Page 29

183 17 4
                                    

Keys ɗinsa ya kwaso wanda suke kan Bedside drawer gabanshi na tsananta faɗuwa duk da har yanzu Doctor yaƙi faɗamaia takamaimain abunda ke faruwa, ba tare da yayi la'akari dare yayi ba haka ya figi motar yabar harabar gidan ba inda ya dosa sai asibiti, jikinshi ba ƙaramin kyarna yakeyi ba ya shiga Hospital ɗin ganin matan Baban nasa zaune a bakin ƙofa ko wacce na gunjin kuka ya tabbatar masa da mahaifinsa ya tafi inda bazai taɓa dawowa ba, tura ɗakin yayi gabanshi na tsananta faɗuwa ganin har an rufe mai fuska yasashi saurin dafa bango dan wata irin hajijiya ya faraji ta fara ɗaukarsa, a hankali ya ƙarasa har inda yake ya yaye mai mayafin da aka rufe fuskarsa dashi, runtse ido yayi yana mai rungume mahaifinsa yana faɗin "Dan Allah Dad karka tafi ka barni, kaine gatana kai kaɗai kake nunamin so, kaine wanda baison kukana...." kasa cigaba yayi jin yadda muryarsa ta harɗe, yana tuno rayuwarsu ta baya tun yana yaro har kawo yanzu, sosai Fahad yake kuka tamkar ƙaramin yaro dan gani yake shima rayuwarsa tazo ƙarshe, kuma yana ganin kamar shine silar faruwar duk abunda ya faru a halin yanzu.
   Mahaifiyarsa a fusace ta shigo ɗakin dan gani take duk abunda ya faru shine sila shine ya janyo duk wa ƴannan matsalolin, ganinshi rungume da gawar mahaifinsa ya zube yana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro yasata karaya tare dajin tausayin ɗan nata, dan tabbas tasa Fahad babu wanda ya shaƙu dashi a gidannan sai mahaifinsa tun yana yaro suke kwana ɗaki ɗaya har saida ya fara zama saurayi sannan suka raba ɗaki, shima dan sauran matansa suna yawan yimai ƙorafi akan kwanan da yakeyi a matsayinsa wanda yayi hankali gani suke hakan bai kamata ba, hakan yasa suka raba gun kwana badan yaso ba, domin duk abunda Fahad yayi mekyau ko mara kyau to tabbas shi gani yake yay masa daidai, baisan fari ba baisan baƙi ba, wannan mutuwa ba karamin bugun Fahad tai ba, saidai muce Allah yasa muma mu cika dakyau da imani.

    Daƙyar aka cireshi daga jikin mahaifinsa yana kuka mai tsuma zuciya, komawa gefe yayi ya haɗa kai da gwiwarsa yana faman rusa kuka tamkar ƙaramin yaro, kafin kace me har fuskarsa ta canza kala ta kumbura saboda tsananin kukan dayasha, a haka har aka gama cuku-cukun abunda za'ai aka ɗauki gawar Alhaji Bashir Iyan Tama sai gidanshi, nan suka bari sai gari ya waye zasuyi mai jana'iza, Fahad kuwa wani Silent ya koma ba Uhm ba Uhm-Uhm saidai yabi mutane da kallo kawai.

   Zuhra tsayawa tai bakin ƙofa ta kasa fita, yanzu ita kanta tasan bata kyautawa Mommynta ba ganin yadda ta ɗauki lokaci a ɗakin Yayan nata, jin hannunsa cikin nata yasata ɗago da fuskarta tana kallanshi idanunta sun ciko da hawaye, ɗaga mata gira yayi alamun menene, shiru tai tanaso ta fara matsar hawaye, "Muje ko?"
  Kallanshi tai, alamun tambaya, "Gun Doctor zamu"
  Shiru tai na ɗan wani lokaci sannan tace "Amma Yaya Mommy batasan zan fita bafa, kuma kasan zataimin faɗa"
  Jan kumatunta yayi yace "Kai kinaji da wannan Mommyn gaskiya, ai ba daɗewa zamuyi ba yanzu zamuje mu dawo"
Shiru tai ba ansa, yayinda ya ruƙo hannunta suka fito daga ɗakin ya rufe suka fita, ganin sun fito harabar gidanne ta cire hannunta daga nashi gudun kar wani ya fito ya gansu.
    Basu dauki wani lokaci ba a Hospital ɗin nan result ɗin ya fito, babu komi a cikin saidai tana fama da ɗan matsalar Infection wanda yake ƙoƙarin hanata yin Period nan yayi mata allurai da wasu magunguna ya bata suka taho tare da shaida musu insha Allahu zata cigaba dayin period ɗin kamar nada, ba inda suka dosa sai gida, yana gama parking tai saurin fitowa daga motar ganin ta doshi hanyar Part ɗinsu, dariya kawai ya bita dashi shima ya kama hanyar nashi Part ɗin dan ya shirya ya tafi gun aiki tunda safiya tayi sosai.
   Kamar mara gaskiya haka ta shiga tana faman raɓewa, ganin Daddynta ya fito yasata sadda kanta ƙasa ta zube tana gaisheshi, ansawa yayi cikin sakin fuska yace "Ina Yayan naki?"
  Shiru tai ba tare datacs komi ba, gyara zama yayi akan 2seaters ɗin dake ɗakin yace "Maza jeki kiramin shi"
Ba musu ta tashi ta tafi kanta a ƙasa dan bataso ta hada ido da mahaifiyarta dan batasan wani irin kallo zatai mata ba, tun data fita jiya ba ita ta dawo gidan ba sai yanzu kai abun da kunya dolene ma taji kunyar iyayan nata, gani take duk abunda ya faru tsakaninta da Yayanta sun gani.
   Da wannan maganar zucin ta ƙarasa Part ɗinsa, Knocking ta fara, ganin ya fito yasata cewa "Daddy na kiranka" ta faɗa tana matsar hawaye, dan ta tabbatar wankesu yau zaiyi, janyota yayi cikin ɗakin tare da rungumota da ita faffaɗan ƙirjinsa yace "Waike mai yasa kuka bai miki wuyane?, Mommy ce tai miki faɗa?, domin nasan Daddy ba abunda zaice dan kin kwana anan, kuma ma ai bacci kikai na kasa tashinki"
   "Uhmm" tace tana ƙoƙarin zare jikinta daga nashi, "Nidai yace kazo karka daɗe" ta fada tai gaba dan gudun karta tsaya suyi aika-aika.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now