Page 36

203 21 11
                                    

Tun safe har yamma abu ɗaya ake har yanzu Azmah bata haihu ba, hankalin mahaifiyarta yayi matuƙar tashi domin tun tanajin ihunta har ta gaji tai shiru ta kasa cewa Uffan, sai ambaton Allah data keyi a cikin zuciyarta, tabbas duk wanda yaga Azmah a halin datake duk rashin imanin mutum saiya tausaya mata, ana ƙoƙarin shiga da ita ɗakin Theater kenan Azmah ta fara jijjaga kafin kace me ta fara tsinkau-tsinkau, da taimakon Allag da taimakon likitoci sukai saurin yi mata duk wasu abubuwa da abun zai tsayar, wani irin nishi tai wanda batasan daga inda ya fito ba domin ƙwaƙwƙwaran numfashi bata iyayi, sai gashi Allah ya taimaketa tai wani irin nishi saiga santaleliyar yarinyarta ta faɗo, jin jaririyar batai kuka ba yasa likitocin bugunta saida ta ɗauki wasu lokuta sai Babyn ta tsandare da ƙara ta fara kuka tana wawurar hannun tana sakawa a bakinta, hamdala aka farayi ganin Babyn ta fito cikin ƙoshin lafiya,saidai mahaifiyar Babyn ta kamu da cuta na Yoyon fitsari sanadiyar dogon naƙudar data ɗauki lokaci tanayi.
   Nan aka miƙawa mahaifiyar Azmah Babyn likitocin suka duƙufa akanta don ganin ciwo kar yayi yawa a cikin jikinta,bayan an mata allurar tsaida jini, nan suka gyarata haɗe da Babyn, bayan sun mata ɗinki domin kuwa ba ƙaramin karuwa tai ba sannan suka  saka mata robar fitsari, tun tanajinsu sama sama hartakai da tai suma ba tare da sun lura datayi ba, nan suka ɗan bubbugi fuskarta ta farka domin kuwa ko kaɗan ba'a buƙatar datai bacci a wannan lokacin.

    Kasancewar tun dare ake ta malala ruwa hakan yasa safiyar yau garin tsit kowa ba gida don kuwa ruwan bai gama ɗaukewa ba, Azmah tana cikin Blanket ta lafe a jikin Muhammad jin yadda take jin sanyi sosai, rungumeta yay tsam yace "Ga dukkan alamu yau Babyna batason sanyi tun dare kin kasa sukuni"
  "Uhm" kawai tace dan bazata iya magana ba saboda yadda taji jikinta na karkarwa.
   Jin ta farajin ɗumin jikinsa ne yasata ƙoƙarin cewa "Ya bari naje na haɗa maka BreakFast"
Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi, rungumo da ita jikinsa ya ƙarayi yace "A'a ba inda zaki kina fama da kanki, nifa lafiyarki ta fimin komi a rayuwa"
  Dawowa tai ta kwanta duk da tana matuƙar jin yunwa itama, a kwanankinnan ba ƙaramin cin abinci take ba, kallanshi tayi ta yatsina fuska tace "Wallahi cikina yunwa yakeji"
   Ƴar dariya yayi wanda ya ƙara fito da ainihin kyanshi yace "Bari naje na haɗo miki koda Tea ne" miƙewa yayi harya kai baƙin ƙofar fita yaji tana cewa "Please Yaya inason ɗumaman Tuwonann..." bai bari ta ƙarasa ba ya tuntsire da dariya yace "Wallahi yanzu kin koyi cin tsiya, shiyasa sai hawa kike, nidai ba ruwana kikai kiɓa ahto"
   Hararar wasa ta balla masa ta koma cikin Blanket ɗin tace "Nidai kai nake jira, ba dole na koyi ci ba ga fitinarka gata Babynka datake damuna da motsi yanzu"
  Murmushi kawai yayi ya fita yana maijin son matar tasa.

   Fahad yana ƙokarin shiga ma'aikatarsa yaga Joseph na nufo sa, tsayawa yay yana kallanshi yanaso ya tuna inda ya sanshi, nan taje ya tunashi, cike da girmamawa ya gaishe dashi, amsawa yayi cikin sakin fuska, ya buɗe baki zai koro masa jawabi na kwana biyu dayay tafiya ba tare daya aiwatar da aikin daya sakashi ba akan Muhammad Ali, Fahad yay saurin ɗaga mishi hannu, fuskarsa ɗauke da yalwataccan murmushi yace "Aikin dana sakaka inaso a sokeshi, yanzu Alhamdulillah na gane duk wasu kura-kuran danake nagode ƙwarai,amma inaso na tunatar dakai wani abu,duk wanda ya ɗauki ran wani to kasani Allah bazai taɓa yafe masa ba,duk da nasan kasani kaima a cikin littafinku mai tsarki wato Bible, kaje ka nemi aikinyi ka zubda duk wa su mugayan ayyuka dakasani kanayi, in baka samu aiki ba kazo nan insha Allahu zan baka aiki" bai jira cewarsa ba ya ja motarsa ya shiga wajan harabar da ake Parking.

