page 5

344 20 11
                                    

Kiran Modibbo ne ya katseshi da tunanin da yakeyi, cike da kasala yasa hannunya ɗauki wayar tare da karata cikin kunnansa yana sauraransa, duk wani abu da Fahad yakeyi saida ya zayyanewa Ogansa tareda tabbatar masa koda yaushe yana tare da security's hakan na nufin basu kaɗai bane sukeson kai masa hari, shiru yayi yana nazari can kuma yace "Shikenan, ka cigaba da saka ido a kanshi"
Cikin girmamawa Modibbo ya amsa da "To" katse wayan yayi ya zauna tunani abunda ya afku shekara ɗaya kenan da faruwar abun kawai yakeyi, yana yanzu abu ɗaya kawai yake tunani a ina zaiga danginsa, yaushe zai samu farin cikin daya daɗe bai sameshi ba, babu abu masoyuwa ace kana da mahaifi da mahaifiya tare da ƴan uwa, uwa uba ga dangi wanda suke matuƙar ji dakai sede a cikin yini guda ya nemi wannan ahalin nasa ya rasa, yayi rashin da bazai taɓa maidashi ba har karshen numfashinsa, kallan ƙasa yayi yana mai ƙara kallo, a hankali ya furta akan ƙasa (Fili) na rasa komai nawa, ya faɗa wasu hawaye masu ɗumin gaske suka sauka akan kuncinta, share hawayan yayi tare da kafe wani kyakykyawan zobe dake manne a ɗan yatsunsa yana sauke ajiyar zuciya.

      Zuhra koda safiya tayi bata fito ba saboda yadda aka taɓo mata wani tabo wanda bazai taɓa goguwa a rayuwarta ba, tsanan Abdul-Jabbar tayi kane-kane a cikin zuciyarta, ko kaɗan bata ƙaunar ganinsa a rayuwarta, wani sa'in zuciyarta takan bata shawara akan idan ta samu dama a kanshi kawai ta kasheshi a rage mugun iri, amma idan ta tuna da Azmah saita kasa, wannan karan tayi alwashin Abdul-Jabbar bazai taɓa tsallake tarkonta ba, tanaso ta nemi izinin mahaifanta akan abunda takeso ta aikata, saidai tasan hakan ba abu bane mai sauƙi, shiru tayi tana tunani, can ta ɗauko lapton ɗinta wanda ta ɓoye cikin ƙatuwar Ghana Must Go ta fara duba wasu muhimman abu.

      Fahad yana tsaye a wani Hotel me kyan gaske, yayinda cikin Hotel ɗin akwai wani club wanda idan aka fara rawa da waƙa akanyi tilldown a wajan ba tare da damuwar kowa ba, jin ƙarar message yasashi saurin dubawa ganin Hot beb yasashi tabbatar da cewar new catch ɗinsa ce, cikin sauri yabi layin datai mai message jin wayar ta shiga yasashi mamaki ba kaɗan ba, dan koda wasa baya samun layin, bai taɓajin muryarta ba, haka zalika bai taɓa ganinta ba, amma ganin yadda take tafiyar da rubutunta ya tabbatar masa da koma wacece ita ɗin mai zafi ce, jin harta gama ringing ba'a ɗauka ba yasashi numfasawa tare da ƙara kiran layin, saida yayi wajan 5 missed calls sannan ta ɗauki wayar, wata irin ajiyar zuciya Fahad yayi tareda gyara muryarsa yadda zatajita da daɗin gaske baisan giya ta rugada ta fasa mishi murya ba, duk yadda zayyi muryarsa tai daɗi abun ya faskara, shiru ne ya biyo baya ta cikin wayar, ya daɗe yana "Hello!!!," tare da sallama amma ba amsa.

    Zuhra jin muryar Fahad yasata saurin runtse tana tunanin anya zata iya yiwa Fahad soyayyar ƙarya kuwa, dan tabbas tsanarsa a cikin jininta dake, amma yaya zatai dole ta ɗauki fansa wataƙil akan Family ɗinsu bazasu ƙara yunƙurin yiwa wasu haka ba, tunanin matake maiya kamata ta aikatawa Fahad wanda Bashir Iyan Tama bazai taɓa mantawa da ita ba, shiru tayi tare da tsantsanyin tunani akan meya dace taima Fahad wanda bazasu taɓa mantawa da ita ba, abunda koda sunji an kira mai sunanta sai gabansu ya razana tare da tsorata, maganar Fahad ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula, ɗan gyaran murya tayi tare da haɗiye wani Saliva me ɗacin gaske daga maƙogwaranta, murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tana mai Allah wadai da halinta ganin zatai fake love tsakaninta da Fahad, gani take bai cancanci magana mai daɗi daga gareta ba saidai yaya zatai ɗaukar fansa ne ya kawo haka.

   Cikin muryarta mai daɗi tare da ɗaukar hankalin ƴan maza tai masa sallama, Fahad baisan lokacin da yayi saurn cire wayar daga kunnansa ba yana dubawa shin anya ba wrong number bace, jin murmushi mai sauti yasa Fahad zama soko, dan zai iya rantsewa bai taɓajin murya mai daɗi kamar tata ba, gata da saka natsuwa, "Malam Fahad kenan, yau dai Allah ya nufa" ta faɗa tana murmushi yadda zai jita dakyau.

Fahad mutum mutumi ya zama najin wannan daddaɗar murya, shiru ne ya biyo baya tana maijin haushin kanta ganin yadda Fahad bayyi magana ba, ƙara danne zuciyarta tayi tace "Sorry na manta kunsan ku ƴaƴan manyan ƙasarmu ba cika son damu kuke ba, daga fara waya harna dameka da surutu am sorry" ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar.

MUHAMMAD ALEEWhere stories live. Discover now