_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿3️⃣8️⃣
Yafice a wajen zuciyarsa na kona, ji yake tamkar ya kurma ihu, shikenan bashi da ikon zab'in rain shi sai abinda suka ga dama, ya san duk abinda yake gani a yanzu yana daukar shi tamkar sakayar baiwar Allahn nan ne, to amma meyasa su Daddy zasu tirsasashi akan Sara, sai ya d'an-dana mata azaba mafi munin wace ta gani a gidan shi, tunda tayi sanadiyar marin shi da wannan ya isa gida ...
Fitar shi a kamfanin yayi dai² da samun nutsuwata a hankali na mik'e tsaye tamkar wata me iska, aikin gabana na cigaba da yi sabida taron da aka kiramu saura yan seconds, munyi taro cikin nutsuwa duk da na lura da yanda ogan namu yake kamar baya cikin jin dadi, bani kadai na lura da hakan ba duk abokan aikina sun fahimci haka, shi yasa bamu wani jimma ba aka tashi...
Ina so naje gaida Umma na, kai tsaye kasuwa na nufa domin yi mata siyayya, duk wani abu da na san zai sakata farin ciki na siya dai-dai kudina, wata jakar makaranta na gani ta yara me kyau sosai, tsayawa nayi a wajen ina duba kudin da ya rage mun kafin na tambayi kudinta, sake juya kudin nayi a hannu zuciyata babu dadi gani kudin bazasu kai ba, gashi ban fito da ATM ba bare na dauka su cire a p.o.s kayana na dauka zan wuce aiko gaba daya hankalina yayi gida kuma, kuss!! mukayi gware irin me shiga jiki din nan, na rintsi idanuna da suka kawo ruwa a take, zafi na gauraye mun kwanyata, kayan dake hannu kuwa tuni suka nema nasu wajen...
Shima dafe goshi yayi a masifance ya dago domin ci mata mutunci, cak ya tsaya da tunanin shi gani yanda hawaye ke zirraya a kumatunta, Asiya ta dago cike da jin zafi da bacin rai" kai wanne irin wawane marar tunani? banda rashin hankali da tausayi in ni ban ganka ba ai kai ba makaho bane! haka kawai kana neman illatani da wani shegen kanka kamar kirgi, zaka matsa mun na wuce ko sai na cinye maka mutunci?.." ta fada a zafafe..
Fauwass ya goce a hanya jikinsa na rawa zuciyarsa tamkar ta tayi tsalle ta fito zahiri, irin yanayi da take shiga dazu shima shi ya shiga, kayan ta dauka ta fice a gun tamkar kububuwa...
Ya Sauke wata nauyayar ajiyar zuciya, cikin sauri kuma ya bi bayanta da gudu, sai dai kashh ko kurarta bai gani ba..A gaggauce ta shiya tsaf da ita, tana cikin dauri Khausar ta shigo bakin ta na kallon sama, zama tayi kusa da ita cikin jin haushi tace" Anti!! yau a makaranta wani yaro yace ni shegiyace da gaske?.."
Wani irin fad'uwa gabanta yayi ta ma kasa magana sai dan kwalin nata da ta yasar kasa, zufa na keto mata ta koina! cike da tashin hankali tace" a ina yake? wayace kina kula maza a makarantar? me ya hadaki dashi?.."
" Anti! bana kula maza fa ni, kawai zuwa yayi yace wai a kalleni bani da Uba! Ni shageyace...
Shiru tayi wannan karon numfahinta na hawa da sauka, a hankali tace" karya yake gobe zanje makarantar taku kinji!.." ta fada cikin son ka war mata da hankali...
Gudun karta sake fada yasa ta shirya tsaf suka wuce tare, Umma tayi farin cikin ganinsu sosai, inda ta samu Sadiya a gidan tayi wani rashe-rashe da ita, cikin dariya ta mike tana fad'in " ohh Allah ya yarda yau zanga yar gaba da fatiha ashe!.."
Gaba daya kamewa sukayi a wajen, ta nufo Khausar game da kura mata ido, babu ko kifftawa a hankali tace" Allah me iko yarinya me kama biyu, wallahi sak Fauwass dan Alhaji tahiri!.." Ta mike zatayi magana taji sakar mari a kuncinta, Aliyune wanda tun farkon zancenta ya shigo kuma yaji komai, ta dafe kuncinta cikin da matsanancin tsoro, zai kara mata Asiya tayi saurin cewa" A'A abba! ka kyaleta ai gaskiya ta fad'a, abun kunya ne na rigada na aikata ni ban isa nace bazaayi magana akai ba, bana so ta dalilina wani ya sake shiga kunci, dama nazo na gankune sai anjima ku!.."
Hannu Khausar ta kama ta juya da sauri, Sauddat tayi saurin ruk'ota cike da jin kunyar yar ta tace" haba ke kuwa daka zuwa har zaki tafi! ai kya zauna ko baby! tayi maganar da jawota tsakiyar falon..
