page 7

287 23 2
                                    

*Kuyi haƙuri da rashin posting ɗin da banayi yanzu, hidindimu ne suka sha kaina ba kaɗan ba, ina cikin busy ne kwana biyu gobema biki nake dashi amma nace bari na daure nai muku kar kuce ina ja muku aji da yawa🥴, ku cigaba da haƙuri dani, da zaran mun kammala bikinnan insha Allahu zan runƙa antaya muku posting babu ƙaƙƙautawa, son so fisabilillah my fans💜❤️*


Azmah tunda suka kaita wani gun babu wanda ya ƙarabin ta kanta, haka kawai ta tsinta kanta dason ganin wannan Ogan nasu, shiru tayi tana kallan inda take, tabarma suka shinfiɗa mata a jikin wata bishiya daga haka kuwa ba abunda suka ƙara yi mata, ba abunda ta tuna sai Zuhra, a halin yanzu tana tsananin buƙatar Zuhra, tanaso ta faɗa mata irin jarabawar da Allah yayi mata na son Muhammad Alee, lumshe idanunta tayi ba tare data lura ba saiji wasu zafafan hawaye tayi masu ɗumin gaske, tunani take mai taiwa Allah har haka da yakeso ya hukuntata da wannan zazzafar soyayyar data shiga naɗan lokaci ƙanƙani, rungume jikinta tayi da hannayanta jin iska na kaɗawa alamun tanajin sanyi ba ɗan kaɗan ba kasancewar muna lokaci na sanyi.

    Zuhra tunda ta shiga ɗaki har yanzu da dare yayi taƙi fitowa kuma ta kasacin komai a bakinta, tunanin Azmah take akan kar suyi mata mugun abu, runtse idanuwa tayi tana sauke wani irin numfashi mai ban wahala, wayar dake hannunta ta kalla ta ƙara kiran layin Azmah amma kalmar ɗayace itace a kashe, jin an buɗe labule yasata cigaba da kallan ƙasan da takeyi dan duk a tunaninta mahaifiyarta ce, mahaifinta ne ya shigo ɗakin sallama ɗauke a bakinsa, ba tare data kalleshi ba ta amsa hawaye na sauka akan kuncinta wani nabin wani, shiru ne ya biyo baya naɗan wani lokaci sannan mahaifinta yace "Zuhra akan Azmah zaki hana kanki sukuni yau?, donme zaki damu kanta alhalin kinsan suɗin azzalumai ne, kome ya faru da Azmah mahaifinta ne yaja mata dan haka ki manta da komai ni nasan mahaifinta zai ƙwatota nan da wani lokaci ƙanƙani"
   Hawaye da suka tsaya kan eye lashes ɗinta ne yasata ganin dishi-dishi, gogewa tayi da bayan hannunta tare da ɗauko Hand Kerchief ta goge fuskarta gabaki ɗaya dashi, ta ɗauki minti a ƙalla zaikai biyar tana sauke wata irin ajiyar zuciya sannan ta kalli mahaifin nata, cikin dishewar murya tace "Daddy inaso ka sani duk abunda kuke ƙoƙarin yi nakan saurin aikatashi kafin ku kuje ga haka, ba komai yasa na shiga jikin Azmah saidan na ɗauki fansa a kanta, amma saina fuskanci wasu kyawawan halayya game da Azmah wanda babu ko ɗaya na halin mahaifinta data ɗauko, Daddy Azmah bata sanni ba, batasan ko ni wacece ba ta karɓeni da hannu bibbiyu kuma ta taimakamin ba tare da ko sisi na ba, samun masu hali irin Azmah yana da matuƙar wuya a wannan lokacin, tana son talakawa, macace mai ƙoƙarin taimako bata ɗauki rayuwar da komai ba, muddin basu saki Azmah ba Daddy bazan iya taɓuka komai ba game da fansar da mukeson ɗauka nan gaba" shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya wasu hawayan na faman zurya a kuncinta, runtse idanunta tayi jin labarin datake yawan ji game da ƴan kidnapping cewar inhar mace tai musu sukan keta mata haddi ba abunda ya shafesu, sauri tayi ta buɗe idanunta da suka sauya launi tana maida numfashi.

    Sun ɗauki lokaci mai tsayi ba wanda yacewa kowa uffan, mahaifinta yasanta sosai tana da wata irin zuciya wacca batada yafiya ko kaɗan bata manta alkhairi ko sharri ko yaya yake, tabbas daga yau yasan Zuhra ta aje makaman ɗaukar fansarta har sai anga Azmah kamar yadda ta furta.
  Baice mata komai ba ya tashi yabar ɗakin yana jinjina kai yana mamakin me Azmah taima Zuhra haka dahar akanta take ƙoƙarin aje makaman yaƙinsu wanda sukasha wahala kafin su samesu.

   Zuhra bin mahaifinta tai da ido saita tsinta kanta da rashin jin daɗin kalaman datayi, tabbas suna sauri ne, kota batai tsamamni zasu ɗauki wannan lokacin ba tare da sunyi abunda ya kawosu ba sun tafi, kallan wayarta tayi datake haske tana duba mai kiran taga Fahad ne, kasa ɗaukar wayar tayi dan batada kuzarin da zata ɗauki waya suyi magana.

*Washe gari*
   Ganij yanayin garinne ya tabbatarwa da Azmah asuba tayi kamar ma harta wuce tunda ko kaɗan bataji kiran sallah ba kuma masu gadin nata bata ga alamun suna Sallahr ba, miƙewa tayi tana tattaɓa jikinta jin yadda yayi mata tsami sosai ga rashin wadatacciyar bacci datayi ga kuma rashin makwancin me kyau, ya mutsa fuska tayi ta ɗan samu taja Veil ɗin dake jikinta ta ƙara lulluɓe jikinta dashi, inda suke ta nufa muryarta a dishe tace "Ruwa nakeso zanyi alwala"
  Saida suka ɗauki lokaci mai tsayi kafin wani ya tashi yaje ya ɗauko mata pure water guda ɗaya ya miƙa mata, dan bazasu manta irin warning ɗin da Ogan nasu yayi musu ba akan idan lokacin sallah yayi su runƙa bawa baƙi ruwan yin alwala, karɓa tayi tana tafiya tana rangaji ba abunda take ayyanawa a ranta sai yadda za'ai ta saci wayar ɗaya daga cikinsu ta kira Zuhra ta bata labari, har ta gota wannan Bukkar ta hangoshi yana zaune yana lazimi ga dukkan alamu sallar ya idar, batasan lokacin data shagala da kallansa ba, jin motsin mutum a bayanta yasata saurin barin wajan ba tare da ta waigo ba, Baffah bin ƙugunta yayi da kallo tate da haɗiye Saliva yana ƙiyasta kyau irin na wannan yarinyar, ba abunda yake ayyanawa a ransa sai Allah ya bashi dama Ogansu yayi nisan kiwo ya hayyaƙe mata saidai duk abunda zai faru ya faru. 
  
Waigawar da zayyi suka haɗa ido da Muhammad sauri yayi zaibar wajan ya dakatar dashi, cikin takunsa na ƙasaita yazo inda yake tsaye, cikin daddaɗar muryarsa yace "Kar naji kar nagani, inba haka ba ranka wannan karan zayyi mummunan ɓaci" bai jira cewarsa ba ya koma inda yake yanaso gari ya gama washewa ya shiga cikin gari.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now