page 23

256 19 15
                                    

Shiru yayi naɗan wani lokacin kafin ya ɗago dakai yace "Alhaji fa doguwar suma yayi ayi gaggawar kaishi asibiti karmu rasashi"
  Kowa saida ya saki ajiyar zuciya musamman ma Fahad, cikin gaggawa aka sukunceshi ba inda aka zarce dashi sai cikin mota, direct asibiti suka nufa dan duba lafiyarsa.
  
Azmah ɗan zare ƙaton Glass ɗin dake mabne a fuskarta tayi, murmushi shinfiɗe a fuskarta ta kalli ƙawarta tace "Zuby wallahi ban taɓa tsammanin bazan iya rabuwa da wannan guy ɗin ba, saidai na ɗauki alwashin mallakarsa kota wata irin hanya domin bazan tsaya ina kallon ruwa ba kwaɗo yayimin ƙafa, ya zamarmin dole na ɗauki ƙwaƙwaƙwarar mataki"
   Ɗan murmushi wannan budurwar tayi wacca aka kira da Zuby tayi tace "Na nuna miki hanya mafi sauƙi kince ke bazaki iya zuwa wajan Boka ko Malam ba, to ga shawara mafi sauƙi amma saidai bazaki taɓa mallakarsa ba a matsayinshi na mijin auranki, saidai duk wani jin daɗi da ma'aurata zasu kasance kema zaki iya kasancewa dashi"
  Azmah zaro idanu tayi tace "What?, kina nufin mu runƙa aikata Zina dashi?" ta tambayeta hankali tashe.
  Zuby tace "Ƙwarai haka nake nufi inba wa ƴannan ba gaskiya banda wata hanya mafi sauƙi, kuma ko wata hanya kikabi inhar ba bin Malamai ba ko Bokaye to wallahi ko kin auresa bazaki taɓa jin daɗin auranshi ba saboda tun farko baya sonki baya ƙaunarki"
   Shiru Azmah tayi naɗan wani lokaci sannan ta numfasa tare da cewa "Amma in banda abunki to tayaya kike tunanin zai haɗa jiki dani alhalin naga ko kaɗan babu ɗigon soyayyata a cikin zuciyarsa"
  Dariyar jin daɗi Zuby tayi tace "Karki damu, kedai kibarmin komai a hannuna, akwai wani sabon Cingum daya shigo, ba kowa bane yasan akwai wani babban sinadarin janyo hankalin ɗa namiji zuwa ga Sex ba, da zaran ya tsaya a gabanki kina cin wannan abun angama hajiyata, yana janyowa mace sha'awa sosai haka zalika maza, amma mayaudaran maza sunfi amfani dashi wajan bawa budurwar dataƙi aminta dasu"
  Sakin baki Azmah tayi tace "Da gaske kike ko wasa?, tayaya Cingum zayyi wanin aikin ko akwai tsafi a jikinsa ne?" ta tambayeta tamkar wata sokuwa, maganar ba karamin bawa Zuby dariya tayi ba tace "A'a, sinadarin bature kenan, kedai idan har kinason hakan baki da matsala dani"
  Gyaɗa kanta tayi tare da kafe wani wuri da kallo tace "Tabbas inason kasancewa da Muhammad Alee, saidai naga koda wasa bazai taɓa aurena ba, idan har ina tare dashi ba abunda zuciyata take ƙwadaituwa dashi sai in kasance ina faffaɗan ƙirjinsa, inhar hakan zai yuwu Zuby a shirye nake don ganin na bashi Virgin ɗina"
Miƙewa gabaki ɗayansu sukai suka fara tafiya Zuby tace "Baki da matsala da hakan, saidai ki tabbatar kinsan yadda zaki don ku kasance a ɗaki ɗaya, sannan zan baki wata shu'umar Humra idan Cingum ɗin bai yuwu ba to ina mai tabbatar miki Humran nan zatai masa aiki yadda bakya tsammani"
  Jinjina kai tayi haɗe da yi mata godiya tana mai jinjinawa Zuby idan ka ganta saika rantse wata ustaziyya ce saboda yadda take da kamun kai da kunya a zahiri amma a baɗini kuwa shu'umar kanta ce.

*_🤙🏼Hattara ƴan mata harma da samari wanda zaku ga Sugar Mommy na ƙoƙarin sakasu a halaka, wannan cingum ɗin gaskiya ce ba ƙarya ba, tabbas anyi shi kuma ana cigaba da yaɗawa cikin al'ummar musulmai, dan Allah ƴan mata a guji cin abun hannun saurayu duk yadda kuke dashi koda kuwa gobe za'a ɗaura miki aure dashi, domin kuwa wasu mazan basu da imani ko kaɗan da sun ƙwallafa rai akan sunason su sameki zasuyi duk abunda zasuyi dan ganin sun samu mace cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba, haka zalika this Humra is real tana matuƙar hallaka maza dan Allah mu runƙa yawaita yin Azkar domin neman tsari daga Allah, Allah yasa mu dace_*

Alhaji Bashir Iyan Tama yana kwance a asibiti, ɓarin jikinsa ya daina aiki saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, ga bakinsa ya karkace yanaso ya faɗi abu mai muhimmancin amma baya iya faɗa saboda yadda Paralyzed ɗin tai masa mugun kamu lokaci guda, Fahad yana zaune dashi hannunsu saƙale dana juna yace "Please Daddy, kai ƙoƙari ka faɗamin abunda kakeao ka faɗa"
  Shiru yayi yana zubda hawaye so yake yacewa Ahalansu su gudu domin kuwa yasan tashi ta ƙare kuma Ahalan Muhammad Alee bazasu taɓa ɗaga mishi ƙafa ba, gashi sun ƙwace duk wata dukiya da sukeji da ita kuma suke taƙama da ita yanzu sun karɓe ba tare dayayi aune ba, yasan tabbas shida Fahad tasu tazo ƙarshe hakan yasa yakeso ya shaidawa Fahad ya gudu amma babu halin yin magana Ubangiji ya rufe bakin gum.
   Ɗan ƙara damtse mai hannu yayi yana faman girgiza mai kai amma ko kaɗan Fahad bai gane me yake nufi ba.
   Haka rayuwar Alhaji Bashir ta kasance cikin asibiti ba Uhmm ba Uhm, uhm tare da jiran tsammani daga iyalan Muhammad Alee.
   Fahad kuwa ya nemi Zuhra ta ɓace ɓat tamkar anyi ruwan sama an ɗauke dan koda wasa yanzu baya samunta koda kuwa yaje gidansu ne, saidai ya gaji da tsayuwa ya tafi yayinda ya hango tsantsan ƙiyayyarsa a idanun Mahaifin Zuhra, kullum cikin kiran wayanta yake amma ko kaɗan bata shiga, hakan ba ƙaramin jefa Fahad yayi cikin gararin rayuwa ba.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now