page 3

296 18 2
                                    

*MUHAMMAD ALEE*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
 

     
                             *03*

Joseph yana faman ciccije baki yabar wajan yaje ya miƙa masa kayanta, karɓa yayi, yana kallan Joseph ɗin yace "Kano zaka koma gun su Modibbo, daga dawowarka zaka fara jamin magana" ba tare daya jira abunda zaice ba ya juya ya fara tafiya, tsayawa yayi yana tunanin ya zayyi, ya ɗauki a ƙalla zayyi minti biyar sannan ya juyo yana kallansu, kiran ɗaya daga cikinsu yayi yace "jeka kwanceta" ba musu yayi hanyar datake ya kwanceta, kamar jira take ta ƙwalla wani uban ƙara tana kiran iyayanta, bayan ya dawo ya miƙa masa kayanta yace kaje ka bata, ansa yayi ya miƙa mata ya fito, shi kuma ya tsaya yana jiran fitowarta, ya daɗe yana jiran fitowarta amma shiru bata da niyyar fitowa ba abunda kakeji sai sautin kukanta, jin shirun yayi yawane yasashi ɗan leƙawa yaga kota suturta jikinta, tana rakuɓe ta saka kayanta tana faman yin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, jin alamun an shigo yasata kurma wani uban ihu, kallanta kawai yayi tuni ta natsu amma duk da haka hawaye masu ɗumi basu daina fita daga idanunta ba, ba tare daya kalleta ba yace "Fito mu tafi" ya juya jin taƙi biyosa yasashi juyawa yana kallanta, wani gu yaga tana kalla jikinta na kyarma, kallan gun yayi yaga baiga alamun kowa ba, "Nace kizo mu tafi gida zan kaiki ko kinaso na barki anan ne?" ya faɗa yana kallanta, cikin muryar kuka tace "Tare da ƙawayena muke"
   A ɗan birkice ya waigo yana kallan inda take kalla yace "Kina nufin bake kaɗai bace?"
Ya faɗa gabanshi na faɗuwa, gyaɗa mai kai tayi tana faman matsan hawaye, gaba tayi yabi bayanta har yana ƙoƙarin faɗuwa, saida suka kutsa sosai cikin dajin sannan ya hango mata biyu suma ɗaure da igiya, girgiza kai yayi yana tunanin rashin imani irin nasu Baffah, ƙwaƙwalwarsa ce ta daina aiki ganin wata yarinya wacca itama bazata wuce sha bakwai ba kwance ƙasa jini na yawo a ƙafafunta, dafe kanshi yayi da sauri jin yana neman faɗuwa, ko ba'a faɗa masa ba yasan aikin gama ya ruga ya gama akan yarinyar nan ya tabbatar da fyaɗe sukai mata, idanunsa sun kaɗa sunyi jajir yabar wajan cike da ɓacin rai, ada suna kawo karuwai wanda suka amince dayin hakan amma yanzu abun harta kai su ɗauko yara su keta musu haddnsu basuji basu gani ba, ikon Allah ne kawai yakaishi inda suke yayinda gabaki ɗaya sunyi tsuru-tsuru suna jiran abunda zai afku, kallansu yayi da idanunsa wanda suka canza kala tamkar banashi ba yace "Waye a cikinku?" ya faɗa yana jifansu da wani irin mummunan kallo, dukkaninsu shiru sukai babu wanda ya bashi amsa, a zuciye ya danƙo ɗaya daga cikinsu yace "Tambayarku nake wanene yayiwa wacca yarinyar fyaɗeeeee?" ya faɗa cikin karaji da tashin hankali, kakari kawai yakeyi ganin yana ƙoƙarin kaishi lahira, tarine ya sarƙesa sannan yace "Joseph ne da Ya'u"
Sakinshi yayi ji kake tim ya faɗi ƙasa, jin yana neman faɗuwa yayi saurin dafa bishiyar dake kusa dashi idanunsa a lumshe jin an ambaci bama mutum ɗaya yayi amfani da ita ba, ya ɗauki tsawon minti talatin yana ƙoƙarin controlling zuciyarsa amma ina ya kasa, yana buɗe idanunsa suka sauka akan na Joseph, juyawa yayi gefen Ya'u yaga kanshi a ƙasa, tamkar ƙwai ya fashe mai a jiki haka ya shiga wannan bukkar data zamana mallakinsa, bindiga ya ɗauko ba tare da tsoron komai ba ya fita waje da ita, saitin zuciyar Ya'u ya saka bindigar yana kallanshi da shanyayyun idanunsa tamkar ɗan maye, wasu irin hawaye ne suka sauka akan kuncinsa saurin runtse ido yayi yana ƙoƙarin maida hawayansa, ji yake tamkar ƙanwarsa akaima yana tuna lokacin da itama ƙanwarsa hakan ta afku da ita, girgiza kai yayi yace "Mai yasa, mai yasa kuke son rugazawa musu rayuwarsu ne tare da iyayansu?, kai yasa kukeson yi musu tabon dahar su mutu bazai taɓa goguwa a cikin zuciyoyinsu ba, in ƙanwarka akaiwa yaya zakaji?, idan mahaifiyarka akaiwa me zakaji a cikin zuciyarka, inaga itama ɗiyarka an mata wani irin ɓakin ciki zaka ƙunsa tsawon rayuwarka?, mai yasa bazaku ɗauke sauran matan iyayanmu, ƴaƴanmu ƙannan mu ba?, bazan iya rayuwa daku ba ku gafarceni" ƙoƙarin danna bindigar ya farayi amma jin kalaman mahaifiyarsa cikin kunnansa yasashi yadda bindigar yayi sauri yabar wajan, Bukkar ya shiga ya duƙa ya fara rera kuka tamkar ƙaramin yaro tamkar ba jarumi ba, ba abunda yake tunawa sai mahaifiyarsa, mahaifinsa da kuma ƙanwarsa wacca ta zeme masa hasken rayuwa, rana ɗaya ya rasasu lokaci ƙanƙani, hargitsa gyararriyar sumar kanshi ya farayi yana mai ƙoƙarin yiwa kanshi illa, gabaki ɗaya fuskarsa ta koma ja abunka da farin mutum saboda tsananin tension da yake ciki, ya ɗauki a kalla wajan minti arba'in sannan numfashinsa ya fara daidaita, lumshe ido yayi yana maijin ɗaci cikin zuciyarsa, a haka har bacci ɓarawo yayi galabar yin gaba dashi yayinda su kuma ƴan matan tuni suka kama hanya suka gudu suna maijin tsananin tsoro da fargaba, wacca suka aikatawa masha'a kuwa haka suka ɗauketa tana raye ko tana mace, rai a hannun Allah,

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now