Aliyu tausayin Asiyane ya cika mai zuciya, lallai ta shiryu tunda yau ta kirashi da suna Abba, ya dubi sadiya dake share kwallar bakin ciki, cikin zafi rai yace" ki biyoni daki, jikinta ya dauki tsuma hawayen ta kwaranyowa, ta dubi Asiya tace" Asiya dan Allah ki bawa Abba hakuri ke ma kiyi hakuri wallahi yau na kadai!.."
Sam bana kaunar ganinta a hankali nace" Umma ya kamata mu wuce lokaci na sake ja! dama nazo ne na gaya miki wani yaro a makarantar su Khausar jiya yace mata shegiya shine nake so kije tunda ni gobe muna da wani aiki me mahimmaci, amma ba damuwa zanje kafin na wuce.."
Tausayin yarta ne ya cika mata rai, ta kamo hannunta cike da raunanniyar muryata tace" ko wanne bawa da irin kaddarasa Dan Allah Asiya karki saka wannan abun a ranki, ta yiyu ma fad'e irin nasu na yara ya had'asu har ta kai ga ya zageta yanzu irin wannan zagin ya zama ruwan dare a wajen yara, karki wani daga hankalinki ba wata babbar matsala bace bare aje makarantar, in kuma ya sake sai a sauya mata makaranta kawai, haka yayi miki?.."
"To Umma!!.." Shine abinda na iya cewa ban sake magana ba, Khausar kam tunda muka zauna tana jikin wani abun wasa sai harkokin gabanta take, damuwar da nazo dashi domin na gaya mata ta bace mun, maganar Sadiya na dawo mun " Ohh Allah yarinyar me kama biyu, wallahi sak Fauwass dan alhaji tahiri, ko a wajen a aikina akwai mutane kusan biyu da sukace Khausar na kama da yaron Oga amma ban tab'a kawowa raina ba, ganin surutun su yayi yawa yasa na bar zuwa da ita, na tsurawa yarinyata ido zuciyata babu dadi, boyayen hawayen da nake danne nawa suka shiga zubowa nayi saurin gogewa domin bana so na ringa kuka a gaba y'ata...
Gani nak'i sakewa a gidan dole Umma ta barni muka wuce, muna tafiya a hanya gaba daya bana cikin nutsuwata, buri na ganin a gida ihu Khausar ne ya saka nayi saurin kallon inda take..
Ta sake shagwab'e fuska a raunane tace" Anti! ina son wancan!.." ta fad'a tana nuna mun ida wasu baby doll's kala² gwanin ban sha'awa, neman waje nayi me kyau nayi paring din motar fitowa nayi na kamo hannunta itama, tafiya muke cike da nutsuwa duk raina ba dadi har muka iso, zab'a ta shigayi inda ni kuma na kame awaje guda, ganin abun nata bana hankali bane yasa na matsu kusa da ita ina fad'in malam guda daya zaka bata!.." aiko ta turo baki gaba ita lallai duka take so, na tsura mata ido rainana sake baci, tambayar shi nayi kudin wanda na dauka ya fada na mike mai, ina fad'i" zaki wuce mu tafi ko sai na b'ata miki?.." aiko ta fashe da kuka cike da sangarcin da ban santa dashi ba, ita ba inda zataje sai an bata dau...
Tafiya tayi na barta a wajen, sai da na kusa zuwa mota na juyo gani ko taji tsoro ta biyoni, babu ita ba labarinta cikin ya kulle a zahiri na furta na shiga uku na lalace...
Da sauri har dan guda na dawo baya, wannan mutun ne a tsugune a gabanta shi yayi mata rumfa yanda bazan hangota daka nesa ba, kudin ya biya gaba daya aka kwaso babydoll zuwa mota na kamar hauka, na kamo hannun y'ata ina zuwa zakici ubanki ne yau!!."
" kar a kuma zagina banji ba ban ganiba! yarinya ubanta na da ikon siya mata duk abinda take bukata a duniya, dan haka abinda take so shi zaanayi!.."
Kallon shasha nayi masa na wuce abuna, samu nayi a lode musu a baya domin but din a rufe yake, sai da na rufe bangarenta kafin na shiga mu kama tafiya...
Muna zuwa gida na kama kunneta na rike kyamm ina me zare mata ido a fad'ace nace" duk randa muka sake fita dake kika mun taurin kai sai na zanne miki jiki wallahi, yanzu uban me zakiyi da wannan babydoll din?.."
Shiru tayi tana kallon kasa domin Allah yayi mata tsoron duka...
Fauwass ya lumshe idanun shi bayan tafiyar mu, yana fad'in kayi maza ka bi bayanta, karka yarfa ta kubuce maka...
"Ok sir...
To kamar yanda na lifa washe gari da wuri na shirya Khausar domin a dakina ta kwana yau, makarantar su naje akan abinda ta fad'a mun ina kokarin shiga da motana na hangi motar mijin Umma tana fitowa, da mamaki a fuska na tsaya dashi da Ummana na gani sai yanzu na tuno akan abinda sukazo, dadine ya cika mun zuciyata ganin wasu mututane uba da uba sun fito hannunsu rik'e da yaronsu...
Gaida su nayi cikin ladabi...

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi