*Assalamu Alaikum, ina muku albishir da maganin sanyi wato infection idan zaku siya maganine me kyau kuma mai ingancine, sahihin maganin sanyi wanda inhar akwaishi a jikinki da yardar Allah zai miki magani cikin lokaci kanƙani,matan aure sunasha, ƴan mata suna sha, haka zalika yaran da suke fama da matsalar sanyi suma zaku iya basu, maza suna sha, gaskiya ɗaya zan iya faɗa muku shine maganin nada kyau, karku tsaya sanya maza garzayo wajan Mum Irfaan domin siyan maganin sanyinki a hannu, siyan ɗaya zakiyi koko sara zaki duk akwaishi, sannan akwai man gashi na al'arabee mai saka tsahon gashi, tsayin gashi, taushin gashi, cikar gashi uwa uba yana maganin dandruff me kike jira ƴar uwa maza tuntuɓi Mum Irfaan domin siyan ingantattatn maganin sanyinki haɗe da Man kitso da sauran abubuwan gyaran jiki, in kina da buƙata zaki iya tuntubata ta wannan numbern 08130515037 plz idan baki shirya ba karkimin magana mu ɓatawa juna lokaci*
Ta ɗauki lokaci mai tsayi saiga wani yazo gabda ita tamkar yasan itace wacca zata basu kuɗin fansar, a ɗan razane ta kalleshi sannan ta kawar da kanta gefe dan bataso ta ƙara tozali dashi sam bashi da fuskar masu imani, cikin murya irin ta bada umarni yace "Ki biyoni" juyawa yayi ya fara kutsa kanshi cikin wani daji, yayinda ita kuma ta tsaya cak ta kasa koda motsi tana ƙarewa inda zasu dosa ganin ko alamun gida bata gani ba, duk da yanzu haka tana bakin Titi tana ganin shawagin mutane, wani irin kallo ya jefeta dashi lokacin daya waigo yaga bata biyosa ba, tamkar an angizata haka tabi bayanshi bakinta ɗauke da addu'a tana mamakin wai mutanene ke rayuwa cikin wannan gurin da zasu nufa, tafiya kawai sukeyi har ƙafar Zuhrs ta fara gajiya tare data sanim bata biyosa, gani take kawai zai cutar da itane amma bazai kaita ga Azmarta ba, ɗingisa ƙafa tahauyi ganin yadda yau ake ƙwalla Rana ba ƴar kaɗan ba, tsayawa tayi ta kasa koda motsi dan a halin datake ciki ba inda zata iya takawa ba saboda azabar da takeji a ƙafarta, lumshe ido kawai tayi tanajin zafin rana har tsakiyar kanta, daƙyar ta samu takai kanta wurin wata bishiya ta zauna a ƙasa daɓas ba tare data duba ƙasan ba saboda yanayin datake ciki.
Juyowa yayi ya ganta fuskarnan tasa tamkar bai taɓa dariya ba ga wani uban suma data mamaye mai fuska, cikin tsawa yace "Bazaki zo mu tafi ba" ya faɗa yana mai ƙarewa halittarta komai ganin komai yaji, da yana ganin Azmah a cikakkiyar mace ganin Zuhra yasashi mantawa da Azmah don kuwa yaga wacca ta fita komai da komai.
Kallanshi tayi cike da gajiya a tattare da ita ta miƙa masa Bag ɗin dake hannunta tace "Gashi, ku duba ku gani za kuga 1 billion ne, ni bazan iya ƙarasawa ba ƙafana ciwo yakemin bazan iya wata tafiyar ba a halin yanzu..."
Bai bari ta ƙarasa ba ya nufota cike da zafin nama yana ƙoƙarin kifa mata mari, warning ɗin da akai maaa ya tuno lokacin da aka turosa wajanta, maida hannun nasa yayi yana faman yin huci tare da maka mata harara tamkar ƙananun idanun nasa zasu faɗo ƙasa, jan jakar yayi har yaso ya haɗa da hannunta yabar wajan duk da tana hango wata Bukka acan nesa da ita hakan na nufin sun kusan zuwa kenan duk da akwai tazara ba ƴad kaɗan ba tsakaninta da wa ƴannan Bukkokin, ganin ya ɗanyi nisa yasata numfasawa tare da gyara zamanta tana kalle Dajin kar wani abu yazo ya cutar da ita, murmushin gefen baki tayi tace "Haka kawai naje su ruƙeni ko kuma suce bazasu sakemu ba mu duka biyun meta kaini, ai wallahi daganan idan na motsa to gida zanje ko ubanwa zaizo kuwa" tana zaune tana hangoshi har taga yayi nesa da ita sosai, ita kam fuskarta ɗaukr da yalwataccan murmushi, wasa ta farayi da zoben dake maƙale a hannunta wanda ya ƙara bayyana kyan yatsunta, ba abunda take tunawa dashi sai mijinta abun alfaharinta kuma ɗan uwa a gareta wanda bata iya tunanin zata bawa wani ɗa namiji gurbi cikin zuciyarta har abada, dashi ta fara a rayuwarta lokaci ƙanƙani aka rabata dashi daidai lokacin da suke tsananin buƙatar junansu runtse idanunta tayi saiga wasu zafafan hawaye na zuba daga idanunta, tunowa da ahalinta da kuma yar uwarta jinin jikinta wacca take matuƙar ƙauna, share hawayanta tayi tana sauke wata irin ajiyar zuciya maiban tausayi ga duk wanda ya kalleta a halin datake ciki yanzu, kallan mutumin tayi taga saura ƙiris ya ƙarasa wannan Bukkar, saka kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tare da ciro zoben ta damƙesa a hannunta tana tuna abubuwa da dama.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...