yayi maka shikenan, dan haka bar nan" yafaɗa yana ƙoƙarin zaro wuƙa daga jikinsa.
    Matsawa Fahad yayi har ya isa gun motarsa, kallan ƙasƙanci yayi musu sannan ya shiga motarsa ya figeta da ƙarfi tare da tsirta musu yawu.
  Da gudu yaran suka bishi, yayinda ya ƙurewa motarsa gudu yabar anguwar yana maida numfashi.

   Kwanaki sun ja yayinda tunda abunnan ya faru tsakanin Zuhra Da Muhammad Alee basu ƙara yunƙurin haɗuwa da junansu ba, duk da har yanzu gyara musu gidan ake saboda gyarane ba karami ba, sa'ilin da Muhammad ya samu Daddy akan maganar yanaso ya fara sana'a nan ya bashi shawarar ya buɗe tafkeken Plaza wanda za'a zuba duk wani abubuwan mora rayuwa, nan suka bazama nemo tanfatsetsen Fili aka zuba ma'aikata dan fara gawurtaccan shago anguwa guda, hakan yasa gabaki ɗaya hankalin Muhammad ya karkata kan aikin da ake masa duk da yasan yayi matuƙar kewar abar ƙaunar tasa.
   Yau Asabar yayinda gidan yayi tsit kowa yana ɗaki ba wanda ya fito, Zuhra ba abunda take a ɗaki sai faman yin juyi tabbas tayi Missing ɗin Ya Saninta, tai Missing ɗin duk wani abubuwa nashi, tanaso ta ganshi saidai bazata iyaba tunda shi bai nemi hakan ba, hawayene suka sauko mata a kuncinta ganin tun lokacin daya samu abunda yakeso bai ƙarabin takanta ba, saidai ya kirata a waya shima baya Minti biyu yake kashewa dayaji tana nan lafiya, ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara share hawayan Fuskarta, tana data sani da bata bashi haɗin kanta ba gashinan ya kaita ya barota.
   Jin Knocking ɗin ƙofarta yasata saurin goge hawayan fuskarta tare da faɗin "Ina zuwa"
   Tashi tayi jikinta a sanyaye ta nufa ƙofar ta buɗe, ganin Ya Saninta yasata ɗan zaro ido tana mamakin tayaya ya shigo part ɗinsu yau, sauri yayi ya shigo tare da sakawa ƙofar key, kallanta yayi ganin duk yanayinta ya canza mai, fuskarta kadaran kadahan, babu alamun tai murnan ganinsa, ɗan jingina yayi da jikin ƙofar hannayansa rungume a ƙirjinsa yana ƙare mata kallo, ganin ta juya masa baya ba tare data ce uffan ba, takowa yayi yazo har gabanta tare da juyo da ita gabanshi yace "Nai miki laifi ko?, ko baki faɗamin ba nasan nai miki laifi saidai ina neman afuwarki da kiyi haƙuri abubuwane suka sha kaina lokaci ɗaya, ina gina mana hanyar da zamu ɓulle ne keda ƴaƴan da zaki haifamin nan gaba" bakinsa yakai saitin kunnanta yace "Am Very Sorry"
  Ajiyar zuciya kawai ta saki ta ɗan matsar da jikinta gefe ta samu gefen Bed ɗinta ta zauna, cikin sanyin murya tace "Ina Wuni?"
  Kafeta yayi da fararan idanunsa sannan ya ɗago da haɓarta, yana ƙare mata kallo, ganin yadda ƙwalla ta taru a idanunta yasashi cewa "Nai miki laifine?"
Ya faɗa cikin sanyin murya haɗe da matuƙar kewarta, lumshe ido tayi saiga hawaye sun sauko daga idanunta, muryarta na Cracking tace "Ya Sani ni gani nake kamar baka sona"
  Wani irin murmushine ya suɓuce masa wanda ya ƙara yiwa fuskarsa kyau matuƙa yace "Duk wanda ya faɗa miki hakan yayi miki ƙaryane kawai..."
