Joseph kallan Fahad yayi yace "Kashe Muhammad Alee yana da matuƙar wuya saboda akwai Baffah a tattare dashi, amma akwai dabarar da zanyi wanda zamu sameshi cikin sauƙi"
Murmushin jin daɗi Fahad yayi tare da tabbatarwa da Joseph inhar hakan ta kasance yana da kaso mai tsoka wanda zai bashi.
Sun ɗauki lokaci mai tsayi suna fafutukar yadda kisan zai kasance saidai har yanzu basu samu takamaiman abunda zasuyi cikin sauƙi ba.
Yayinda Joseph ya sanar da Fahad su samu Baffah su turashi wani gun mai nisa tare da kashe wayoyinsa sannan su kira Muhammad Alee su shaida masa da Baffah yayi hatsari mafi muni yana cikin tsakankani rayuwa ko mutuwa, ganin yadda Muhammad Alee ya ɗauki Baffah tamkar ɗan uwansa na jini hakan zaisa ya taho duk inda sukace mai yake hankali tashe, wannan itace damar da zasu samu.
Fahad ba ƙaramin jinjina basirar Joseph yayi ba ganin yadda ya samo musu hanya mafi sauƙi, nan suka rabu tare da tsaida ranar da zasu fara aikin.Zuhra zaman ɗaki ya zame mata jiki yanzu dan itama ba ƙaramin kunyar haɗa idanu takeyi ba itada mahaifan nata, wayar dake kusa da itane ta fara ringing numfasawa tai tare da duba mai kiran nata, ganin sabuwar number yasata kauda kanta ta cigaba da abunda take, ganij yadda ake kiran nata babu ƙaƙƙautawa yasata ɗaukar wayar a fusace ta ɗauka tare da karata a kunnanta ba tare datace Uffan ba, muryar Fahad ce ta doki Dodon kunnanta, shiru tai dan harga Allah jin muryarsa datayi ba ƙaramin faɗuwar gaba ya sakata ba, domin tasan ko wanene Fahad mutum ne mai hatsarin gaske.
Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa "Har yanzua kina amfani da wannan Line ɗin kenan"
Shiru tayi ba amsa yayinda gabanta ya cigaba da tsananta faɗuwa, cikin sanyin murya tace "Please Fahad me kake ƙoƙarin yin haka, donme zaka kirani alhalin kasan ni matar aurece"
Dariyar rainin hankali ya bushe da ita yace "Niko na sani, kafin wani lokaci ƙanƙani ki fara takabar gaske bayan kinyi ta wasa a daa Zuhra ni zaki rainawa hankali?, ni zaki yaudara?, ni zakiciwa amana, kinsan ko wanene Fahad Iyan Tama kuwa?, wallahi billahil azim kinji na rantse miki da badan akwai narkakkiyar soyayyarki a cikin zuciyata ba da sai kinsha mamaki na, daa ko a mafarki akace kima Fahad Iyan Tama wasa da hankalo da bazakice zaki ba,bazan daina faɗa miki kalmar soyayya ba tare da miki albishir na cewar Fahad Iyan Tama an haliccesa dominki ne, wallahi Zuhra kota halin ƙaƙane saina mallakeki koda kuwa Muhammad zai rasa rayuwarsa ne ban damu da hakan ba burina naga kin zama mallakina" bai jira cewarta na ya kashe wayar ya barta da ɗunbin tashin hankali.
Wata zuface ta fara tsatstsafo mata duk da A.C ɗin dake aiki a cikin ɗakin, tamkar wata sabuwar kamu haka ta fito daga Bedroom ɗinta, yayinda taci karo da mahaifiyarta tana zaune tana kallo, ganin ta fito tamkar ba'a hayyacinta ba yasata cewa "Zuhra lafiya?"
