_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN Y'ATA SHINE BURINA_BY.
_USAEEENAH B. ABUBAKAR_
(Mrs abubakar)32
"Albushir na kiraki nayi miki Sauddat yau y'arki da kanta ta rungume y'arta, duk yanda akayi akwai abinda ya faru kafin zuwanta fad'a mun ya ake ciki?.."
Wani irin dad'ine ya kama sauddat har ta manta halin da take ciki na neman saki, " yanzu me take mata? khausar din ta yarda da ita?.."
" To ta dai tsaya k'erere a haka na baro su!.."
" Alhamdulillahi Alhamdulillahi, zanzo nima insha Allah!.."
Cikin sanyi murya da son ta jah ta a jiki tace" zo muje na baki abun dadi!.."
Khausar ta tsira mata idanu kirrr gaba d'aya yarinyar a tsorace take, ta juya taga babu Kaka a wajen aiko sai ta saki kuka, magana bata fita tace" zajje gidanmu!.." ta fada tana zame hannunta tana so ta gudu..
" Eh dama zaki gida amma ba yanzu ba nan na gidanku ne, kiji?.." Ta fad'a tana jan hannunta zuwa d'akinta...
Abun mamaki kayan ciye-ciye irin na yara ta dube jakarta ta d'auko ko yaushe ta siyo ohh...
Yaro ba wayo tana ganin kayan dadi ta manta da batun kisa, da sauri ta haye gadon tana dariya, itama dariyar take mata zuciyarta fal farin ciki, taci wanda zata iya ragowar ta bari da kanta tayi mata wanka tass ta mata kwalliya wanda rabon da ta zauna tayi irinta har ta manta a rayuwarta, ta kimtsa ta cikin wata dogowar riga me balain kyau, itama irin ta sak ta saka banbancin su shine ta babbace ta khausar karama, mayafe ta dauko musu da takalma duk iri guda, sunyi bala'in kyau sosai ga kamanin su ya sake fitowa na alamar y'a da uwa kye din motar ta kawai ta d'auka sai wata hanbak pink colo din kayan su, a tare suke takawa abin gwanin ban sha'awa, gaskiya sunyi mutuk'ar kyau sosai da sosai..
A falo muka tarar da Kaka tamkar jiran fitowar mu take ta mik'e tsaye bakinta a bud'e, farin cikinta yak'i boyiwa ta saka dariya tama kasa magana cak muka tsaya muna kallonta kamar kuma had'in baki dukan mu sai muka saki murmushi, ziriri wasu hawayen dadi suka zuwa Kaka da kyar ta iya daga kafarta ta iso inda muke gaba daya ta rungume mu, game da farurta alhamdulillahi...
" Kaka!!."" na fad'a a shagwabe muna had'a ido kuma sai na girgiza mata kai alamar ta daina bana so, cikin sauri ta share kwallarta a hankali kuma tace" iyee sai ina kuma?.."
" Zamuje wajen shak'atawa ne kaka, nima inaso tayi farin ciki ta dalilina!.." Na fad'a ina ji a raina zan jure ko wanne irin cin kashi muddin akan y'atane...
Da kyau da kyau yarinyar Saude Allah ya tsare hanyya.." ta fad'a tana jijina mun..
Kai tsaye MUNJIBBIR PAK na nufa da y'ata zuciyata a sake, ba laifi muyi farin ciki sosai a wannan ranar yarinyata sai dad'i take ji, wajen wasa yara mukaje nan tai ta gani abubuwa wasan da take so aiko taji dad'i, ina tsaye ina kallon ta ji nayi kamar ana kallona juyowar da zanyi kuwa sai kuke kummm!! cikin gigita na dafe goshi na wani zafi na ziyarta ta, har wata kwallar azabace ta zubo mun, sai da naji dama-dama sannan na dago a masifance, na mijine shima dafe da goshi yana ta yarfe hannu gaba na ne yayi wata irin mummunar fad'uwa, ina ji a jikina tabbas duk yanda akayi mun tab'a had'uwa amma a ina?.."
Kafin na dawo a tunani na sai ji nayi khausar na kirana na juya gareta da sauri zuciyata babu dad'i, dauko ta nayi ina so nazo na tambaye shi waye shi, sai na neme shi narasa na saki tsaki ganin ba kowa a wajen, hannunta na kama muka bar gun...
Muyo siyayya sosai rabin abinda na siyo duk na khausar ne har da wasu tsala-tsalan kaya na siyo mata, yarinyar sai murna take...
Muna shigowa Hajiya ta taso da sauri ta tare mu zuciyarta cike da farin ciki, y'ar ta dauke sama kuma tak'i ajiye ta, gaidata nayi ta amsa fuska a sake, niko haushi ya kamani ganin yada ta dauke mun y'a nace" Hajiya ki sauke mana bakya tunanin ciwon kirji?.."
" har wani nauyi take dashi da zata saka mun ciwon kirji, tunda bata saka mun tana karama ba yanzu kam ba abinda zai faru insha Allah!.."
"Umm to ki sauketa zamu tafi d'aki!.." Na fad'a ina tura baki gaba..
Kasa boye dariyarta tai sai da ta dara kafin tace" lokacin barcin ta yayi sai da safe!.." ta fad'a tana nufar kofar fita nima bayan ta na bina tana juyowa muka had'a ido sai ta ci burki tace" ina kuma zaki?.." "Zanje mu kwanta ne!.." Na bata amsa ina kallonta..
Ajiye khausar din tayi tana harara ta tace" inda akan tane zaki bini ga ta nan na baki aro da sasafe ki tashi ki had'a mata abin karyawa da wanda zata je skl dashi.. tana zuwa nan ta fice a gidan..
Wani dadi ya kamani...
Mrs Abubakar ce
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi