*Assalamu Alaikum, ina muku albishir da maganin sanyi wato infection idan zaku siya maganine me kyau kuma mai ingancine, sahihin maganin sanyi wanda inhar akwaishi a jikinki da yardar Allah zai miki magani cikin lokaci kanƙani,matan aure sunasha, ƴan mata suna sha, haka zalika yaran da suke fama da matsalar sanyi suma zaku iya basu, maza suna sha, gaskiya ɗaya zan iya faɗa muku shine maganin nada kyau, karku tsaya sanya maza garzayo wajan Mum Irfaan domin siyan maganin sanyinki a hannu, siyan ɗaya zakiyi koko sara zaki duk akwaishi, sannan akwai man gashi na al'arabee mai saka tsahon gashi, tsayin gashi, taushin gashi, cikar gashi uwa uba yana maganin dandruff me kike jira ƴar uwa maza tuntuɓi Mum Irfaan domin siyan ingantattatn maganin sanyinki haɗe da Man kitso da sauran abubuwan gyaran jiki, in kina da buƙata zaki iya tuntubata ta wannan numbern 08130515037 plz idan baki shirya ba karkimin magana mu ɓatawa juna lokaci*
Share hawayan fuskarta tayi ta tashi ta fita waje, ita kanta zaman ɗakin yanzu ya fara isanta, ba abunda ke mata yawo a kunnanta sai muryarshi dataji sama-sama lokacin da yakewa Azmah magana, haka kawai idan ta tunoshi dai gabanta yayi mummunan faɗuwa, tanaso tasan a inda tasan wannan muryar duk da can ƙasa ta jita amma tabbas jikinta na bata koma wanene ta sanshi, wanke-wanken data aje batai ba tazo ta farayi tana tunanin Azmah a wani hali take ciki yanzu, a haka harta kammala wanke-wankenta jikinta ko kaɗan ba ƙwari, mahaifiyarta na kallanta amma ba abunda tace mata domin kuwa a halin yanzu haushin kafiya irinta Zuhra kawai takeji, tuno yau yaushe ne ya ƙara hassalata ganin baza suyi sati ɗaya ba a garin dan iya kwanakin da suka ɗiba yana ƙoƙarin wucewa, sallamar wani ƙaramin yarone yasa tunaninta katsewa, ɗan dubansa tayi tana tunanin a ina ta sanshi, muryar yaronce ta maido da ita cikin hayyacinta, kallanta yayi yace "Maman su Uti wani na kiran Aunty Zuhra a waje yace tazo yanason ganinta..."
Cike dajin haushin aiken bata bari ya ƙarasa ba tace "Kaje kace bata nan"
Fita yayi bai daɗe ba sai gashi ya dawo yace "Yace zasuyi magana akan Azmah ne mahaifinta ne ke kiranta"
Cike da masifa tace "To da ƙarya nai masa, nace bata nan kaje kace na aiketa"
Bai kara cewa komai ba ganin yadda ta rufesa da faɗa ya tafi, Zuhra tana zaune a tsakar gida akan ɗan dakalin dake kusa da ɗakinta tana jinsu amma ba abunda tace, mamakin mahaifiyarta kawai take ganin yadda ta ɗauki wasu abubuwa da zafi, ita a nata ganin itace yafi dacewa taji ɗacin abunda sukai mata a rayuwa, shiru tayi ta maids hankalinta ga wani wajan ba abunda ƙwaƙwalwarta take tunani sai wannan muryar.Ganin yaron ya ƙara dawowa yasata kallanshi tace "Safwan jeka kace gani nan zuwa" yanajin haka ya juya ba tare dayace komai ba, ita kuma miƙewa tayi tana ƙoƙarin shiga ɗaki ta tsinkayi muryar mahaifiyarta tana cewa "Wallahi kul naga kin fita daga gidannan inba haka ba ranki zayyi mummunan ɓaci, zaki haɗu da fushi na, kuma na ban mamaki"
Ɗan murmushi Zuhra tayi tace "Mommy kenan, halan kin manta yau laraba, kuma kinsan ranar Friday insha Allahu zamu bar wannan garin mu nufa Kano, tayaya zan cika muku burunku akan Abdul-Jabbar ba tare dana je inda yake ba, karfa ki Manta Fatima nake insha Allahu zan cika muku burunku a kwanaki biyunnan,zanje naji me ke tafe dashi, wannan karan bamu da ishashshen lokaci, dan Allah mahaifiyata ki yarjemin naje domin tamu manufar badan ceton ran ƴarsa ba".Murmushin jin daɗi tayi tace "Ki maza kije ki dawo kar mahaifinki ya ganku tare dashi"
Gyaɗa kanta tayi ta shiga ɗakinta ta ɗauko Hijab ɗinta har ƙasa sannan ta nufa hanyar wajan, da fara'a ya tareta duk da kana ganin fuskarsa zaka tabbatar da cewar bashi da kwanciyar hankali, itama da murmushin ta tare sa duk da ƙasan zuciyarta tsantsan tsanarsa ce a ciki, gaishe dashi tayi har ƙasa sannan ta jingina da motarsa tare da harɗe hannayanta tana jiran abunda zaice mata.Kallanta yayi da fitinannun idanunsa, duk da kwana biyu baya cikin kwanciyar hankali amma zuciyarsa ba abunda yake kwaɗaita masa sai Zuhra, Zuhra murmushin gefen baki tayi ganin yadda taga ya kafe da idanunsa tuni ta tabbatarwa da kanta haƙanta zai cimma ruwa, kallanshi tayi da Sexy eyes ɗinta tace "Ina jinka My yaya kukai da ƴan Kidnapping ɗin"
Wani irin jin daɗine yaji ya ziyarcesa ya manta da tashin hankalin da yake ciki jin ta ambacesa da My, murmushin jin daɗi ne ya bayyana a fuskarsa, kana kallansa zaka tabbatar da cewar yana cikin farin ciki mara misultuwa, gyara hular kanshi yayi sannan ya dubeta dakyau yace "Gimbiya sarautar mata, sun kirani sun buƙaci da na basu Biliyan ɗaya, nai bakin ƙokarina akan su rage amma sunce daga haka ba abunda zasu rage, in zaɓa ɗaya cikin biyu ko in bada biliyan ɗaya ƴata ta tsira ko kuma su kasheta su hanani gawarta" yana gama faɗan haka yanayinsa ya canza tashin hankali tsantsan ya bayyana a fuskarsa.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...