Tsayawa tayi tai wuri-wuri da ido tana faman sauke ajiyar zuciya tamkar wacca ta shiga gasar yin tsere, sosa ƙeya tahauyi tace "Mommy gun Ya Sani zanje"
Ta faɗa wannan karan babu alamun kunya ko kawaici a tattare da ita, wani kallo ta jefeta dashi tace "Ba inda zaki, maza ɓacemin a gu"
Tsayawa tayi cak babu alamun zata bar wajan, kauda kanta gefe tayi tace "Mommy gun Ya Sani nace fa" ta faɗa yayinda hawayan dataita ɓoyesu suka sauko akan kuncinta tasa tafin hannunta ta goge,
Kauda fuskarta tai dan karta gane halin datake ciki, shiru mahaifiyarta tayi ganin halin da ƴarta take ciki, sassauta muryarta tayi tace "Zonan Zuhra"
Ba musu Zuhra ta zauna kusa da ita tana so ta ɓoye damuwar datake addabarta, hannunta ta ruƙo tace "Sani baya nan sun fita shida Daddynku kinsan aiki yasha mai kai akan Plaza ɗin da yake ginawa" shiru tai tana wasa da yatsun hannunta ba tare datace ma Mommyn nata Uffan ba, sallamarsu ce ta katse musu hanzarinsu, mahaifin Zuhra ne yayinda Sani ke biye dashi da wasu kaya a hannunsa, tunda taji muryarsa ta ɗago da Oily Eyes ɗinta tana kallansa, haka zalika shima kallan nata yake saidai yanaso yayi Controlling ɗin kanshi dan kar Daddy ya gane, danshi sam bai kula da cewar tana kusa da Mommy bane.
Mahaifiyar Zuhra kauda kanta gefe tayi ganin sunaso su bata kunya, muryar Daddy ce ta katse musu abunda suke yace "Aje kayan anan ma ya isa" ajiyewa yayi kanshi a ƙasa ya gaishe da Mommy dan sai yanzu ya lura da ita a ɗakin yayinda wata kunya data kamashi ganin ashe Zuhra na kusa da ita, addu'a kawai yake Allah yasa bataga kallan da yyaiwa ɗiyarta ba.
Juyawa yayi ya fita, yayinda Zuhra ta miƙe itama zata bishi, mahaifiyarta harta buɗe baki zatai magana ganin yadda mijin nata ya kalleta yasata yin shiru tabarta ta fita, ganin ta fita yasata ce mishi "Yanzu zuba ido zamuyi tana zuwa ɗakinsa, alhalin kasan abunda ya faru rannan"
Dariyar manya yayi duk da maganarta ba ƙaramin kunya ta saka shi ba, gyara zamanshi yayi yace "Toya zamuyi, bamu da hujja ko agun Allah, takunkumin da muke saka musu sai kiga Allah yayi fushi damu mun hana ma'aurata kasancewa da juna, saidai kawai ki mata faɗa akan ba koda yaushe zata runƙa binsa inda yake ba"
"Hmm" kawai tace, ta juyar da kanta ta cigaba da kallanta, tashi yayi yazo inda take yace "Haba Uwargida sarautar mata wannan zafin fa, kinsan dai Zuhra da Sani ma'auratane to danme zamu runƙa haramta musu junansu, kinsan Sani yana da matuƙar kunya ke shaidace haka ma Zuhra amam tunda kikaga sunyi fatali da wannan kunyar sunyi ahunda sukeso kinsan haƙurinsu ne ya ƙare, insha Allahu sun kusan tarewa a gidansu"
Taɓe baki tayi tace "Nidai wallahi gwanda su tare ɗin dan bazasu barni ina fama da jin kunyarsu ba a cikin gidannan"
Sosai maganar ta bashi dariya, miƙewa yayi yace "Bari na watsa ruwa, please ki barta karki aika a kirata dan nasan halinki"
"Uhm" tace itama ta miƙe ta marawa mijin nata baya don tai maka masa.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...