Page 28

193 14 3
                                    

Ganin hankalinta gabaki ɗaya yana kan T.V, yasashi kintsawa cikin natsuwa, dawowa yayi kusa da ita ya zauna haɗe da janyota jikinsa yana faɗin "Har yanzu dai bakisan kin girma ba ace mutum tun yana yaro yanason Cartoon har ya girma yay aure, to yaya yaranmu zasu kasance su kuma?"
  Murmushi kawai tai tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa, kallanshi tai tace "Yaya bari naje nasan Mommy nacan tana faman leƙa window kona taho"
  Maganar tata dariya ta bashi hakan yasa ya murmusa tare da janyota cikin jikinsa yace "Ba inda zaki, nida Mommy wake da iko dake?"
  Shiru tai ba amsa can kuma ta yatsina fuska tace "Nifa yanzu banga period ɗina ba gashi ina ƙoƙarin shiga 2months" ta faɗa damuwa fal cikin ranta, ɗan kallanta yayi ganin yadda ta canza fuska ya tabbatar masa da bada wasa takeyi ba, "2 months kuma Zuhra?" ya tambayeta yanason jin ƙarin bayani, ɗaga mishi kai tayi tana wasa da yatsun hannunta, shafa cikinta yayi, kardai har nayi a jiya a cikin wannan shamulallan cikin"
  Kallanshi tayi da alamun tamabaya dan ita harga Allah batasan me yake nufi ba, ɗan tsugunnawa yayi yay ma cikin Kiss ya kasa gasgata abunda yake gani yau da gaskene, jinshi kawai yake tamkar yana mafarki, ɗan zillo tayi tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa kumburo baki tayi tace "Wai menene haka" ta faɗa tamkar zatai kuka, kallanta yayi da fuskarsa wacca ta cika da tsantsan farin ciki yace "Tashi muje Hospital" dafe ƙirji tayi tace "Maye haɗina da Hospital kuma?, nifa Yaya banso zuwa Asibiti kaika sani"
Ta faɗa tana turo mai baki, murmushi yayi yace "So nake Doctor ya ƙara tabbatarmin da abunda nake zargi"
   "Yaya, me kake zargi akaina?"
Dariya yayi yace "Uhm, cikinmu mana, muga na how many weeks ne"
  Dafe ƙirjinta tayi gabaki ɗaya idanunta sun firfito waje tace "Ciki kuma?, a jikinwa?, innalillahi wa inna illayir raju'un, na shiga uku" ta faɗa tare da zamewa ƙasa tai zaman ƴan bori nan take ta fashe da matsinanci kuka tana kiran ta shiga uku ta lalace.
   Muhammad tsayawa yayi yana kallan ikon Allah, dan bayyi tsammanin haka daga gareta ba, tsugunnawa yayi kusa da ita yace "Haba Zuhra wai meke damunki haka, cikin nawane bakiso?"
  Shure-shure ta farayi da ƙafafunta tana faɗin "Wallahi saina zubda,wallahi bazan zauna a gidannan da cikinnan ba, abun kunyar sai yay yawa"
  Maganar datai ta ƙarshe ba ƙaramin dariya ta bashi ba, amma ganin tabbas ya tsaya yi mata sanya zata zubda cikin kamar yadda ta faɗa domin yasan halin Zuhra fiye da yadda nai karatu baya tsammani, ganin ya tashi ya shiga ɗaki yasata binshi da kallo fargaba fal cikin ranta, yanzu idan Mommy tasan tana da ciki zatace kullum sai tazo ɗakinsa alhalin kwata kwata so nawa suke keɓe da juna, ita ta sani inhar akace cikine da ita tsangwama kaɗai da isheta a cikin gidan barinma Mommy.
  Da kallo ta bishi dashi ganin ya fito daga Bedroom ɗinsa ya canza kaya hannunsa ruƙe da Key fuskarsa sam babu akamun fara'a a tattare da ita, ko kallan inda yake baiba ya fita daga ɗakin yayinda tai yunƙurin biyosa sai taga harya fita ya sakawa ƙofar Key, bubbugawa tahauyi tare da leƙa window taga ko alamun waigowa ma bai ba bare ta saka ran zaizo ya buɗe mata, komawa tai ta zauna ta zabga uban tagumi tana shafa cikinta, da gaske yake wai cikine da ita, ta faɗa a cikin zuciyarta, sauri tai ta girgiza kai, yayinda hawaye masu ɗumi suka sauka akan kuncinta dan tasan tabbas sai Mommy tai mata wankin babban bargo tare da yi mata kirari bata da kunya, tagumi tayi tare da ƙurawa gefe ɗaya ido.

"Yaushe zaki leƙa gidansu mutuniyarki?" Fahad da yake zaune saman mota ya tambayi Azmah datake tsaye kusa dashi, taɓe baki tayi tace "Ni zan taka ƙafa naje gidansu mara kunyar yarinyarnan, ai ina kyautata zato naje wallahi sai ta saka a dukeni ko ita ta dukan da kanta, kasan irin korar karan dataimin kwanakin baya kuwa?" ta faɗa tana ɓata rai ga dukkan alamu abun yana matuƙar cin ranta.
  Dariyar rainin hankali Fahad yayi yace "Yanzu Zuhra tana da Izzar da zata korekine, yarinya natsatstsiya ga ruƙo da addini...." ba ƙarasa abunda yakeso ya faɗa ba yaga Azmah ta makamai harara, ɗan gajeren tsaki tayi tace "Nj kuma ba tarbiya ko?" ta faɗa tare da janyo Hand Bag ɗinta saman mota ta fara tafiyarta, dama hanya takeso tabar wajan dan sunyi da Alhajinta zaizo ya ɗauketa su fita, Fahad da murmushi yabi bayanta yayinda ya kunna wayarsa yana kallan hoton Zuhra bai taɓa soyayyar gaskiya ba sai akanta, ba abunda yakejin tsoro sai kar Zuhra ta shiga wani hali idan taji cewar kasheshi akai, hakan idan ya tuna zuciyarsa na neman karaya akan abunda yakeso ya aikata, koda wasa bayaso ya ganta cikin damuwa bare kuma tashin hankali, tabbas yana matuƙar son farin cikinta amma ganin yana da buƙatar mallakarsa yasashi manta da duk wa ƴannan abubuwan yake ƙoƙarin ganin nashi burin ya cika akanta, kewartace ta addabeshi yayinda ya tuno irin tsantsan soyayyar da sukai a baya, gabaki ɗaya hankalinshi ba a kwance yake ba jin lokacin da yake shaida mata cewar Muhammad zai mutu, haka kawai zuciyarsa ta kasa samun natsuwa dan yana da tabbacin tana cikin tashin hankali, numfasawa yayi tare da furzar da iska daga bakinsa yace "Tabbas inaso nai ƙoƙarin yin yaƙi da duk abunda nake mara kyau ko Allah zai dubeni ya mallakamin ke cikin sauƙi, ina miki son da ban taɓa yiwa wata ƴa mace a doron ƙasarnan ba, ina ƙaunarki Zuhra, bani da niyyar cutar dake a rayuwata"
Idanunsa sauya kala sukai yay shiru kishi na faman cinshi cikin zuciyarsa idan ya tuno babu wanda Zuhra ta mallakawa zuciyarta face Muhammad Alee.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now