page 20

249 23 5
                                    

A babban parlour ya samesa ya zauna dirsham a ƙasa yana sauraransa, gyran murya mahaifin Zuhra yayi yace "Yanzu a ina kake zaune?"
   "Ina zaune a Area Ten ne nidasu Baffa" cewar Muhd.
  "Okay haya kuke kenan?"
  Gyaɗa kanshi kawai yayi baice masa uffan ba.
   "Daga yau ka dawo gidanku da zama, kafin na samu natsuwa na nemo malamai naji yaya maganar auranku take kaida Zuhra, shin yana nan ne koko sai an gyarashi, inyaso saiku zauna a gidanku kenan sai a fara gyara"
  Murmushi ya suɓuce masa ba tare da yayi aune ba, ɗan kawar da kanshi gefe yayi dankar yaga annurin dake kwance a fuskarsa, sosa ƙeya yahauyi yace "Daddy duk yadda kace haka za'ai"
  Shima murmushin yayi yace "Shikenan tashi kai tafiyarka Allah yayi muku albarka, ka tambayi Zuhra ko Mommy su baka Key ɗin extra ɗakinnan"
  Tashi yayi hannunshi saƙale a wuyansa yace "Godiya nake" a haka ya fito yabar ɗakin, direct waje ya fita ya nufa parking space dan zuwa ya sanar da Baffah halin da ake ciki, ganin Fahad ya fito yana jingine da motar hannunsa ruƙe da waya ga dukkan alamu neman Zuhra yakeyi a wayar, nan take annurin fuskarsa ya canza kishi yayi saurin ziyartar zuciyarsa, haɗe fuska yayi yana maijin wani iri cikin zuciyarsa, kasa tafiya yayi shika ya tsaya a jikin motarsa hannayansa sarƙe a ƙirjinsa yana jiran fitowarta.
  Ta ɗauki lokaci kafin ta fito dan duk a tunaninta Muhammad Alee ya tafi domin kuwa taji motsin fitarsa, fitowa tayi fuskarta gadaran gadahan, ganin Muhammad Alee a tsaye hasken fitulu sun haskashi tai saurin ɓoyewa a wani gurin ƙirjinta na faman bugawa da ƙarfin gaske, samu tayi ta saɗaɗa ba tare data bari ya ganta ba ta gudu cikin gida tana maida numfashi, lumshe ido kawai tayi ƙirjinta na faman bugawa, tasan ko sama da ƙasa zata haɗe Yayanta bazai taɓa barinta ta ƙarashe wannan mission ɗinba, gashi Fahad inhar yajita shiru to tabbas zai zargin wani abu, ba abunda kawai take sai tunanin tayaya zata ɓullowa lamarin.

   Fahad ya daɗe matuƙa a tsaye, yayinda Muhammad Alee ya shiga motarsa yana jiran fitowar Zuhra, ganin Fahad ya shiga mota ya fita daga gidan a fusace yasq Muhammad yin murmushin gefen baki, shima ya tada motarsa ya fita daga gidan zuwa tsohuwar anguwarsu.

     *Washe Gari*
   Tunda Muhammad suka dawo daga masallaci ya shiga ɗaki ya shige har yanzu bai fito ba, gashi gabaki ɗaya gidan sunyi break fast nashi kawai aka aje akan Dinning Table, ɗan juyawa yayi jin wayarsa na ƙara alamun tana hana mishi jin daɗi, ƙara tura wayar yayi ƙasan Pillow ɗinsa yana ƙoƙarin komawa baccinsa, ganin mai kiran bazai haƙura da kiransa ba yasashi ɗauka ya kara a kunnansa ba tare daya duba mai kiran ba, cikin murya wacca kanaji kasan bacci yake yayi sallama, an ɗauki minti wajan uku kafin a ansa, jin muryar mace yasashi ɗan ware manyan idanunsa tare da cire wayar a kunne ganin sabuwar number yazashi kashe wayar tare dayin guntun tsaki ya koma ya kwanta, jin an ƙara kira yasashi ɗauka a fusace yace "Wacece ke?"
  Muryarta na rawa tace "Azmah ce" ta faɗa hawaye na sauka akan kuncinta.
   Shiru yayi naɗan wani lokaci yana tunanin wacece ita, ƙara katse mai tunani tayi ta hanyar cewar "Ɗiyar Alhaji Abdul-Jabbar..." ɗif taji an kashe wayar ba tare data ƙarasa faɗan abunda takeson faɗa ba.

   Azmah bin wayar tata tayi da kallo zuciyarta na mata zafi, yanzu ta samu numbern nasa daƙyar amma bai tsaya ya saurareta ba, batai fushi ba ta ƙara kiran Line ɗin saidai wannan karan numbern nashi a kashe take gabaki ɗaya, ajiyar zuciya ta saki tare da janyo pillow ta rungume tana zubda hawaye, ya zamar mata dole yau taje ta sameshi tunda ta rugada tasan inda yake zaune, share hawayanta ta ƙarayi tare da kafe wayar da kallo.

