*MUHAMMAD ALEE*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*
*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*04*Nan take mahaifin Azmah yayi mata alƙawarin saka Zuhra a makaranta har saitacd ta gaji, sosai sukai godiya daga Zuhran har Azmah, ita Allah-Allah kawai take ta tashi su tafi saboda taga garin ya fara duhu, ɗan mintsinin Zuhra tayi cikin muryar raɗa tace "Kizo muje kar Mama taimin faɗa"
Miƙewa Azmah tayi tace "Daddy bari mu maida ita gida nida Driver Mamansu tace kar ta daɗe" jin haka yasashi miƙewa shima yace "Ina zuwa bari na kaita saimu dawo tare dake, kinsan banso Driver na fita dake da yamma"
Murmushin jin daɗi tayi ta samu guri ta zauna tare da zaunar da Zuhra tace "Lallai yau kin taki babbar sa'a Daddy ne zaikai ki gida yau da kanshi, cab gaskiya kinzo da goshi"
Murmushi kawai Zuhra tayi ita haka kawai taji jininta bai haɗu ba dana mahaifin Azmah ganin irin kallon dayake jifanta dashi, bai wani daɗe ba sai gashi ya fito, ɗaukar Keys yayi sannan suka fita, Azmah ce a gaba sannan Zuhra ta rakuɓe a baya tamkar mara gaskiya.Sun ɗan jima kafin su ƙaraza gidan saboda irin yanayin tafiyar da yakeyi a hankali, ana zuwa ƙofar gidansu Zuhra Azmah tace Daddy munzo, kallan gidan yayi cike da ɗunbin mamaki yana tunanin wannan wani irin talaucine dasu har haka, bayyi tsamamni talaucinsu yakai haka ba, murmushin cin nasarane ya bayyana a fuskarsa ganin lokacin ƙanƙani zai shawo kan Zuhra dama iyayanta gabaki ɗaya, Zuhra ƙoƙarin fita ta farayi tare dayi musu godiya, dakatar da ita yayi ta hanyar miƙa mata Bundle ɗin ƴan ɗari biyar-biyar, nan take cikinta ya murɗa saboda tsananin fargaba na ganin wa ƴannan kuɗin, kauda fuskarta tayi tace "Nagode Daddy amma gaskiya bazan karɓa ba inba hakaba Mahaifina zaimin faɗa"
Sauri tayi ta fita jin har an fara fitowa daga sallahar magrib ta shiga cikin gidansu, tana shiga direct ɗakinta ta shigaa tai saurin canza Hijab ta ɗauko ƙarami ta fito tsakar gida ta ɗauki buta ta fara alwala dan taji mahaifiyarta na Sallah, jin sallama yasata ɗaga kanta taga Azmah ce, mamaki abun yabata dan ita ta ɗauka sun daɗe da tafiya, kallanta tayi ta maida hankalinta wajan yin alwalarta har saida ta kammala, waigawar da zatai taga ba Azmah jin muryarta cikin ɗakin mahaifiyarta ya tabbatar mata da tana ɗakin, ɗakinta taje tai sallahrta bayan ta idar ne yasata fitowa itama ta shiga ɗakin mahaifiyarta, kusa da mahaifiyarta ta kalla taga wannan kuɗin da aka bata, ɗan ɓata rai tayi mahaifiyarta murmushi kawai tayi tare da cewa "Zoki zauna" ta faɗa tana nuna mata kusa da ita, Azmah hankalinta ne gabaki ɗaya ya tafi akan wata sarƙa data gani agaban madubin Mahaifiyar Zuhra ganin yadda tasan sarƙar inhar ta gasken ce to tabbas tana da matuƙar tsadan gaske, Zuhra ganin Azmah ta maida hankalinta wani gurin yasata saurin duba inda take kalla, ganin tana kallon sarƙa yasata saurin zungurar mahaifiyarta itama ta kalli wajan, rasa yadda zasuyi tayi can sai dabara ta faɗo tace "Oh ni kinga Zuhra na ajiye kayan ajiya anan wajan salon azo har ɗaki a ɗauka na shiga uku"
Zuhra tace "Mama yaka mata ki aje mata kaya dakyau kinga yadda ce yasa ta baki ki ɓoye mata"
Zuhra jin hirar da suke yasata saurin sakin ajiyar zuciya can kuma tace "Mama sarƙannan koma ta wacece ki aje mata shi dakyau tana da matuƙar tsada yanzu by mistake aka ɗauka tayaya zaku biya me shi"
Murmushin karfin haki mahaifiyar Zuhra tayi tace "Insha Allahu zan ajeta dakya"
Azmah ta buɗe baki zatai magana kenan sai taji Yusha'u yanawa Zuhra magana ta waje cikin harshen turanci saika rantse ba'a ƙasarnan yayi rayuwa ba saboda yadda yake fito da ward ɗin, cikin Zuhra ne yayi wani juyi saboda tsananin fargaba, Azmah jin turancin nasa yasa ta shiga ruɗani matuƙa tare da ɗunbin mamaki, tana tunanin dama Zuhra najin turanci, turancin dataji Yusha'u yayi ko ita bazata iyashi ba duk da tana makaranta mai tsadan gaske.Buɗe labulan da akaine yasa gabaki ɗayansu waigawa, Yusha'u ganin Azmah yasa yaɗan tsorata yana kallan Auntyn nasa, singa tai masa da ido tuni ya gane abunda take nufi kasancewar Yusha'u yarone mai matuƙar wayau, ƴar dariya yayi yace "Aunty Zuhra kinji yau Allah ya nufa saida na haddace wannan turancin ko, saidai matsalar bansan me nake faɗi ba, dole saina koyo fassarar" ya faɗa tamkar zayyi kuka.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...