  Joseph ya daɗe a tsaye yana bin motar da kallo,maganar Baffah ce ta faɗo masa arai lokacin da suka haɗu a ƴan kwanankinnan yake shaida masa yayi tafiyane yaje ganin dangi jan Yola hakan yasa kwana biyu yajishi shiru "Joseph ina maka sha'awar musulcin tun ba  yanzu ba,kamata yayi ka daina biyewa su Modibbo tunda har kaga azal ɗin data faɗa musu na hukuma data cafkesu, wannan damace a wajanka ka zama mutumin kirki sannan ga rahamar Allah nan tana tafe kusa dakai ka zama cikakkan musulmi to tabbas ka samu ribar duniya sannan data lahira, mu yawaita Istigfari na neman tuba wajan Ubangiji akan zunuban da muka ɗibarwa kanmu, karka ɓatawa kanka lokaci wajan neman Muhammad Alee,domin kuwa tabbas idan har ina raye da yardar Allah bazan taɓa barin ka cutar dashi ba, domin kuwa Muhammad Alee mutum ne da duniyarmu ke buƙatarsa" numfasawa Joseph yayi ga kuma maganar da Fahad ya faɗa masa yanzu.
  A hankali ya fara takawa har ya bar ma'aikatar.

   Tabbas musulcin tun yau na burgesa, idan yay la'akari da baida kowa a wannan duniyar baisan wani nashi ba, shidai ya tasone yana garararba akan Titi tare da addinin Christian a tattare dashi, tabbas yanaso ya canza rayuwarsa ya zama mutum tamkar kowa, ya daɗe a tsaye yana kallan wani masallaci dake wajajan ma'aikatar babban masallaci ne, kallon mutanan gurin yayi dayaga kowa yana alwala suna ƙoƙarin shiga masallacin suyi sallah, murmushine ya suɓucewa Joseph ya zauna can nesa da masallacin harya jira aka idar, wani ya samu akan yanason ganin Imam ɗin masallacin nan take aka kaishi, bai tsaya wata-wata ba bai ɓatama kanshi lokaci ba ya sanar da Imam ɗin buƙatarsa na yanaso ya musulunta, jin kabbarar Liman yasa wa ƴanda ke ƙoƙarin barin gun suka tsatstsaya sunason suji maiya sakashi yin kabbara cike da jin daɗi da nishaɗi, nan ya sanar da mutanan wajan  buƙatar Joseph sosai aka tayashi murna wasu suka fara bashi kyaututtuka, nan take ya amsa kalmar shahada ya zaɓi sunan da yakeso yace yanaso a saka mishi Aliyu, nan ma saida akai kabbara, sosai Imam yayi mishi bayani yadda zai fahimta, haɗe da wankan tsarkin da zayyi na shigowarsa musulunci.
   Duk ya fahimta bayanansa kasancewar yay rayuwa sosai da musulmai, fitowa yayi daga masallacin yanajin wata irin iska mai rahama tana shiga ko wani sassan jikinsa, hamadala yayi tare da godewa Allah S.W.A.
    "Congratulation Aliyu ina tsananin tayaka farin ciki na shiga addinin gaskiya da kayi" Fahad ne ya faɗa haka hannunsa saƙale a ƙirjinsa yana jifanshi da wani irin kallo mai nuna tsantsan murna da farin ciki.
Joseph rungume Fahad yayi yana mai zubda hawayen farin ciki yace "Nagode, nagode da kuka fahimtar dani addinin gaksiya tun kafin na rasa raina ya tashi nazo duniyar a banza na koma a hofi, tabbas ina alfahari daku"
  Murmushi ne shinfiɗe a fuskar Fahad yace "Babu komai Aliyu, hakanma ka godewa Allah dayasoka da Rahamarsa, ina maka albishir zan ɗaukeka aiki a ma'aikatarmu koda kuwa bakai karatu ba, akwai aikin da zan baka wanda zaka runƙa ansan salary ɗinka da gwaɓi-gwaɓi"
   Godiya sosai Joseph yayi yana maijin farin ciki a ransa, a haka suka jera shida Fahad suna hira sama-sama tamkar sun saba da juna.

Kuyi maneji yau banda caji

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now