Ganin baccin ya gudu ya sashi tashi ya shiga Bathroom yana faman yin guntun tsaki ba abunda yake tunani sai a ina ta samu numbernsa dahar ta kirasa, koma waye ya bata numbernta na jikinsa ne, tsayawa yayi da wankan da yakeyi yan tunanin wasu abubuwa da dama, badai a cikin yaransa akwai wanda sukewa su Abdul-Jabbar aiki ba, tabbas akwai ɗan leƙan asiri a cikinsu saboda kuwa wannan numbern ba kowa yasanshu da ita ba saisu, murmushin takaici yayi ya cigaba da wankansa yana tunanin wanene wannan a cikinsu, tuno da Baffah da yayi yasashi tabbatar da cewar Baffah yasan kosu waye ganin yadda yake taka tsantssn da lafiyarsa sannan bai yadda tafiya ta haɗasu ba, ba tare da Baffah yace zai bisu ba, yakan lura da fuskokisunsu ganin ta canza lokaci ɗaya shi a tunaninsa dan Baffah yana saka musu ido ne.
    Da wannan tunanin ya fito ƙugunsa ɗaure da Towel, ɗaya kuma na kanshi yana goge sumar kanshi, ɗagowar da zayyi yaga Zuhra tana jera masa Breakfast akan ɗan madaidaicin Stool ɗinsa, murmushi yayi tare da takawa a hankali ya ruƙe mata ƙugu.
   Ɗan zillo tayi jin wani abu ya ratsa ƙugunta ya wuce, juyoww tayi da sauri sai ganin faffaɗan ƙirjinsa tayi wanda gashin gun yasha ruwa yayi luf, ɗan runtse ido tayi tunda tau tozali da Nipples ɗinsa, ba abunda gabanta yake sai bugawa da ƙarfi, juya mishi baya tayi tana ƙoƙarin guduwa amma sai taji hannunsa a ƙirjinta ya rungumeta tsam ya karkato da kanshi zuwa wuyanta tare da faɗin "Good Morning my Pricess, tunda ke bazaki gaishe dani ba"
   Wani saliva ta haɗiye ji kake ƙut, tace "Yaya Ina kwana?" ta faɗa muryarta naɗan rawa amma ba sosai ba.
   Murmushi yayi yace "Lafiya ƙalau, shine jiya dana dawo nace kizo mu kwanta kikaƙi ko"
  Ya faɗa yana ƙoƙarin saka laɓɓansa a wuyanta, tsigar jikinta ce ta tashi tace "No ba haka bane dama..." muryartsa sarƙewa tayi jin yadda yake mata wasu abubuwan ta kasa ƙarasa maganar.
    Ɗan turesa tayi tace "Wallahi Yaya yanzu ko kaɗan naga kamar baka da kunya"
Ƴar dariya yayi wacca ta ƙara fito da ainihin kyansa yace "Dama ai bani da kunya inhar akan matar dana aurace, kawai dai baki sani bane saboda kinsan lokacin baki zama mallakina ba"
   "Hmmm" kawai tace tana ƙoƙarin barin ɗakin, "Dakata" yace mata tsayawa tayi cak tamkar ta rusa ihu haka takeji, gani take ta jawa kanta saida Mommynsu tace ta bari Uti yakai masa amma tace ita zata kai masa saboda yadda zuciyarta ta kwaɗaitu da ganinshi, dan baccin datai jiya ba abunda take face mafarkinsa.

  Cikin muryar shagwaɓa tace "Yaya wallahi inhar haka zakaimin zan daina zuwa inda kake"
  "Hmmm lallai yarinyar nan, aiko da mala'iku sun wuni suna tsine miki, oya zoki shafamin mai"
  Dafe ƙirjinta tayi haɗe da zaro idanu tamkar yana ganinta tace "Ni?"
"Ke kika ba Azmah numbernta?" ya jefo mata wannan tambayar.
  Gaban Zuhra wani irin faɗuwa yayi tai saurin waigowa tana kallanshi tace "Azmah kuma?" ta faɗa tana ƙoƙarin danne kishin daya taso mata lokaci ɗaya.
   Ɗaga mata kai kawai yayi ya maida hankalinsa wajan shafa Lotion ɗinsa, ɗan kallanta yayi da wutsiyar idanunsa yace "Ita ta tasheni daga bacci so ganin bazata daina kirana ba yasani kashe wayar gabaki ɗaya"
   Shiru Zuhra tayi a hankali ta taka har zuwa wajan Bed ɗinsa tare da kafe wayarshi da kallo, badai har yanzu Azmah bata manta da Ya Saninta ba, me take nema a gunshi datake bibiyarsa haka alhalin tasan *MIJIN ƘAWARTA* ne, ta shiga uku yaya zatai duk ranar data gane cewar har yanzu Azmah zuciyarta babu kowa sai Ya Saninta, hawayen dake ƙoƙarin sauka akan kuncintane yasata saurin sharewa tanaso ta dake, tana ƙaunarshi sosai bataso yayi sharing soyayyarta ga wata ɗiya mace, mai yasa Azmah zatai mataa haka danme yasa bazatai haƙuri dashi ba tunda tasan Ya Sani mallakinta ne, mai yasa wasu matan ko kaɗan kansu suka sani.

