page 16

240 25 5
                                    

Shiru ko wannansu yayi bayan sun gama zayyane masa iya abunda suka sani, "waca anguwa ya ɗauko yarinyar kukace?" ya faɗa yana kafe Modibbo da fararan idanunsa, ƙara maimaita masa yayi, kallan Baffah Muhammad Alee yayi yanaso ya tabbatar da abunda zuciyarsa take ce masa, muryar Modibbo ce ta katse mai tunaninsa ta hanyar cewar "Gaskiya daga gani masoyane na usuli hasalima shi baisan muna binsa ba itace tai gaggawar sanar dashi, dan daa wannan Titin anguwar suka so su shigo ganinmu yasa tace su tafi gida"
   Numfasawa yayi jin maganarsa ta ƙarshe, don da harya fara zargin kosu Zuhra da gaske suna gidansu dake cikin Kano, jin cewar Budurwar da Fahad ya ɗauko Girl Friend ɗinsa ce ya tabbatarwa da kanshi ba Zuhra bace domin yana da tabbacin koda wasa bazata taɓayin soyayya da ahalin Bashir Iyan Tama ba, alamu yayi masa dasu bar wajan, ba musu ko wannansu yabar wajan ya zamana daga Baffah saishi zaune a Parlourn, haka kawai zuciyarsa ta kasa samun sukuni, kallan Baffah yayi yace "Ka ɗauko Keys ɗin gidannan inason zamuje yau"
Ba musu ya amsa da "To" tare da barin gurin dan zuwa aikin da Ogan nasa ya sakashi.

Ba abunda zuciyar Muhammad Alee sai wani irin bugu tsoro yake kar ace Zuhra suna soyayya da Fahad domin ɗaukar fansa, shi sam wannan fansar batai mai ba tayaya da auransa akanshi take mu'amala da kamar Fahad wanda ya tabbatarwa da kanshi cewar Fahad ya wuce duk wani tunanin mai tunani, lumshe idanu yayi tare da dunƙule hannunsa hankalinsa sam yaƙi kwanciya, gani yake ma Baffah zamansa yayi ba ɗauko Keys ɗin yaje yi ba, cikin sassarfa ya shiga Bedroom ɗin da Baffah yake saura kaɗan suyi karo da junansu, gani Keys ɗin a hannunsa yasashi cewar "Muje"
  Baffah ɗan ruƙo mai hannu yayi yace "Dakata, wai menene haka kana abu kamar ba namiji ba, menene hakan, please be a Man mana"
  Ɗan kallanshi yayi da idanunsa wanda suka sauya kala saboda tsananin kishi irin na Muhammad, sassauta muryarsa yayi ganin tana neman harɗewa garin yin magana, cikin sanyin muryarsa yace "Idan da Zuhra yake Dating fa inyi Yaya?, kai bakasan ba'a wasa da soyayya ba wajan ɗaukar fansa ba, jikina ya bani Zuhra ce" ya faɗa yana juyawa Baffah baya haɗe da dafa bangon yanajin wani irn kishinta na tashi cikin zuciyarsa.
   Baffah ganin yanayinsa yasashi cewar "To kai waya faɗa maka Zuhra tana Kani bare har ta samu damar yin soyayya da Fahad, kwata-kwata yaushe mukazo da har zasu fara soyayya, kasan akwai abunda zamuyi a gidannan ko, dan haka ba inda zamu dole ka jira zuwa dare ko gobe da safe"
   Wani irin kallo ya jefeshi dashu tare da barin gurin dan yasan halin Baffah tunda ya faɗa haka to tabbas sai zuwa dare ko goben zasu, direct Bedroom ɗinsa ya shiga tare da shiga Bathroom ba tare daya damu ya cire kaya ba ya tsaya a tsaye ya sakarwa kanshi shower yana sauke wata irin ajiyar zuciya, dan har yanzu zuciyarsa sai nanata mishi cewar da Zuhra Fahad yake tare bada kowa ba domin bugun zuciyarsa ya tabbatar masa da haka, lumshe ido yayi yanaso ya daina jin wannan bugawar zuciyarsa amma babu yadda zai iya, kwanciya yayi sai faman juyi yake, lokaci zuwa lokaci sai yayi tsaki dan tabbas Baffah bazai taɓa bashi Keys ɗinnan ba dayau sai ya tafi shi kaɗai.

     Azmah yau cike take da tsantsan farin ciki kasancewar yanzu haka Abdul-Jabbar na gidan yari na tsawon shekara goma hakan yasan mahaifiyarta tattara komi nata dan ta koma gaban iyayanta wato jahar Kano, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba zuciyarta na raya mata ta kusan haɗuwa da Muhammad Alee.
    Cikin murya wacca kanaji zaka tabbatar da tana cikin tsantsan farin ciki tace "Mom yanzu gidannan yaya zamuyi dashi?"
  Harara mahaifiyarta ta maka mata tace "Waike meke damunki ne Azmah, baki ga yadda rayuwa ta sauya mana ba lokaci guda ba, donme ke hakan bai dameki ba, ko kin manta yanzu haka mahaifinki na Gidan Yari, kika sani zai fito ya samemu koko bazai samemu ba, amma saboda ke baki da hankali baki damu da halin da yake ciki ba har wani murna kike akan zamu bar mahaifarki, ina jinki sai faɗawa ƙawayanki kike kamar ba abunda ya dameki"
   Shiru Azmah tayi tana faman sosa ƙeya ba tare data cigaba da haɗa kayan nata ba, ganin mahaifiyartata ta fita a fusace yasata samun damar ƙarasawa tana Allah-Allah su tafi kar dare yayi musu a hanya.
   Ƙarfe biyu Dot na rana suka shirya duk wani abu na buƙata saida suka kwashesu tas tare da kiran dillalai suka siya abunda zasu siya suka bata kuɗinta, wani ta miƙawa Key ɗin gidan tare da zuba komai nasu a Boot ɗin motarta tahau ta shiga ta tayar suka fara ƙoƙarin fita daga gidan sai Jahar Kano.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now