Azmah kallan jinjirarta takeyi tanajin wani sonta na shiga duk wani kafafun dake jikinta, tausayi, tsoro da tsantsar nadamane suka ziyarce ta lokaci guda, tana tausayawa ƴarta sannan tana tsoron kar ƴar wataran ta girma ta tambayeta wanene mahaifinta, hawayene masu ɗumin gaske suka sauka akan kuncinta tana neman gafarar Allah tare da bayyana mata mahaifin wannan yarinyar ko yayane, ba abuna take sai kaico da rayuwar data ɗauko ma kanta mara amfani, haka Azmah tai ta zama a asibiti domin jinyar kanta kafin a sallamesu.
Sallamar Get Man ɗinsu ce ta dawo da ita duniyar tunanin data wulla, kallanshi tai da Oil Eyes ɗinta tace "Wa'alaikumussalam" ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar mata saƙon dake tafe dashi, numfasawa tayi tace "Kace gashinan zuwa" tashi tai jikinta a matuƙar sanyaye yau kwata-kwata batajin daɗin jikinta, a hankali ta tura ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta samu gefen Bed ɗin ta zauna tana ƙarewa kyakykyawar fuskarsa kallo, lallausan hannunta tasa ta fara shafa fuskarsa, jin hannunta akan fuskarsa yasashi ruƙe hannun fuskarsa a rufe murmushi shinfiɗe a fuskarsa ya juya mata baya, bakinta tasa a tsakiyan bayanta tai masa kiss har saida ya ɗan banƙare tana dariya ƙasa-ƙasa, cikin sanyin murya tace "Ka tashi kayi baƙo"
"Bana nan" itace amsar daya bata ya cigaba da baccinsa.
"Nace ace gaka nan zuwa fa"
"Uhmm" kawai Muhammad yace, ƙara yaye Blanket ɗin daya rufa tayi tace "Baffah ke kiranka inji Hamza"
Buɗe idanunsa yayi tar suna kallan Ceiling "Baffah?" ya faɗa fuskarsa ɗauke da tsantsan mamaki da kuma farin ciki mara misiltuwa, yaye Blanket ɗin daya rufa yayi, Boxer ne kawai a jikinsa Direct Wardrobe ya nufa ya buɗe yana neman kayan da zai saka, jikinsa har rawa yakeyi saboda tsananin farin ciki yanaso ya fita ya ganshi, soyayyar Baffah a cikin jinin jikinsa take, Zuhra rungumesa tai ta baya tare da yiwa wuyansa Kiss tace "Waye Baffah agunka haka?"
Ajiyar zuciya kawai ya sauke ba tare daya bata amsar data tambaya ba ya fara saka wata tsaleliyar jallabiya, juyo da ita gabanshi yayi yana ƙare mata kallo sonta na shiga duk wasu kafofi na jikinsa, a hankali ya rungumo da ita jikinsa ya ɗaura bakinsa kan laɓɓanta ya fara Kissing ɗinta, saida ya gaji dan kanshi sannan ya saketa yana maida numfashi, fesa turare yayi kaɗan, sannan ya kama hanya ya fita dan tarbar babban abokinsa kuma ɗan uwansa.Fahad ya ji sauƙi sosai tamkar bashi ba, yanzu ba abunda ya saka a gaba sai harkar kasuwancinsa, sallamar da akaimai ne ta katse mai abunda yake, Jiddah itace tai sallamar cikin sanyin murya tare da tsoro ƙarara a fuskarta, cikin natsuwa taje fa ajiye Warmers ɗin da Maman Fahad ta bata akan ta kawo mai Part ɗinsa, tunda ta shigo idanunsa suke kanta, kusan sati biyu kenan tunda tazo gutu gidan yakejin wani abu a tattare da ita, tun yana tunanin menene nan take zuciyarsa ta bashi amsar da ya faɗa soyayyarta ne.
Saida tazo gab dashi ya lura da tana kusa dashi "Ya jikin naka?, Mom tace ka daure kaci abincin ko yayane"
Ta faɗa cikin sanyin murya kanta a ƙasa domin kuwa ba ƙaramin tsoronsa takeji ba tun lokacin da yayi yunƙurin aikata mata fyaɗe shekarun baya da suka wuce, daƙyar tasha ranar saidai har yanzu Allah ya haneta da faɗawa kowa abunda ya faru tunda dai Allah ya auna azziki.
Jin numfashinsa a kusa da ita yasata ɗago da kai cike da tsoro tana kallanshi, dan bazata manta ba tun lokacin bata ƙara gigin zuwa gidansu da sunan hutu ba bare kuma Part ɗinsa,yanzu ma labarin natsuwarsa taji da kuma ita kanta yadda taga Changes a tattare dashine yasata harta amince ta yarda Mommy ta aikota ɗakinsa.
Cikin wata irin murya Fahad ya kira sunanta wanda tunda suke tare bata taɓajin ya ambata sunanta haka ba, runtse idonta tai ba abunda take karantowa sai addu'o'in tsari daga Fahad, a hankali ya saka hannunsa cikin nata, nan take jikinta ya fara rawa, hawayan datake ƙoƙarin ɓoyewa suka sauka akan kuncinta, ɗago da fuskarta tayi tana kallanshi hawaye na daɗa saukowa a kuncinta, girgiza kanta ta fara mai, daƙyar ta iya haɗa kalmar "Please".
Hannunta ya saka saitin zuciyarsa, sauri tayi ta cire hannun jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfin gaske, cikin sarƙewar murya yace "Dan Allah ko zaki zauna muyi wata magana mai muhimmanci?"
Kallanshi tai na wani lokaci taga babu fitinar data saba gani a ƙwayar idanunsa, jiki ba ƙwari ta samu guri nesa dashi ta zauna kanta a ƙaza tana wasa da yatsun hannuwanta.
Ya ɗauki lokaci kafin yafara bayyana mata sirrin dake cikin ransa, yayinda Jiddah ba abunda take sai faman girgiza mai kai tana kallanshi da idanunta wanda suka cika da ƙwalla.
Kamar an mintsineta ta tashi tsaye tana jifanshi da wani irin kallo wanda ya kasa gane me take nufi, baza'a kira kallan da kallan tsana ba haka zalika baza a kira kallan da farin ciki ba ko fushi.
Ya buɗe baki zayyi magana kenan tai saurin ɗaga masa hannu alamar daya dakata, bakinta ta toshe jin kukan nata yana ƙoƙarin yin ƙarfi tai maza tabar ɗakin cikin sassarfa, direct ta ƙofar baya tabi ta shiga ɗakin ƙannansa tana ta addu'a Allah yasa babu kowa a Bedroom ɗin ilai kuwa ba kowa a cikinsa, faɗawa kan Bed ɗin ɗakin tayi ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, tabbas zuciyarta ta daɗe da kamuwa da son Fahad amma tai ƙoƙarin yaƙarta domin kuwa Fahad ba sa'anta bane ko kaɗan, halayyarsu ta banbanta ta ko ina, Allah yayiwa Jiddah kamun kai da natsuwa tayaya zata iya aurar Fahad alhalin tasan halinsa ciki da bai, gaskiya bazata iya aurarsa ba, a gaban idonta yake kawo mata cikin ɗakinsa yayi duk abunda zayyi dasu su fita haka zalika inhar yaga ɗaya daga cikin ƴan aikin gidan sun masa yarinya ko tanaso ko bataso to tabbas saiya ɓata mata rayuwa, rufe kunnuwanta tai da hannayanta bataso taji wani abu game da Fahad, bazata iya aurar mazinanci ba saboda faɗan Annabin ne duk wanda ya ɓata ƴar wani to tabbas sai an ɓata ƴarsa, tayaya zata bi son zuciyarta ta zaɓarwa ƴaƴanta Uban da ba na gari ba, wata irin ajiyar zuciya ta sauke kishin datake fama dashi akanshi yau ya tashi bazata taɓa auran Fahad ba domin ya lalatawa yara rayuwarsu da dama, tashi tai ta ɗauko trolley ɗinta ta fara haɗa kayanta don kuwa ta rantse yau bazata ƙara koda awa ɗaya a gidan ba, tana haɗawa taba faman share hawayan fuskarta, mafarkin datakeyi ya tabbata saidai har abada bazata taɓa auran Fahad ba, bata taɓa Zina ba tayaya zata auri Mazinanci, wannan abun shine yayi tasiri a zuciyar Jiddah tare da kuɗurin barin Kano yau insha Allahu Zaria zata koma.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...