*_Idan kun bani haɗin kai nayi ƙoƙarin kammala muku wannan littafin kafin azumi, idan kuww kunƙi bani da case daku haka zamuyi tayi ana zuwa hutun rubutu tunda ɗan comments ɗin da zakuyimin ne yake gagarar wasu, dan haka aƙi comments naƙi typing sai randa na nishaɗantu nai muku ƙaramin page na wullo muku😂ina yinku masu comments, marasa comments kuna janyo musu delay ɗin posting fa_*
*Flash Back*
Idanunsa ne suka sauya kala, kallan Zuhra yayi amma kanta a ƙasa yanaso ta zauna kusa dashi amma hakan ya faskara, numfasawa yayi yace "Daddy lokacin da akaita jiranku akan zuwanku aka jiku shiru hakan yasa Mahaifina yace bari ya ɗaura auran kawai ganin yadda al'umma suka taru kai kawai ake jira, gashi jirginku lokacin bai sauka ba, duk da kaine maɗaurin aurena shi kuma na Zuhra hakan yasa ya naɗa babban abokinsa akan shine maɗaurin aurena, nan aka fara gabatar da ɗaurin auranmu, bayan dubban mutane da suka sheda ɗaurin auranmu hakan yasa kowa ys watse aka bar wa ƴanda baza a rasa ba, ashe a cikin taron Bashir Iyan Tama da abokinsa Alhaji Abdul-Jabbar da kuma sauran ƴan ta'addan da suka ɗauko suna cikin wannan taron, saida suka tabbatar da kowa ya watse sai imu-imu suka fara sakin ruwan harshashe, kafin muyi wani yunƙuri Sun fara kashe mana mutananmu, hakan yasa na fara neman yadda zan kare kaina dana sauran mutanan daba'a kashe ba, saidai ina, sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, da bindigogi suka tsaya a gidan taron mata suka bada umarnin ko wacce ta fita ahalanmu kawai za'a bari, hakan yasa mata suka tsure suka bara neman hanyar fita daga gidan, kafin kace me kowa ya watse aka bar Familynmu dan ba ƙaramin taka tsantsan sukai ba na babu wacca zata fita inhar a Familyn take, dan wani suka samu wanda yayiwa Familynmu farin sani ya sa ido akan matan, gidan yayi tsit tamkar ba mutane haka haka suka shiga cikin gidan bansan maiya faru ba saidai tabbas nasan ba ƙaramin ta'asa sukai mana ba, domin jikina ya bani har fyaɗe saida suka aikatawa matan gidan domin yanayin yadda suka fitone ya tabbatarmin da haka"Shiru yayi yanajin babu daɗi ko kaɗan cikin ransa yanaso ya zubda hawaye amma ko kaɗan babu alamunsa, saidai yadda zuciyarsa take tuƙuƙi ya tabbatarwa da kanshi yana cikin tashin hankali.
Runtse ido yayi yana tuno yadda sukaci zarafinsu, suna zuwa harabar gidan basu sauraremu ba suka fara binmu ɗaya bayan ɗaya suna harbi, tare da dariyar mugunta harda shewar jin daɗi, nan take saiga Bashir Iyan Tama da Abdul-Jabbar sun bayyana sun fito daga cikin wata mota sun tsaya kan mahaifina suna tattakashi da ƙafafunsu, faɗi suke tashi ta ƙare harsu zai maka a kotu saboda ya samu sake, Bashir Iyan Tama da bakinsa yake faɗin shi da kanshi ya aikatawa ƙannina da kuma matar dana aura fyaɗe, haka Abdul-Jabbar shima ya maimaita, Fahad zayyi magana suka juya suka fara tafiya, naso naji me zaice, shima ya aikata musu fyaɗenne kamar yadda iyayansa suka da faɗa, saida suka tafi sukai nisa a tafiyarsu saiga Police mutanan danafi awa guda ina kiransu sukaƙi ɗauka amma sai gasu bayan komai ya lalace mana, dai gashi sunzo a lokacin da bama buƙatarsu, banda ƙarfin dazan iya korarsu saboda harbin da sukaimin a ciki amma tabbas da saina koresu, tunda na gansu suka zo da motar ambulance aka fara fiddo da matan ko wacce cikin jini mahaifiyata itace ta samu damar yin magana, tunda ta tabbatar da nima ina raye,ta barmin nasiha mai tsuma zuciya duk da nima inaji a jikina cewar zan bita, ganin an sakata a mota ga jini na faman zubar mata ya tabbatar da cewar Allah yasa itama bazata mutu ba, nan take naji jiri ya fara ɗibata bansan inda kaina yake ba saida nayi sati uku a Hospital, ba'a shaidamin dawowarku ba andai shaidamin duk wanda na sani na Familynmu to Allah yayi masa rasuwa, na zubda hawaye babu adadi nai kukan baƙin ciki amma haka na fawwalawa Allah, bayan na koma gidane naga an sakashi a kasuwa cewar Bashir Iyan Tama na binku bashi mai ɗunbin yawa, murmushin takaici nayi sai naga Baffah a bayana yana numfarfashi ashe yaje asibitine ance an sallameni, kuma tun lokacin dana sume shine yayi duk wani ƙoƙari ganin anmin aiki an cire bullet ɗin dake cikin cikina, na shaida masa duniya zan shiga ya ansamin dayaji ya gani zai bini, a da zuciyata ta yanke shawarar na zama ɗan ta'adda wanda za'ai Allah wadai dani, sai kuma zuciyata ta bani shawarar na ɗauki fansa kawai hakan shine daidai a rayuwata, hakan yasa na fara Kidnapping ɗin Familyn Bashir Iyan Tama da kuma na Abdul-Jabbar, ban taɓa kisa ba,haka zalika banso nai saidai nai alƙawarin ɗanɗanawa Familynsu jin ɗaci na har abada kamar yadda suka sakani nayi"
Kallan Mahaifin Zuhra yayi yace "Wannan shine abunda nasani akan abunda ya faru a ranar, saidai nayi mamaki ganin Zuhra ita kaɗai a raye" ya faɗa yana jifanta da wani irin kallo mai wuyar fassarawa.
YOU ARE READING
MUHAMMAD ALEE
Actionko wani bawa da irin tashi jarabawar, akwai ɗan ta'addan da yana ta'addanci amma ko kaɗan bada son ranshi yake aikata hakan ba, tayaya al'umma zasu fahimci hakan?, tayaya al'umma zasu gane cewar baison ta'addanci?, kudai ku cigaba da bibiyata na sab...