_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_3⃣4⃣
Cikin sauri Aliyu ya ruk'o hannuna da ka yake mun alama kada nayi haka, na daure zuciyata jikina na kad'awa na sake aza kafata da kyar nake takawa sai hakan ya bada wata maana a tafiyar tawa tamkar yanga, yarinyar nan ta sake watsu mana ido fuskarta babu annuri ko kad'an! wata kofa muka sake shiga a nan gabana ya cigaba da fad'uwa na kasa jurewa cak na tsaya ina sauke a jiyar zuciya tamkar wace nayi gudu, Aliyu yace" are you ok?.." kasa amasawa nayi sai tari da na fara gaba d'aya hankalin sa ya tashi, sai da nayi me isata ganin zai wuce nayi saurin kamo hannunshi da kyau ina lumshe idanuna a hankali alamar na fara samun nutsuwa mun kai kusan minti shabiyar kana na samu nutuwa a hankali nace" muje Abba!.."
" Baby ko zamu koma gida ne a hakura?."
"Abba y'ata fa?.."Baice mun komai ba sai gaba da yayi na bishi a baya, wani hamshik'in mutune a hakimce kan wata kujerar alfarma, ya sha sut bak'ake, farine me cikar haiba cikin yauk'i ya d'ago kan shi gani Aliyu da yayi ya saki murmushi game da mikewa tsaye yana mana maraba, alamar sun san juna hannu ya bashi sukayi musabaha daka bisani nima na gaida dashi ya amsa cikin sakewa, bamu dauki wani lokaci ba muka fara abinda ya kawo mu, komai nayi yayi kyau sosai bani da wata matsala a tardduna, haka duk wata tambaya da yayi mun na amsa mai ita dai-dai yace" malama hasiya, gobe insha Allah muna bukatarki a d'akin tantancewa da musalin karfe 7:00 fatan mu ki kasance me kwazo kamar yada saka makonki ya nuna, a yanzu zaki iya tafiya gida zuwa gobe zaa nuna miki komai."
Cikin jin dadi nace" na gode yallab'e!.."
Aliyu shima yayi mai godeya sosai kafin muka baro wajen...Wajen aikinsa na sauke shi kafin nima na dawo gida zuciyata wasai, ranar sai fara'a nake ga a halina Ummana tazo yi mun murna har gid..
Washe gari shigar da nayi tafi ta jiya daukar hankali da nutsuwa, abun mamaki Aliyu ya bar mun motar da muka fita jiya dadi kamar ya kasheni, sai wani rawar kai nake, gaba daya na manta da damuwata tunanin rayuwata a irin wannan kamfanin kawai nake, tun kafin 7:00 na gama shirina haka ma na shirya khausar tsaf da ita domin yau da ita zanje kayan mu iri d'aya, lokaci na cika na fice a gidan zuciyata fal farin ciki...
Muna da yawa jammaar da zaa tantance mata da maza babban hol ne aka tara mu a ciki ko wanne yana wane wannan daka gani ba sai an fad'a dukan mu munaji da kudi da izza kowa harkar gaban sa yake, an fara taro kamar yanda aka tsara duk yawan mu ne nan mutun biyar ne masu duba mu, abunda banyi tsamani ba shi aka tambayeni akan shi, kamfanin jaridda ne babban abinda aka tambayeni shin meyake kawo fayde da zinace-zinace, wace irin rayuwa wanda kayi wa fayde suke fuskanta, in kaddara ta fado musu a irin haka sun samu juna biyu ya jammaa suke daukar su? wace irin tsangwama da kyar suke fuskanta?
Gaba d'aya jikina ya dauki tsama gani nake tamkar rayuwata ya bude mun gashi kowa yana kallon mu da sauraren mu, na rikice matuk'a na dube dumbin jamaar dake gaba na wata irin ladama dana sani ya fad'o mun a zuciya sai naji na raina kaina, me tambayar yace" malama Asiya ke muke jira lokaci na tafiya?.."
Cikin rawar murya zuciyata na zafi nace" Fyad'e!!! wata kalmace me barazana ga rayuwar y'ay'a mata yara da manya, Fyade kalmace marar dadin sauraro da dadin ji, Fyade wani bala'in ne dake iya afkuwa ga wanda Allah ya kaddarto mai, Fyad'e wani iftaine me girman gaske a rayuwar mu, tabbass a wannan rayuwar da muke ciki abinda yafi yawaita kenan birni da kauye lungo da sako na ciki afirika, a yanzu iftta'in da muke fuskata kenan sai da muce innalillahi wa'inna illaihirraju'un, zaka ga wata mak'ocin su ne yayi mata, wata me aikin gidan su, wata malamin makarantar su, wata almajirin gidan su, wata ubanta ne yayi mata, wata kanin mahaifiyarta ko na mahaifita, wata yayanta, wata mijin babarta in ya kasance kaddarar mahaiyarta sake wani auren, gasi nan dai e. t .c.
