😂🤣😂 kunsan maiya ban dariya?, yau mutane sun saki jiki zan hada Zuhra da Muhammad Alee haba abun yayi wuri da yawa kudai ku cigaba da bibiyar littafin Muhammad Alee tare da sambaɗo comments da Votes naga bakwasan yimin commets da Votes ƴan wattpad ɗinnan😒
*Assalamu Alaikum, ina muku albishir da maganin sanyi wato infection idan zaku siya maganine me kyau kuma mai ingancine, sahihin maganin sanyi wanda inhar akwaishi a jikinki da yardar Allah zai miki magani cikin lokaci kanƙani,matan aure sunasha, ƴan mata suna sha, haka zalika yaran da suke fama da matsalar sanyi suma zaku iya basu, maza suna sha, gaskiya ɗaya zan iya faɗa muku shine maganin nada kyau, karku tsaya sanya maza garzayo wajan Mum Irfaan domin siyan maganin sanyinki a hannu, siyan ɗaya zakiyi koko sara zaki duk akwaishi, sannan akwai man gashi na al'arabee mai saka tsahon gashi, tsayin gashi, taushin gashi, cikar gashi uwa uba yana maganin dandruff me kike jira ƴar uwa maza tuntuɓi Mum Irfaan domin siyan ingantattatn maganin sanyinki haɗe da Man kitso da sauran abubuwan gyaran jiki, in kina da buƙata zaki iya tuntubata ta wannan numbern 08130515037 plz idan baki shirya ba karkimin magana mu ɓatawa juna lokaci*
Ta daɗe a ɗakin tana tsoron buɗe idanunta, ba abunda hancinta ke shaƙar mata sai daddaɗan turaran da yake sawa, a hankali ta ware idanun nata ta saukesu a ɗakin, ɗan waro manyan idanunta tayi tana kallan ɗakin, babu kowa a ɗakin sannan an ɗauki wasu abubuwa da dama a cikin Bukkar ga dukkan alamu gaba sukaci bazasu ƙara waiwayar gun ba, batasan lokacin data zube ƙasa ba kan cinyoyinta tare da wata irin ajiyar zuciya tamkar itace ajiyar zuciyarta ta ƙarshe a duniya, wannan karan ta dake bata zubda hawaye ba, saidai tabbas da zatai hawayan a wannan lokacin sai tafijin daɗi fiye da yadda takeji a cikin zuciyarta, ji take tamkar wacca zata kamu da Heart Attack ba abunda zuciyarta take yi sai harbawa da ƙarfi tamkar wacca ta samu tangarɗa a cikinta, tashi tayi murmushi ɗauke a bakinta tanaso ta gasgata Azmah amma zuciyarta na ƙaryata zancan, turaran da yake sakawa yana mata kamanceceniya da nashi duk da ba ƙamshinsu ɗaya ba da akwai bambanci sosai a tsakaninsu, ɗakin ta fara bi da kallo tanaso ta tabbatarwa da kanta cewar Ya Saninta yayi rayuwa a cikin ɗakin, ba abunda ke yawo a cikin ƙwaƙwalwar kanta sai tunaninninka da dama, zama tayi dirsham a ƙasa tare da yin tagumi ta kafe ƙasa da ido, ji take tamkar tayi rayuwarta a nan jin yadda ƙamshin turaransa ke ratsa ko wani sashe na jikinta, wayar mahaifin Azmah ta ɗauko ta kira layin da sukai waya amma sai taji layin a kashe, sosai takeso ta danne zuciyarta akan yadda takejin wani abu amma ta kasa, haƙura tayi ta saki kukan data danne ko zata samu sukuni a cikin zuciyarta, wasu irin hawaye take fiddawa masu matuƙar ɗumi ga jikinta shima lokaci guda ya ɗauki zafi ga dukkan alamu zazzaɓi ne me zafin gaske zai rufeta, ta ɗauki awa a ƙalla zayyi biyu a gurin saidai ba abunda take jin sauti sai kukan tsintsiye, ganin yamma na ƙoƙarin yi yasata tashi ta ƙara gwada kiran Numbernsa amma amsar ɗayace itace numbern a kashe, a fusace tayi wurgi da wayar ta fara kuka tana jujjuya kanta jin yadda ciwon kai yayi nasarar damƙarta lokaci ɗaya, fitowa tayi a Bukkar tana gudu tana kuka tamkar wacca akace ma iyayanta sun rasu, a haka har ta fito bakin Titi ta tsaida Taxi tahau, tana faman jin zafi cikin zuciyarta.
Baffah kallan Zoben dake hannun Kamal yayi yace "Waya baka wannan Zoben?"
Ya faɗa yanaso ya anshe dan ya tabbatar wannan Zoben zayyi tsada, ɗan ɓoyewa yayi yace "Tsakanin wacca muka sata da wacca ta kawo kuɗi ne suka yardashi, dan inda suka tsaya wajan bishiyarnan anan naganshi yana kashemin ido" ya faɗa yana mai faɗaɗa murmushi a fuskarsa.
Baffah haɗe fuska yayi yace "Banshi"
Kamal sauri yayi ya ɓoye yace "Kamar Ya?"
Tashi Baffah yayi yana ƙoƙarin ƙwacewa saiga Muhammad Alee ya fito daga Bathroom hannunsa ruƙe da Towel yana goge wa ga dukkan alamu daga wanka ya fito, ganin shi yasa Baffah komawa ya zauna yana cewa "Wallahi zaka banshi dan dolene" dan tunda ya ƙyalla ya tabbatar da cewar Zoben zayyi kuɗi.Kamal sanin halin Baffah ne yasashi miƙewa ya nufa inda Muhammad Alee yake dan bashi Zoben ya ajemai dan tas Baffah zai iya murɗesa ya ƙwace, yana tafiya Baffah na galla mai harara, Muhammad Alee baice musu Uffan ba, dan inda sabo ya saba, yana zaune gefen gado yana gogge kanshi, jin Kamal ya tsaya mai aka yasashi ɗan kallanshi tare da kauda kanshi gefe.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...