Zuhra ɗan zaro idanu tayi tana ƙoƙarin faɗin "Ya Sani Please mana, dan Allah ka daina banso..."
Bai bari ta ƙarasa ba ya ƙara haɗe bakinsa da nata ko kaɗan bayaji baya gani, dan har wani duhu-duhu yake gani a idanunsa, ganin da gaske yake baya cikin hayyacinsa yasata yunƙurin turesa dan ko kaɗan bazata taɓa jurar saƙonnin dayake bata ba, dan ita kanta tana da buƙatar kasancewa dashi saidai bazata iya bashi kanta ba a wannan halin da suke ciki, kallanshi tayi ganin baima san abunda takeyi ba haka kawai sai taji ya bata tausayi, tabbas idan harya tsare kanshi a wa ƴannan shekarun to tana da tabbacin saiyayi mata abunda yafi hakama, domin tasan ko waye Ya Saninta akanta, hawaye da suka fara sauka akan kuncintane yasashi jin ɗumi a fuskarsa, a hankali ya buɗe idanunsa ganin tana zubda hawaye ya fara ƙoƙarin yin controlling kanshi, ɗan sakinta yayi ya fara tambayarta lafiya.
Zuhra tuni zuciyarta ta afka banzan tunani, ba abunda take sai kuka, ƙara matsowa yayi kusa da ita tare da lulluɓe jikinsa cikin Blanket ɗin ganin ta matsa kusa dashi ya fara ƙoƙarin janyota jikinsa, bigeshi tayi da ƙarfi ta cigaba da rera kukanta, matsawa kusa da ita yayi muryarsa can ƙasan maƙoshi saboda halin da yake ciki yace "Zuhra menene please, kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba, but kinsan nai ƙoƙarin ace kusan 2years da aurena ban samu na keɓe dake ba daidai da na minti ɗaya ba sai yau, amma bazan ƙara ba..."
Dakatar da kukanta tayi tare da ɗaga mishi hannu tace "Ya Sani ya isa haka, banson jin daɗin bakinka, tayaya zan yadda cewar bakasan mace ba, zuciyata ta tabbatarmin da cewar Ya Sanin yasan mace, ba komi yasa na yadda ba kalli yadda kake sarrafani sai kace ba saurayi ba" wani abune ya tsaya mata a maƙoshinta saboda kishin datakeji game dashi, "Nidai karka ƙara taɓani, kuma wallahi sai an warware auranmu"
Muhammad Alee mutuwar tsaye yayi saboda matuƙar mamakin jin furucinsa a gareshi, muryarsa na rawa yace "Faɗima!" duk wani jin daɗi dayajishi a ciki nan take ta gushe saboda tashin hankalin daya jishi a ciki, jikinsa har wani rawa ya fara jin abunda tace game dashi.
Ya daɗe yana kallanta koda wasa ya kasa ƙiftawa, yanaso su haɗa ido da ita dan ya ƙara tabbatarwa da kanshi cewar dashi take, "Ni kike zargi da lalata da wata macen bayanke?"
Ya jefa mata wannan tambayar.Zuhra kanta a ƙasa ba tare data kalleshi ba, so take ta tabbatarvda gaskiyar lamari, ganin har yanzu ta kasa haɗa ido dashi yasashi cewar "Koda wasa ban taɓa zarginki da aikata Zina ba Faɗima saboda zuciyata ta aminta dake yadda bakya tsammani, ko wani nagani ya fitilo daga Bedroom ɗinki yana gyara belt ɗin jikinsa bazan taɓa zargin cewar ya taɓa miki hannu ba bare yayi lalata dake amma danme ni zaki yankemin wannan ɗanyan hukuncin?"
Zumɓuro baki gaba tayi amma duk da haka ta haɗa idanu dashi, domin kuwa ba abunda take sai ɗunbin dana sani na faɗa masa wannan furucin datayi.
Sama ya kalla yace "Allah kaine shaidata, koda wasa ban taɓa yunƙurin taɓa hannun wata ba dan naji daɗin kaina ba" cikin ɗaga murya yace "Faɗima!, dake nake magana ki ban amsata"
Jin muryar tasa daɗan ƙaraji ta tabbatar da ranshi ya soma ɓaci, cikin in-ina tace "Please Ya...ya...."
Dakatar da ita yayi yace "Ya wuce tashi ki tafi gida"
Yana gama faɗan haka ya juya mata baya tare da janyo Blanket ya lulluɓe gabaki ɗaya jikinsa, Zuhra ganin ya juya mata baya yasata kafe bayanshi da ido tabbas tasan batai masa adalci ba, ita kanta tasan tun tana yarinya Ya Saninta miskiline na gaske amma inhar akanta ne shi soko ne, haka tunda ta taso inhar yazo gidansu mata suyita zuwa kallanshi daga baƙar fatar har turawan saboda kyanshi da kwarjininsa amma koda wasa bai taɓa sakewa ɗaya daga cikin ƙawayanta ba, hasalima da yayi musu kallo ɗaya zasu daina kallanshi ko su bar wajan, da ita kaɗai ta iya wasa, akanta ne kaɗai zai zauna yayi dariyar da zai daɗe bayyita ba, akanta ne yake toshe kunnawansa wajan abokanan wasansa na cewar shi bawan macene, ko kaɗan bai taɓa fushi da wannan kalmar ba saboda yasan akan wa ake kiransa haka, tasan Ya Sani yana da tsananin sha'awa saidai koda wasa bai taɓa yunƙurin yin lalata da ita ba ko suyu Romacing sanya biyawa kanshi buƙata ba, hasalima zai faɗa mata abunda yakeji saidai koda wasa bai yunƙurin yi mata komai, ansha barunsu a gida su kaɗai tai shigar datakeso saidai yayi mata faɗa akan taje ta can dressing saboda halin da zata jefashi ciki, ciwon cikin da yakeyi kuwa yakai maƙura tun yanayi a ɓoye har tazo ta sani iyayanshi suma suka sani, hakan yasa tana gama Secondary School aka fara yi musu shirye-shiryen aure gudun faɗawa halaka.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...