Katseshi tayi da cewar "Ba wanda ya faɗamin hakan zuciyatane ta shaidamin haka, saboda tunda ka samu abunda kakeso a jikina baka ƙara bin takaina ba" ta faɗa wasu hawayan na ƙoƙarin saukowa.
Numfasawa yayi yace "Zuciyarki ta daina faɗa miki ƙarya da Gaibu dan Allah, domin ni Sani ke nakeso ba komi naki ba, karki manta tun kafin ki mallaki abubuwan da kike faɗa nake ƙaunarki, amma mai yasa zuciyarki zatai saurin yanke wannan hukuncin haka?"
   "Hmm yanzu baka kulani kamar da, baka faɗamin kalaman da kake faɗamin gani nake kamar ma bataini kake ba alhalin kasan bawai na cika lafiya bane"
   Ajiyar zuciya ya sauke tare da harɗe hannayansa yana kallanta, cikin sanyin muryarsa yace "Kefa nakewa komi a duniyar nan, ina miki tanajin da zakuji daɗin rayuwarku ne keda ƴaƴan da zaki haifamin nan gaba wataƙil nai tsahon rai wataƙil na tafi na barku danme yasa bazan muku abunda zaku daɗe kuna nema ba ba tare da kun tagayyara ba, wallahi Faɗima tunda Allah ya halicceni zan iya cewa bayan iyayena a duniyar nan wallahi babu wacca nake ƙauna sama dake, banason komi naki sai ke ni ke nake so, tayayq zan shigo cikin gidannan alhalin ina da tabbacin suna zargin danai miki aika-aika, wallahi Faɗima ina tsananin jin kunyarsu Daddy da Mommy shiyasa na kasa taɓuka komai game dake, yau ma saida naga fitarsu anguwa yasa na shigo don naga lafiyarki, tayaya zaki gane ban baki kulawa ba alhalin munyi nesa da juna, inaso ki sani Ina matuƙar ƙaunarki a rayuwata, bana fatan ki rugani barin duniya domin wallahil azim bansan ina zan saka kaina ba, ni jikina ya bani danke kawai aka halicceni, dan Allah ki runƙamin kyakykyawar fahimta"
   Goge hawayan fuskarta tayi dan tabbas ta yadda da kalamansa domin kuwa ƙwayar idanunsa ta tabbatar mata da hakan, sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace "Kayi haƙuri nai maka bahaguwar fahimta"
     Hannunta ya ruƙo yace "Ko kaɗan banyi fushi ba saidai inaso ki runƙamin uzuri kinsan bama tare bare ki gane yanayin Yayan naki"
  "Uhmm" kawai tace tana lumshe ido jin laɓɓansa kam wuyanta, yayinda wata irin sha'awarsa ke addabarta a kwana biyunnan, saitin kunnanta yaje cikin whisper Voice yace "Ya jikin naki?"
  Kasa magana tai jin yadda yake ƙoƙarin mantar da ita daga duniyar datake, ɗan kallanta yayu ganin yadda ta runtse idanunta gam tana faman sauke ajiyar zuciya kaɗan-kaɗan, sunanta ya kira a hankali ta buɗe idanunta da suka sauya kala ta kalleshi, "yaushe zakizo Part ɗina?" ya tambayeta yana ƙoƙarin danne abunda yakeji shima.
   Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ni Banso Mommy tace banda ajine, hakan yasa nakejin tsoron zuwa inda kake"
  Maganarta ba ƙaramin dariya ta bashi ba, murmusawa kawai yayi yace "Haka kike gani?"
Ɗan tuno mai baki tayi tace "Hakane ma, tace na jira na tare mana saurin me muke"
   Murmushi kawai yake mata yace "Haka Mommyn tace?"
