Page 31

203 23 6
                                    

Fahad ne zaune a ɗakinsa yayinda ɗakin nasa ya dawo na masu hankali, domim kuwa kwalima yayma ɗakin duk wani kayan shaye-shaye saida ya fitar dasu tare da ƙara tsaftace ɗakin duk wani abun iskanci saida ya fiddashi ciki, saidai tabbas yanaji a jikinsa soyayyar Zuhra itace zata zama ajalinsa itace jarabawar da Allah ya ɗaura masa, yay addu'a akan Allah ya yaye masa sonta saidai ji yake tamkar ana ƙara mishi wutar sonta, hannunsa ne dafe akan ƙirjinsa yana faman lumshesu, jin yadda zuciyarsa ke faman harbawa da ƙarfin gaske, lumshe ido yayi yana mai Allah wadai da irin halin rayuwar da yayi a baya, idan ya tuna ba abunda yakw furtawa sai neman gafara gurin Ubangiji, tashi yayi ya shiga Bathroom dan watsa ruwa.
   
     Muhammad kallan Zuhra yayi tana lafe kan ƙirjinsa tana faman lumshe ido saboda abunda takeji, kallanta fuskarta kawai yake ganin yadda tai haske kuma tai fayau da ita, sai wani jarababban Bacci data iya wanda bata mintu 5 zata zube agun tai kwanciyarta tana bacci, yanzumq dawowarsa kenan yaganta a tsakar ɗakin ta baje tana bacci ga tsintsinya a gefenta ga dukkan alamu shara take bacci yayi awon gaba da ita, hakan yasa Muhammad ƙarasa sharar tare da ɗaukarta cak tamkar wata ƴar Baby ya kaita kan Bed ya shinfiɗar da ita akan ƙirjinsa.
    A hankali ta fara buɗe idanunta ganinta a Bedroom yasata saurin miƙewa dan ƙarasa aikin da zatai kar Yayanta ya dawo ya maida ita mara tsafta, ko kaɗan bata lura cewar ma tana jikinsa ba, ganin yadda ta tashi a hargitsene yasashi saurin ruƙota yana faɗin "Ina zaki?"
  Murza idanu tayi ta ga harya dawo, kallan Agogon dake manne a jikin bango tayi taga har takwas tayi na dare, nan ta fara murza idanu ganin bama tai girki ba ga ɗakinma bata gama gyara shiba, yau kusan sati ɗaya kenan tana haka, ita tsoronta kar tazo ta ƙuresa ya fara mata faɗa duk fa har yanzu bai nuna damuwarsa akan rashin girkin da batai ba na kwanankinnan sai gabda yamma wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
   Cikin rawar murya tace "Dan Allah kayi haƙuri" tana faɗa tsoro ƙarara ya bayyana a fuskarta, kwanto da ita kafaɗarsa yayi yace "Me kikai?"
  Shiru tai tana tsoron faɗa masa yau ma batai girki ba, kama hannayanta yayi ganin yadda ta naida hankalinta akansu tana wasa dasu, sadda kanshi ƙasa yayi yace "Tambayarki fa nake, haƙurin me zanyi?, laifin me kikai min?"
   Farawa matsawa tai da baya da baya tace "Wallahi bansan dare yayi haka ba, banma san bacci ya kwasheni ba sai yanzu dana farka naga dare yayi"
  "Uhum" Muhammad yace, sannan ya ƙara jefo Mata wata tambayar yace "Se kuma maiya faru?"
  Ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin tace "Banma gama gyara ɗakin ba kuma yau banyi......."
  Shiru tai ta kasa ƙarasawa, hakan yasa Muhammad ya fahimci cewa duk maganar da yayi mata jiya da nasiha akan ta runƙa mai girki ashe bataji ba, yauma batai girkin ba kenan, shiru yay yana ƙoƙarin kawar da ɓacin ran da yake ciki, ɗagowa yayi fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "Zuhra mai yasa kwana biyunnan kike fatali da magana tane?, raini ya fara shiga tsakaninmu ne bansani ba?"
   Sauri tai ta girgiza kai tace  "Dan Allah kayi haƙuri Yaya, nima wallahi banason ina kauce maganarka" hawayan daya sauko matane tasa bayan hannunta ta goge jikinta na rawa.
   "Zonan" ya umarceta, kallanshi ta tsayayi tana karantar yanayin fuskarsa, sai kuma ta kasa zuwa, kuka tahauyi tare da sharce hannayanta tace "Dan Allah kayi haƙuri ban ƙarawa wallahi bazan kuma ba"
   Tausayi ta bashi ganin yadda duk ta rame zai haske, hakan ya tabbatar masa da cewar akwai abunda ke damunta, sakin fuskarsa yayi yace "Zona tambayeki"
Ganin fuskarsa a sake yasata zuwa cike da fargaba, tana zuwa ya janyota jikinsa tare da kwantar da ita ya yaye rigar fake jikinta yana kallan cikinta tamkar ba'a taɓa bashi abinci ba, cikin sanyin murya yace "Faɗima kinacin abincin rana kuwa?"
  Girgiza mai kai tayi tana matsar hawaye alamun "A'a", "Yaushe rabonki da kici abinci?" ya tambayeta mamaki fal kan fuskarsa, "Yaya Bana iyaci banjin sha'awar ci Tea nakesha kawai"
   Dafe kanshi yayi ganin yadda Business yakeso ya hanashi kula da abar ƙaunarsa, "Tea fa kikace?"
Gyaɗa kanta tai tana ƙoƙarin tashi daga kwancan datake tace "Eh, bana iyacin komi, sai baccin dake yawan addabata" kawar da kanta gefe tayi tace "Gashi kuma ko yaushe ina tsabanin sha'awarka Yaya na rasa yadda zanyi, naga kai kuma kwana 2 kana cikin aiki"
  Kalamanta na ƙarshe ba ƙaramin mamakinta suka saka shiba jin yadda Zuhra ta buɗe baki ta faɗa masa haka,  ganin yadda ya santa inhar ta fanninan ce tana matuƙar jin kunyarsa daidai gwargwado, danma yakan nuna mata bayaso.
   "Faɗima!" ya kira sunanta amma taƙi waigowa su haɗa ido, gashi idanunta a rufe suke ita kanta batasan lokacin da bakinta ya furta hakan ba saidai ba yadda zatai dole ta sanar dashi ko zai bata lokacinsa ko yayane.
  Murmushi kawai yayi ganin yadda ta runtse idanunta kuma taƙi bari su haɗa ido.
  Tashi yayi ya fita yayinda tabishi da idanu har saida ya ɓacewa ganinta, ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda wata irin muguwar sha'awarsa ke addabarta gashi kwana biyu baya bata lokacinsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da janyo Pillow ta kwanta kafin kace me Bacci har yayi nasarar ɗaukarta.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now