  Jin hannunsa a kafaɗarta yasata saurin lumshe ido tana ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin datake ciki, juyowa da ita yayi suna fuskantar juna yana kallan hannunta data ruƙe wayar tasa, cikin sanyin murya yace "Kunna wayar"
  Ba musu ta kunnata, amma har yanzu gabanta bai bar faɗuwa ba, ɗan dakewa tayi tace "Yaya mai tace maka?"
  Ɗan murmushi yayi ganin yadda duk yanayinta ya canza, haɗe fuska yayi tamkar da gaske yace "Eh to ta kirani ne akan dan Allah ba aureta sannan kuma tana so na..."
  Irin rungumar datai masane yasashi kasa ƙarasawa, ba abunda ƙirjinta yake sai bugawa hakan ba ƙaramin mamaki yaba Muhammad ba, ƙara ƙanƙameshi tayi idanunta a runtse tana sauke wata irin ajiyar zuciya kamar mai Asthma, tausayinta ne yayi mugun kamashi, kiran sunanta yake amma taƙi ansawa tanaso zuciyarta ta daina mata wani iri raɗaɗi datakeji a cikin zuciyarta.
   Ɗago da fuskarta yayi daga jikinsa yana ƙarewa kyakykyawar fuskarta kallo, ƙara rufe fuskar tayi sai ganin wasu siraran hawaye yayi.

    Kallanta kawai yake babu ƙauƙaƙƙautawa wata irin wutar son tane ke ruruwa cikin zuciyarsa, a hankali ya saka harshensa cikin bakinta ya fara yi mata wani irin salo, duk da bata maida mishi amma hakan yayi masa ganin yadda batai yunƙurin hanasa ba kamar yadda ta saba, saidai idanunta a kulle suke gam.
    A hankali numfashinta ya fara daidaituwa, wani irin bacci mai daɗine yayi awon gaba da ita, kafin kace me har ta fara bacci, murmushi kawai yayi ya kwantar da ita tare da gyara mata kwanciya akan Bed, tashi yayi ya saka kayansa yana mamakin wannan sabon salon kishin daga matarsa, babu faɗa saidai zata wahalar da kanta, kallan sama yayi yace "Allah ina roƙonka karka samin soyayyar wata ƴa mace bayan ta Faɗima daka sakamin" cigaba yayi da shirya kanshi yana maijin sonta da ƙaunarta.
   Zama yayi ya janyo Stool ɗin data harhaɗa mai Breakfast yanaci a hankali, amma hankalinshi gabaki ɗaya yana kanta, cikin natsuwa ya kammala tare da ɗauko Keys kan Mirror ya ja mata ƙofar ya fita dan zuwa ganin Baffah.
   A hankali yake tuƙinsa haka kawai ya tsinta kanshi cikin farin ciki na hango tsantsar kishi a idanun Faɗimarsa, cikin natsuwa ya ƙarasa anguwar yayi parking motarsa ya fito ya nufa Flat ɗin.
   Tura ƙofar yayi ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama, ganin wata a kujera yasashi girgiza kai a tunaninsa ko wanine ya kawo mace ganin baya gidan yanzu, duk da har yanzu basusan inda yake ba dagashi sai Baffah sukasan komi, domin kuwa Baffah ne ya roƙi alfarmar akan a ɓoye lamarin lokacin bayyanar hakan bayyi ba.
   A hankali ya fara tafiyarsa cikin natsuwa ba tare daya kalli inda wannan macen take ba.
   Azmah ganin Muhammad Alee yasata shagala da kallanshi, ganin yadda ya ƙara yi mata kyau matuƙa ga wani irin gogewa da fatarsa da ƙarayi sai sheƙi takeyi.
   Miƙewa tayi tana so ta dakatar dashi amma yanayin datake ciki na shauƙin ƙaunarsa ta hanata yin magana, gani zai ɓacewa ganinta yasata saurin faɗin " *Muhammad Alee* " ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi mai matuƙar tsada.
  Tsayawa yayi cak mamaki ya cikashi yana tunanin wacece wannan har haka.
   Ganim yaƙi juyowa yasata tashi cikin sassarfa ta ƙarasa inda yake tana murmushi duk da ta rame amma yanzu ba sosai ba ta ciko kuma kyanta ya ƙara bayyana.
    Ɗan turo mai baki tayi cikin muryar shagwaɓa tace "Tun ɗazu nake jiranka, kuma kana zuwa saika wuceni"
   Ta faɗa tare da rausayar fa kanta tana kallanshi cikin wani irin sex style.

   Ɗan kallanta yayi yanaso ya tuna a ina yasan fuskar amma ya kasa tunawa..
  Katseshi tayi da cewar "It's me Azmah Abdul-Jabbar" ta faɗa fuskarta cike da annuri na ganinshi kawai datayi.
   Kallanta yayi sosai da fararan idanunsa yace "What" ya faɗa yana yatsina kyakyakyawar fuskarsa, baisan hakan da yayi ba ƙaramai kyau tayi ba.
  Ɗan shagala tayu da kallanshi ta buɗe baki zatai magana......

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now