  Ɗaga mishi kai kawai tayi, janyo da ita jikinsa yayi yace "Nikam tunda yanzu babu ranar tarewa Mommy dole tai haƙuri damu, ko kuma su barmin ke ki koma Part ɗina, kinsan maiya faru?" ya faɗa yana kallan Lips ɗinta datake faman cijesu, girgiza kai tayi yace "Uhm bazaki gane ba, na ɗauka na nemawa kaina mafitane ashe kamar tsokano ciwon daya daɗe yana addabata nayi, yanzu ki manta da maganar Mommy, ki ɗauka zatai miki yaran mutanan Daa ne ki saki jikinki da Mijinki Allah ya baki lada mai ɗunbin yawa, ni kuma zan biki yadda kikeso"
  Kallanshi tayi naɗan wani lokaci tamkar mai tunanin wani abu,tace " Yanzu idansu Mommy sun dawo fa?" ta faɗa tana ɗan guntse dariya.
   Shima dariya yayi yace "Tunda haka kike tunani bari na baki abunda kike buƙata sai in tafi kar Mommy tai miki buƙulu"
  Maganar tasa dariya ta bata tace "Kodai kake da buƙata"
"Hmm" kawai yace yayinda ya fara mantar da ita a duniyar datake saidai ba ƙaramin jin daɗin yadda yake Romance ɗinta take jiba, ji take ba wata sai ita.

   Azmah kallan Fahad tayi tace "Haka sukace maka?, to mai yasa bazaka basu kuɗin da suke da buƙata ba, na faɗa maka karsu kashemin shi kawai su ɓatar dashi daga Kano inyaso saisu nuna mana inda suka kaishi, dan Allah kar a raunanashi sosai" ta faɗa tamkar zatai kuka.
  Shafa ƙeyarsa Fahad yayi yana sakin wani irin malalacin murmushi shi mahaukacine zai bar Muhammad a doron ƙasarnan, kenan burinsa bazai taɓa cikaba akan Zuhra.
  Murmusawa yayi tare da saka hannayasa cikin aljihu duno da Joseph da yayi cikin yaran Muhammad yasashi kara murmusawa tabbas kisan mummuƙai zasuyi masa ba tare da kowa yasan su bane, tunda Joseph yana tare dashi kasheshi bazai musu wahala ba.
   Kallan Azmah yayi a gefensa, don tunda aka tabbatar masa da Zuhra mallakin wanine bashi ba hakan yasa Fahad komawa ruwa tsundum akan abunda yakeyi ada yanzu kuwa ya ninka fiye da yadda mai karatu baya tsammani, yayinda yayi nasarar samun Azmah a cikakkiyar budurwa ya keta mata haddi tare da yardarta, hakan yasa ya sabar mata da duk wani launi na Sex har Azmah ta zama ƙwaruwar kanta, saidai Allah ya halitta mata wani kishi wanda ita kanta batasan tana dashi ba sai da taga Fahad da ƙanwarsa suna wasa da dariya hakan yasata jin wani irn baƙin ciki tamkar ta shaƙi wuyanta ta mutu ta huta, ga shi Fahad bai samu Azmah ba saida shima ya tabbatar mata da bai taɓa sanin wata ɗiya mace ba a rayuwarsa hakan yasa ta yadda dashi, saidai tun a daransu na farko ta fara zargin kamar ba wannan bane abu na farko daya fara sanin mace ba saboda yanayin yadda yabi da ita, saidai tuni ta manta da hakan daga zuciyarta, saidai har yanzu batasan Fahad ƙwaro bane ta fannin harƙalla da mata, hakan yasa Fahad yin takatsantsan akan karta ganeshi kafin lokacin sauya rigarsa yayi yay watsi da ita.

   Tana manne a jikinsa tana ƙara jaddada masa kar a kashe Muhammad ɗinta, Fahad jinta kawai yake dan yayi imani bazai taɓa samun Zuhra a matsayin matarsa ba inhar Muhammad Alee na raye, tuni ya gama ayyana mugun nufin da zasuyiwa Muhammad Alee.

*#Comments*
*#Subscribes Mum Irfaan TV Channel*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now