Rayuwar da suke fuskanta kuwa rayuwace ta kunci da d'acin zuciya rayuwac me cike da takaici kullum tunanin su da wanne ido zasu kalli duniya in ya kasance suna da kunya fa kenan, in kaddara ta fado an samu rabo kuwa lallai suna cikin ifftala'i zasu rayuwar boye kai, rayuwar zaman kad'aici duniya zata zage su zaa su zama abun tsagumi a cikin unguwa, zasu tsane kan su da abinda suka samu ta wannan dalilin, musamma ga wanda bai san waye wanda yayi masa wannan aika-aikar ba, kullum tunanin shi ina zai ganshi? wasu suka kashe abunda suka haifa gudun abinda zasu fuskanta su da abinda suka haifa ga jamaa, wasu sukan kai su gidan marayu wasu kuma sukan rikesu a hannu sabida soyayyar d'a da mahaifi sai Allah baza su iya rabuwa dashi ba duk runtsi, wannan shi ake kira da soyayyar gaskiya, wai shin me yasa wasu mazan basa tausayin mata ne da kananun yara da suke b'atawa rayuwa? shin ya zasuji in haka ta faru akan y'ar su ko kanwar su ko uwar su? wanne irin bakin ciki zaji in suka waye gari suna kallo y'ar su da cikin da baa san uban sa ba? wace irin amsa zaa bawa d'an ko y'ar yayin da suka tambayi waye mahaifin su? shi kanshi wace irin rayuwar zai fuskanta in yaji tushin shi ba me kyau bane? wai ya ake so muyi ne mu mata? shikenan mu yanxu bamu da y'anci kp mu fito ko kar mu fito zaa biyu mu har cikin gidan uban mu ayi mana mummunar illah, to ya ake so muyi ne? wani kuka ya 'kwace mun rad'ad'in abunda ya faru dani ya dawo mun sabo dal! gaba daya jikin jamaar dake cikin hol din yayi matukar yin sanyi hata shi wanda ke mun tambayar sai da ya zubar da kwalla, wasu ko sai daukata suke a waya, matan dake zaune suma banda share hawaye ba abinda suke...
Game da zinace-zinace da kake magana akwai dalilai da yawa da yake kawo hakan! wata zaga marainiyace bata da kowa bata da wani gata, ta rasa ci ta rasa sha inda take tunanin samu taje an hanata bara in taje bazata samu ba, ta fara aikin karfi ba wani me bata hakinta a lokacin da take bukata, ta fara bin manya gidajen masu kudi nan ma sun hanata a haka zata fad'a mugun hannu inda zaa bata amma zaa amshi mutuncita wanda har abada ita dashi sunyi sallama...
Wata zaga tana da iyayen sun sakata a makaranta amma basu damu da d'auwainiyar makantar ba fatan su ma ta samo ta basu, ita kuma gudun karta fad'i sai ta bada mutuncinta ga malamai marasa imani da tausayi, wanda in babu wannan ba yanda zaayi su bari ta wuce...
wata zaka tana da gata iya gata amma shed'an yayiwa zuciyarta fitsari iskacin kawai ta saka a gaba, kuma iyayenta basa kwabarta..
Wata zaga iyayen nakasasune basu da yanda zasu yi ita ke fita nemowa tana cikin wannan halin wani atajiri me wayon banzan zai bude mata ido da kudi shikenan ya lalat..
Wata tsabar son abun duniya ne da neman duniya zai sa ta fad'a harka da ranar lahiri zata zubar da hawaye, a ranar da ba wani me taimakon mu sai fiyayyen halitta..
Wata kuma dama chan a hannu b'ata gari ta taso ta saba da maza da maza tun kafin ta san meye duniya, irin wanna yaran iyayen su a bariki suke haka suma a bariki suka taso, to tayaya zasuyi bariki ba tunda babu arabi ba boko...
Wata kuma iyayenta ke turata ga halaka akan mugun son kudin su...
Yallab'e hakan ya isheka ko na cigaba?.." na fad'a ina me kare mai kallo ganin tunda na fara yake kallona...
Gaba d'aya wajen ya dauki taffi ta ko ina, na sunkuyar da kaina kasa ina kuka sosai domin babban tabone aka tab'o mun, yace" baki rufe maganarki ba wanne irin kira zakiyi ga masu irin halin da kika lisafo kuma wace irin shawara zaki bawa irin matan da tsautsayin fyade afakar musu!..??"
Na kasa magana sai kuka nake, Khausar dake can nesa dani itama ta kama kuka, gani ina kuka da sauri na mike ina me bude mata hannu domin har cikin raina bana son kukanta, aiko ta taho da gudu na rungume y'ata ina jin tausayinta har cikin kokon raina!...""
Mrs Abubakar ce
KAMU SEDANG MEMBACA
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Cerita Pendeklabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi