Chapter 36

6 1 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿3️⃣6️⃣


Dogon bayani ne sosai yayi mun daga baya bani wasu aikin na musamma,  sannan ya hadani da wanda zamuyi aiki tare dasu...


Kiran hamza yake kamar zai tashi sama,  sai da ya dauki lokaci me tsaho kafin ya daga wayar tashi a gadaran ce yana fad'i " ya akayi ne?.."

" Hamza!! dan Allah ina zan same ta?.."

" wacece?." Ya jefa mai tambayar cike da rashin fahimta..

Shima cikin sauri ya bashi amsa da cewa" yarinyar da ka turo mun dazu..

"Ok nima abokina ya turo mun,  dana gani na tura maka sabida abun yayi kamceceniya da na sarah..

" look aboki na,  yanzu ba lokacin wasa bane dan Allah ka nutsu muyi magana ka nemo mun ita pls ina tsananin neman ta a rayuwata ina so na ganta ko sau daya ne,  ta hakan ne kawai zan iya goge shafin rayuwarta na huta gaba daya..

" OK zan sa a duba maka ita.. daga haka su kayi sallam kowa ya ajiye wayar,  zuciyar Fauwass cike da zulumi da tunani iri-iri,  ya zaiyi kenan abinda ya jima yana jira a rayuwarsa tsahon shekaru da dama,  sai yau Allah ya kawo mai dole ne ma ya tashi tsaye dan gani wata matsala bata kunno kaiba.."

Sarah ce ta fito hannun ta dauke da khausar dinta,  idanunta jawur cikin in ina tace" Yallab'e dan Allah ina so naje gida kamar yarinyar nan bata jin dadi kuma na rasa me yake damunta!.."

A wulakance ya kalleta ko me tuno kuma ohoo sai cewa yayi " zaki iya zuwa saura kuma naji wani abu kiga yanda zan karye miki kafa,  munafika kina wani sunnakai kasa kamar ta Allah,  algunguma kawai...  ya wuce ta b'acin ran sa na k'aruwa ran shi yana fatan mutuwa ga khausar din ko zai huta da ganin damuwa...

Tana fita yayi kiran waya domin abi masa bayanta aga inda zataje...

Yau da wuri na shirya domin muna da aiki me mahimmacin da zamuyi a office,  ina shirin fita Umma na shigowa fuskarta babu yabo ba fallasa tace " Baby manya gari!. Na fahimci me take nufi dan haka nayi kasa da kaina cikin girmmawa nace ki yafe ni umma ta aikine yayi mun yawa a kwananki nan shi yaaa ban leko ba,  amma ina nan zuwa ba da jimawa ba,  yanzu ma sauri nake ai zaki kai dare ko in na dawo zamuyi magana.." Na kai karshen zance da kiss din ta a goshi ina fice a dakin da sauri ban jira cewar ta ba...

Murmushi tana kallo na ganin yanda na sake cika da kyau gashi kayan jikina ya amsheni nayi wani fam dani a ciki,  dogowar rgace ta atamfa sai mayafi ne da nayi roling dashi nayi kyau sosai,  a tsatsaye na sha tea din  ina d'agawa Khausar hannu da take kokarin bina a hankali nace" yarinyata yau fa bazani dake sabida ba zama zamuyi waje guda ba sai wani lokaci kya bini,  bye!.." na fada ina nufar hanya ta marairaice fuska cike da shagwaba zatayi kuka Umma na ta taho da sauri tana rik'o hannunta game da fad'in i shiru yarinyar momy zaki bini!.?

Cike da son yawo tace" eh zaki siya mun sweet?.." Cikin maganar da bata fita sosai..


Duk yanda Fauwas yaso da ganin a samo mai yarinyar a ranar abun gagara yayi sai ma kira da ya samu daga sama akan ana neman sa a kamfanin  baban sa dole ya shirya dan halarta taron...

Tun kafin na shiga gabana ya tsananta fad'uwa duk wata addu'a da tazo baki na nakeyi sai da naji zuciyata ta samu salama sannan na kutsa kaina bakina dauke da salama...

Gaba daya jamaar suka zuba mun ido domin kamshin turarena ne ya cika wajen baki daya, da sautin tafiya ta, sau daya na k'alli jamaar wajen na dauke kai na,  abinda ke gaba kawai nake wani irin sauti na fara ji wanda har abada bazan manta shiba,  take kirjina ya cigaba da bugawa babu kwakwautawa,  jikina ya dauki wani irin rawa,  ban san lokacin da na fad'a kan kurejar dake kusa dani ba,  ga wata irin zufa da take keto mun ta ko ina a jikina,  sauti ya cigaba da kusanto ni yanayi da ni kuma na gama ficewa haiyyaci na...

" Aboki na! d'an tsaya mana cewar wani matashi dake kusantuwa  inda yake,  ya sauke hannun shi da barin bud'e kofar yana ware manya idanun sa akan wanda ya dakatar dashi alamar ya akayi...

" Sir na nemanka a ciki kafin a fara taron!.." ya fad'a ba alamar tsoro a tare dashi,  wani kallon raini yayi mai kafin ya juya ya wuce ta bayan sa...

A zaune ya same shi nesa dashi kuma Sarah ce zaune itama da alama taci kuka ta koshi,  gefe daya kuma Khausar ce dake wasa da wani karamin ted...

Ya sake b'ata fuska yana wani fuzfuzga a hankali yace" daddy gani!.."

A hankali ya matso inda yake yana kallon shi cike da kunar rai, karo na farko kenan da ya tab'a masa rai duk ko da irin kaunar da yake mai ya zama dole ya nuna mai  kurensa,   yana dagowa ya kwashe shi da mari Sarah ta mike tsaye a mutukar tsorace jikinta na kad'awa gani daddu na shirin kara mai tayi saurin rik'e hannun sa bakinta na rawa tace" a'a daddy kayiwa Allah da manzon tsira ka rabo dashi,   wallahi ni kadai na san azabar da zai gana mun in muka koma gida... ta ida zancen tana share kwallar da ta zubo mata...

Fawwazz ya kura mata ido zuciyarsa na anyya na masa abubuwa da dama,  a hankali ubanasa ya sauke ajiyar zuciya sai da ya d'an huta sannan yace" ya mukayi dakai?.."

Tsabar rad'ad'in abinda yayi masa kasa magana yayi sai Sarah da ya kurawa ido kamar za hadiyata,  Daddy ya sake buga mai tsawa had'i da dukan tebur din dake gaban sa yace" karo na karshe da zan sake shiga maganar ku wallahi..."

Asalin su...

To masu karatu anzo wajen fa.

Ya kamata ku hito ku nuna mana kauna...

Mrs abubakar ce

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum