page 24

245 22 9
                                    

Ƙoƙarin barin ɗakin tahau yi sai kuma ta juyo tace "Wallahi nida kai har abada..." kasa ƙarashe kalamanta tayi ganin yadda ya sadda kai ƙasa ba abunda yake fita a idanunsa face hawaye masu ɗumin gaske, harara ta makamai ta juya zata fita, muryarsa ce ta dakatar da ita daga fitar datake ƙoƙarin yi "Zuhra karki tafi"
  Dariyar takaici tayi haɗe da tafa hannayanta tace "Waikai Sani wani irin jarabban mutum ne, koda yake idan ma an aura maka mata Huɗu a rana ina da tabbacin zaka iya dasu, me zan maka?, kana tunanin zan ƙara sauraran duk wani abu da zai fito daga bakinka ne?, to ka sani wallahi na daina yadda da duk wasu mayaudaran maganganunka" tsaki taja tare da faɗin "Maƙaryaci, ai nagodewa Allah daka nunamin halinka tun kafin na shiga daga ciki, yau ni Sani zaka ɗauki hannunka ka wankamin mari dan na ganka da karuwa ko" yanayin yadda take faɗan haka abun ba ƙaramin taɓa mata zuciya yayi ba.
   Ɗan damtse hannunsa yayi jin yadda take gaggasa masa maganganu marasa daɗi, wani irin iska ya furzar ga numfashinsa yadda yake ƙoƙarin ɗaukewa lokaci guda, so yake ya dake amma tashin hankalin da yake ciki ya wuce minsali don kuwa ya tsani shaidar Zina abunda ya tsaneta yake ƙyamarta tayaya zata runƙa dangantashi da aikata hajan, yama rasa da wacca zayyi lalata da ida sai wacca ya tsana baya ƙaunar ganinta, wacca Mahaifinta ya rusa mishi duk wani jin daɗin rayuwarsa, amma yanzu wacca yafi ƙauna fiye da kowa a duniyarnan wacca ta zame masa ƙanwa, Mahaifiya, Mahaifi amma take jifansa da wannan kalaman, gashi ƙwayar idanunta a yanzu babu komai a ciki face tsantsan tsanarsa datake.
   
Gabaki ɗaya jikinsa baya jin ƙwarinsa ya rasa menene dalilin haka ga wani irin ciwon Mara wanda yayi mishi mugun kamu saidai tashin hankali da yake ciki bazai tsaya ya saurari mararsa ba, duk da yanajin ciwon ba kaɗan ba ga wani irin zazzaɓi da ciwon ya sakin masa lokaci ɗaya, kallan Zuhra yake da idanunsa na alamun yana tsananin buƙatar taimakonta a halin da yake ciki, saidai ita kallan datake jifanshi dashi babu komai a cikinsa face tsantsan tsanarsa da kuma jin haushinta ga kishi tamkar zai kasheta saboda a halin datazo taga Azmah.
   Kallan ƙofar Bathroom ɗin tayi ganin har yanzu Azmah bata fito ba gashi ta ɗauki a ƙalla fin awa a ɗakin, zuciyarta ce ta fara yi mata wasi-wasi saidai tanaso ta kawar da wannan wasi-wasin saboda ita ganau ce ba jiyau ba.
  Kallanshi tayi yayinda ya kafe da kyawawan idanunsa saidai gabaki ɗaya sun sauya kala sun tashi daga launin fari.
   A hankali ya buɗe baki yace "Please" ko kaɗan bataji abunda yace ba saidai yanayin yadda ya motsa bakinsa ta gane me yake nufi, ɗan harararsa tayi tabbas tanaso taje inda yake amma ko kaɗan zuciyarta ba abunda takeji game dashi sai haushinsa da kuma tsanarsa.
    Buɗe ɗakin tayi harta sa ƙafa ɗaya tana ƙoƙarin fita yaɗan buɗe murya yace "Fatima!"
Cak ta tsaya gabanta yayi wani irin mugun faɗuwa, a iya rayuwarta bai taɓa kiran ainihin sunanta ba sai yau, a ɗan fusace ta juyo sai taga yana ɗan jujjuya kai hannunsa ruƙe da mararsa, tsayawa tayi sororo tana kallanshi ganin yadda ciwon marar tasa ya tashi saidai ganij yadda yake zai tabbatar maka da wannan karan ciwon marar yafi na koda yaushe, kafeshi tayi da ido hawaye na ƙoƙarin saukowa daga idanunta ganin yadda yake ƙoƙarin bata haƙuri gashi yana tsananin jin ciwo.
   A hankali ta kalleshi sai hawayan da suka maƙale a idanunta suka sauko, kantane yayi matuƙar ɗaurewa meye haɗinsa da ciwon mara a halin yanzu, lumshe ido yayi jim yadda yakejin numfashinsa na barazanar ɗaukewa, cikin dauriya irin ta ɗa namiji yace "Ki yadda dani dan Allah, ki bani Second Chance, tabbas kika tafi kika barnia wannan halin dagani har ke sai mun tafka babbar nadama dan Allah ki saurareni...." kasa ƙarasawa yayi jin yadda marar tasa ke murda masa.
   Dafe bango tayi hawaye na zarya a idanunta ta kasa gane gaskiyar lamarin dake afkuwa, tayaya zayyi ciwon mara yanzu alhalin tana zargin kamar sun gama aikata masha'a shida Azmah, "Pleaseee" kawai yaje jikinsa yaɗan fara rawar sanyi.
   Juya mai baya tayi bata ƙaunar ta ganshi cikin wannan halin ko kaɗan.
  Kallan Bathroom tayi taga har yanzu Azmah batai yunƙurin fitowa ba, tuni zuciyarta ta yanke cewar wannan abunda ke faruwa shirin Azmah ne tabbas sai yanzu ta gane hakan.
  Share hawayan fuskarta tayi, ta nufa Bathroom ɗin tana tura ɗakin taga Azmah a zaune, babu alamun tai wanka a tattare da ita, matsawa tayi kusa da Azmah tana karewa halittatta kallo tare da jifanta da wani irn kallon tsana, tsirtar da yawu Zuhra tayi tace "Tabbas sai yau na yadda da karin maganar Hausawa na cewar barewa bazata taɓa yin gudu ba sannan ɗanta ya ɓige dayin rarrafe, sai yanzu kika tabbatarmin dake ɗin jinin Abdul-Jabbar ce, wallahi tallahi Azmah da nasan kina da mugun nufi a zuciyarki da dake da Ubanki zan tattara na ɓatawa rayuwa gabaki dayanku ku ɓige da zaman gidan kaso, abu ɗaya yasa na ɗagawa mahaifinki ƙafa saboda soyayyarki dake zuciyata da kuma kyawawan ɗabi'unki hakan yasa nai bala'in raga muku, banyi Mamakin sanina da kikai a baya ba saboda wannan book ɗin dana baki nace na manta na bakishi na baki shine dan ki tabbatar da abunda Ubanki yayi mana da abokinsa, kuma nasan kin karanta hakan yasa kikaimin Pretending kamar yadda nima na barshi a haka, idan karuwancin kike da sha'awar yi maizai hana kije ki kama ɗaki gidan karuwai?, ki fita daga harkar Family ɗina inba haka ba gab kike dayin nadama wacca batada amfani, Fita daga gidannan" ta faɗa mata fuskarta sam babu alamun wasa yayinda tsantsan ɓacin rai ya bayyana a fuskar Zuhra.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now