Page 34

179 19 8
                                    

Ba abunda suke zai faman zirga-zirga a Hospital ɗin hankalinsu a matuƙar tashe musamman Muhammad da tunani ya cika masa ƙwaƙwalwa yana zargin anya ba ruwan daya bashi bane ya janyo silar faruwar hakan ba, ganin Doctor ya fito yasa Zuhra da Muhammad Ali nufar inda suke suna tambayar lafiyan me jiki, ɗan jim Doctor ɗin yayi sannan ya kalli Zuhra yace "Ki zauna ki jiramu anan zamuyi magana mai muhimmanci ne"
  Gabaki ɗaya idanun Zuhra sun koɗe saboda tsananin kukan datasha dan har gefen idanunta sunyi ɗan baƙi, cikin muryarta wacca tasha kuka ta ƙoshi tace "Doctor duk abunda zaka faɗamai ka faɗa mishi a gabana kawai domin hankalina saiyafi kwanciya, dan Allah kuyi ƙoƙarin ceton ran Bawan Allahnnan"
Ta faɗa tare da haɗa hannayanta waje guda hawaye na sauka akan kuncinta, Muhammad rungumo da ita jikinsa yayi yana ɗan shashshafa bayanta alamar rarrashi, sannan ya kalli Doctor ɗin yace "Mu shiga Office ɗin"
Ba musu ya juya baya ya shiga yayinda suma suka mara masa baya, zaunar da ita yayi akan kujerar dake Office ɗin sannan shima yaja ɗaya ya zauja yana fuskantar Doctor ɗin, cikin sanyin murya yace "Doctor maiya faru dashi haka lokaci guda ya fara fidda amai daga hancinsa zuwa bakinsa"
   Numfasawa Doctor ɗin yayi yace "A Zahirin gaskiya Poison yasha mai ƙarfin gaske, domin kuwa da bakuyi gaggawar kawoshi Hospital ba ina mai tabbatar muku da cikin lokaci ƙanƙanci zai iya rasa rayuwarsa, wannan case ɗin ba ƙaramin Case bane dan haka dole sai mun shigar da ƴan Sanda akan wannan case ɗin dan su gudanar mana da bincikenmu yadda ya kamata, kuyi haƙuri haka dokarmu take dan haka kuma dokar zata hau kanku"
   Cike da mamaki Muhammad Yace "Poison fa kace?"
  Jinjina kai yayi yace "Ƙwarai kuwa, yanzu haka Police zasuzo su tafi dakh gidanku su fara gabatar da bincike akan abunda ya faru, insha Allahu sai mun kama wanda yake da hannu dumu dumu a wannan lamarin"
   Gabaki ɗaya jikinsu ne yayi sanyi musamman ma Zuhra, gyaɗa kai Muhammad yayi yama kasa cewa uffan saboda mamakin dake ɗawainiya dashi.
   Knocking aka fara nan Doctor ɗin ya bada umarnin da su shigo, ƴan sandane masu fararan kaya suka shigo, ganin Muhammad da Zuhra yasasu zaro ID Card ɗinsu suka nuna musu tare da ƙara tabbatar musu da su Police ne, nan suka kora musu jawabi na cewar ya zama dole aje gidansu ayi bincike, nan take Muhammad Ali ya goya musu baya, tashi sukai suka shiga motarsu ƴan sandan suka mara musu baya da tasu motar.

  Yadda suka bar gidan haka yake ba abinda aka taɓa, hand glove suka saka suka fara dube-dube tare da shinshina duk wani abun ci dana sha dake gidan, ruwan da Fahad yasha shi suka ɗauka tare da rufe murfin gorar suka saka cikin wata ƴar jaka, duba ruwan dake Fridge sukai ganin yadda har ya fara sauya launi gabaki ɗaya ruwan yasasu tabbatar da kaf ruwan shima an zubamai Poison a cikinsa, ƴan rubuce rubuce sukayi, sannan Ogansu ya ɗago da kanshi ya duba Muhammad yace "Tabbas duk wani abunci dana sha dake gidannan an zuba mai Poison shin a cikinku waya aikata hakan?, ko ko kuna zargin wata ko wani da aikata hakanne?"
   A kiɗime Zuhra ta kalli Muhamand hankalinta a tashe, janyota yayi jikinsa gudun kar abunda ya faru ɗazu ya ƙara afkuwa da ita gata da ƙaramin ciki yasashi murmusawa, numfasawa yayi yace "Tabbas Azmah ce ta aikata hakan, ban tabbatar ba sai yanzu ta kuka ƙara bincike akan hakan saboda na ganta tana rufe ruwan da Fahad yasha ganina datai naga ga tsorata tabbas a lokacin jikina bai bani komi ba"

"Wacece Azmah?" Ɗan sandan ya tambayesa.
  Furzar da wata iska mai zafin gaske yayi, ranshi a matuƙar ɓace tare da ƙoƙarin danne ɓacin ran nashi yace "na kira Police dake wajan Fly Over sun tafi da ita, ta sanadiyyar tai ƙoƙarin watsawa Matata Acid"
   "Acid?" suka haɗa baki suna kallonshi ta matuƙar mamaki, babban cikinsu yace "Ko zamu iya tafiya dakai dan muyi mata wasu tambayoyi agabanka?"
Ɗaga kafaɗa yayi yace "Why not, zamu iya tafiya saidai ku ɗan bani 15minutes please"
   Gyaɗa kai sukai yayinda suka gyara Parking ɗin motarsu.
   Shiga ciki yayi ya tarar da ita zaune ta rafka uban tagumi, zama yayi kusa da ita tare da cire hannayanta daga tagumin datai yace "Please ki daina damun kanki, insha Allahu Fahad zai warke ya koma tamkar bayyi wani ciwo ba, zamuje Police wajan Azmah domin sunason yi mata wasu tambayoyi, zaki shiga gidane ko anan zaki zauna muje mu dawo?"
  Share hawayan fuskarta tai tare da girgiza mai kai tace "Kaje ka dawo banaso in shiga Mommy ta fahimci akwai matsala, banso susan cewar wata tazo gidannan domin ta illatamu watanma Azmah bazanso suji hakan ba"
   Hannunsa ya saka ya share mata hawayen dake zuba a fuskarta yace "Wannan case ɗin ba ƙaramin Case bane Faɗima, dole su Daddy susan komai, idan har suka tsinta magnar a waje kina tunanin wani irin kallo zasuyi mana, ki tashi ki watsa ruwa saiki kwanta bazamu daɗe ba zamu dawo"
  Gyaɗa kanta tai,tana kallanshi yayinda ya tashi yace "Ki kulamin da kanki, sannan ki kulamin da jinina"
  Gyaɗa mai kai tayi ta rakosa har Balcony sannan yace ta juya ta ta shiga ɗaki.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now