page 17

268 25 6
                                    

Zuhra tana tsaye tamkar gunki tana kallan tafiyar Ya Saninta, tamkar mutum mutumi haka ta koma saboda tsananin tsoro da tashin hankali, ita gani take anya ba gizo yayi mata ba kamar yadda yake mata ada ba, har yanzu idanunta yana kan hanyar da suka tafi ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana jij duniyar tai mata zafi, ta kasa yadda yaya abun Ya Saninta ta gani kuma ya ganta ya tafi ya barta, har yanzu ta kasa yadda shine, wata irin tsohuwar soyayyarsa ce ta taso mata daga zuciya tanajin kanta inhar babushi a yanzu haka to tabbas itama mutuwa zatai, ɗaga ƙafarta tayi taji ta mata nauyi ƙirjinta rungume da Files ɗin da Fahad ya bata, sam batajin daɗi a jikinta.
    A hankali ta fara tafiya tamkar mara laka a jiki, jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba ganin irin kallon daya watsa mata, bata taɓa tsammanin haka daga gareshi ba, ita a ganinta yadda suka shafe sama da shekara suna neman juna cancanta yayi ace ganinta da yayi ya shiga farin ciki mara misltuwa.
   Idanunta ne taga suna ganin duhu-duhu kamar wacca yana ta maƙale mata a idanu, ba abunda zuciyar Zuhra takeyi sai faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, saura kaɗan ta ƙarasa ƙofar gidansu ta hango motar da suka tafi da ita ta nufota, batasan lokacin data saki wani irin yalwataccan murmushi ba saboda tsananin farin ciki da ya mamaye mata zuciyarta, ga fararan haƙoranta suma saida suka bayyana.

    Motar tsayawa cak tayi a inda take, yayinda Zuhra ta runtse idanu murmushi ɗauke a fuskarta zataga Ya Saninta dakyau, a hankali ta buɗe idon saidai har yanzu ba'a buɗe motar ba bare tasan su waye a cikinta, a hankali Glass ɗin motar ya sauka ƙasa saidai yanzu babushi a ciki, Baffah ta gani fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Zuhra!"
   "Baffah!" Zuhra ta kira sunanshi da mamaki fal kan fuskarta, murmushi kawai Baffa yayi yace "Ki sauri ki shigo kizo mu tafi" kamar jira take tai saurin buɗe motar ta shiga, rufe Motar tayi ba tare da Baffa ya kalli inda take ba ya fara tuƙinsa a hankali, hankalinshi naga Titi yace "Zuhra menene haɗinki da Fahad Iyan Tama?"
    Zuhra bata amsa mishi ba sai jefo masa wata tambaya tayi tace "Ina Ya Sani?"
Baffah yace "Tambayarki nayi baki bani ansa ba
"Ba abunda ya haɗani dashi" ta faɗa tana so ta kauda zancan.
   Baffah murmushi yayi, yayinda yake ƙoƙarin shiga anguwar tasu yace "Shine kike hira dashi, kuma ga dukkan alamu hirar na miki daɗi, domin kuwa tun kafin ki fito muke wajan nidashi, amma saboda tsananin shauƙin soyayya baki kula damu ba"
   "Hmm" kawai Zuhra tace bata ƙara ce masa Uffan ba, a haka har suka ƙarasa gidan, Parking yayi saida ya fito sannan yace itama ta fito mana, ba musu ta fito tana ƙarewa anguwar kallo kamar ta taɓa zuwanta, ganin ya shiga wani madaidaicin Flat ne yasata biyosa cikin sassarfa, duk da gabanta ba ƙaramin faɗuwa yakeyi ba na haɗuwarta da Ya Saninta.
   Baffah tsayawa yayi a ƙofar shiga ɗakin yace "Ki shiga yana ciki, kinsan yadda zaki ki shawo kanshi dan ba ƙaramin cikin tashin hankali yake ciki a halin yanzu ba"
  Gyaɗa kanta kawai tayi ji take bazata iya haɗa idanu dashi ba, domin kuwa gani take tamkar taci amanarsa na ganinta da yayi da Fahad a tsaye, daure zuciyarta tayi sannan tace "Na aje wasu File a motarka ka kulamin dasu"
   Gyaɗa kai yayi, tare da barin gun, ita kuma ta murɗa Handle ɗin ta shiga ciki gabanta na tsananta faɗuwa.
   Tana tura ƙofar taga babu kowa a cikin Parlourn sai ƙarar T.V da kuma A.C ɗin dake cikin Parlourn ganin Bedrooms ɗin har uku yasata tsayawa cak ta kasa gane wannene nashi, haka kawai jikinta ya bata Bedroom ɗin ƙarshe shine nashi, a hankali ta taka zuwa cikin Bedroom ɗin, tura ƙofar tai a hankali ta hango mutum kwance kan Gado ya lulluɓe jikinsa da Blanket.
   Muhammad Alee jin buɗewar ƙofa yasashi yin tunanin ko Baffah ne kasancewar ya juyawa ƙofar baya, muryarsa na Cracking yace "Baffah ƙishi nakeji"
   Cikin sauri Zuhra ta nufa Fridge ba abunda ke tashi cikin zuciyarta sai tausayin kansu ita dashi kawai take, bata taɓa yadda cewar yana raye ba sai yau, bata taɓa sanin yana cikin garin Kano ba sai yau, ɗauko ruwan tayi tare da tsiyaya mai a cikin Cup tai sauri ta nufa inda yake ta aje Cup, ƙoƙarin miƙar dashi takeyi ta kasa.
    Muhammad mutuwar zaune yayi, tabbas Zuhra ce ta shigo ɗakinsa, tayaya tasan inda suke, shine tambayar da yayiwa zuciyarsa, ɗif ya ɗauke wuta tare da ƙara janyo Blanket ɗin ya lulluɓa har kanshi baiso ya ganta, baiso ya haɗa idanu da ita dan tabbas yayi ɗaya daga cikin ws ƴannan zai manta da duk abunda tai masa ne.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now