_YA ZANYI_
_(FARIN CIKIN ƳATA SHINE BURINA)__BY_.
_USAEENA B ABUBAKAR_
*(MRS ABUBAKAR)*
*Na gode sosai Allah Ya bar zumunci ina kan samun sauki sosai, wa yanda sukazo gida ina muku Allah ya huta gajiya na gode*
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION💫
*We _are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are the best among all...DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO.*🅿5⃣
A hankali nake jiyo sautin takalmi, na sake ruɗewa ainon na lumshe idanuna hawaye na shatata, a hankali nake karanto duk addu'a da tazo baki na, cikin sanɗa aka shigo ɗakin nawa haske aka kunna a hankali murya ƙasa² naji ana kiran suna na.
" Baby!!! Baby!!! kina jina kuwa?.."
Da sauri na fito a maɓoyata jikin ta na shige ina rera kuka ƙasan maƙoshi na, cikin rawar murya nace" Umma na! tsoro nake ji sosai, ji nake kamar da mugaye a gidan!.."
"Shittt.." shine abinda ya fito a bakin ta, hannu na ta kama mukayo waje gaba ɗaya, cikin sauri muka shige ɗakin ta bayin ɗakinta ta buɗe jikin ta na rawa tace" Baby na!! ki kasance me taka tsantsan a duk halin da zaki tsinci kan ki, duk runtsi duk wuya ban amince ki fito a bayin 'na ba har sai gari ya waye, kiyi mun alkawari bazaki fito ko da ko zaa kashe mu ne a gaba idanunki?..."
Waro idanunawa nayi waje zuciyata 'na wani irin bugawa da ƙarfi, zanyi magana tayi saurin katseni da cewa" bana buƙatar tambayarki a yanzu umarni na baki muddin kika fito a nan ban yafe miki ba..."
Kuka nake cikin maƙoshina ina ji ina gani ta manna mun kissing a goshina tana waye²'na har ta fice a ɗakin baki ɗaya bayan ta kulleni a ciki!..."
Tana fitowa haske ya gauraye ilahirin falon a ɗaure ta hange shi goshin sa na ɗigar jini, a take jikinta ya ɗauki tsima cikin tsanani kanɗuwa take duban su ɗaya bayan ɗaya, gaba ɗaya fuskar su a rufe take ko idanun su bata gani, ko wanne yana ɗauke da muguyen makamai a hannu, wanda ke kusa dashi ya daka mata wata muguwar tsawa, cikin wata kausashiyar murya yace" keee! zauna nan a wajen!.."
Cikin wasu hawaye masu zafi take kallon shi, murya a raunane tace" ko wanne bawa da irin kaddarar sa, ko da zaka ringa yankar naman jikina sala-sala banga wanda ya isa yayi min shamaki da isa wajen rushina ba!..."
Cikin ƙarfin hali take takawa a ƙwai taraza a tsakanin su, taku biyu tayi masu kyau wani yazo ta bayan ta ya makamata gora a kai, wani irin zafi ne ya ratsa mata ƙwanya a hankali ta zube akan gwiwoyin ta ganin ta na rauni, ta kalle jabeer dake ɗaure tamau shima yana kuka yana so yayi magana amma babu dama, ta numfasa hawaye na bin ƙuncinta cikin mugun ƙarfin hali tace" zan iso gareka ko da hakan zai zamo ajalina!...
Shugaban ƴan fashin ya tintsire da dariya me kama da kukan jaki, har gaban ta yazo ya sunkuyo cike da ƙyata yace" ya kayi sarauniya soyayya ni ko zanga karshe soyayya yau, 'in kin isa ki motsa a nan wajen!..." Ya faɗa yana taka mata gadon baya da kafar sa me shegen ɗauyi, ta saki wani irin ihu cikin wahaltuwa ta dube shi numfahin ta na fita da ƙyar tace" har gaba da abada ba zamu taɓa yafe maka ba daga ni har ahalina!..."
Kafa ya ɗaga ya sake maka mata a yanxu kam ko motsi bata sakeyi ba....
Ni da nake bayi a kulle jin ihun Umma ta yasa na kirata da ƙarfi, hankali na a tashe ina bugon ƙofar ko zata buɗe..
Gaba ɗaya hankalin su ya dawo inda suke jin sautin...
Comment
And
Shared
Pls
KAMU SEDANG MEMBACA
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Cerita Pendeklabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi